Gwamnatin Tinubu ta yi wa Sarki Sanusi raddi kan manufofinta

Lokacin karatu: Minti 3

Gwamnatin Najeriya ta buƙaci mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II da ya ajiye son rai da nuna ɓangaranci ya mayar da hankali kan buƙatun ƴan Najeriya.

A ranar Laraba ne dai Sarki Muhammadu Sanusi II a yayin taron tunawa da fitaccen lauyan nan ɗangwagwarmaya na Najeriya, Chief Gani Fawehinmi karo na 21 a Lagos, ya yi kalaman da suka harzuƙa gwamnatin.

Sarki Sanusi ya bayyana cewa yana da bayanai kan wasu abubuwa game da halin da Najeriya ke ciki da hasashen abin da zai iya faruwa da kuma yadda za a iya kaucewa hakan, to amma ya ce ba zai bayyana hakan ba, domin idan ya yi hakan zai taimake su, shi kuma ya ce ba zai taimaki gwamnatin Tinubu ba.

Cikin wata sanarwa da ministan yaɗa labarai da wayar da kan alumma na Najeriya, Mohammed Idris ya fitar, gwamnatin ta nuna takaicinta "kan yadda matakan da take ɗauka waɗanda ƙwararru a duniya suka amince da su, ciki har da shi Sarki Sanusi, a yanzu yake sukar su saboda ba ya tare da gwamnatin."

Sanarwar ta ce "gwamnatin Tinubu ta yarda da cewa Sanusi, da ma duk wani ɗan Najeriya na da damar faɗin ra'ayinsa ta hanyar jinjina ko kuma suka kan yadda ake tafiyar da gwamnati."

Sai dai a cewarta, "abin mamaki ne ace shugaba, musamman wanda ya fito daga ɓangaren da ke girmama faɗin gaskiya, da adalci, zai fito fili ya nuna cewa yana ƙin faɗin gaskiya saboda son rai da kuma tunanin ana ƙin sa."

Gwamnatin ta Tinubu ta kuma ce ba ta buƙatar amincewar Sarki Sanusi kan muhimman manufofinta, waɗanda a cewarta ƙasar na wata gaɓa da wajibi ne a ɗauki irin waɗannan tsauraran matakai da tsare tsare domin magance matsalolin tattalin arziƙi, waɗanda kuma a yanzu sun fara samar da cigaban da ake buƙata.

"Gwamnati na ɗaukar matakan da za su kawo sauyi ne ba don suna da sauƙi ba, sai dai domin suna da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da makoma mai kyau da kuma cigaba mai ɗorewa ga ƙasar, kamar yadda Sarki Sanusi ya yi ta fafutukar ganin an samar." In ji sanarwar.

A cewar gwamnatin, sake gina Najeriya na buƙatar haɗin kai, mayar da hankali da kuma sadaukarwa daga dukkanin masu ruwa da tsaki, kuma a matsayinsu na gwamnati, suna buƙatar shugabbanin al'umma su gujewa kalaman da za su kawo cikas ga amincewar da al'umma ke da shi a kansu.

Sun ƙara da cewa wannan wani lokaci ne mai muhimmanci a ƙasar, kuma abin da ake buƙata shi ne haɗin gwiwa ba rarraba hankali ba.

"Gwamnatin Bola Tinubu ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba kan manufofinta na kai Najeriya ga tudun mun tsira, kuma kofarta a buɗe take domin tattaunawa masu muhimmanci da masu ruwa da tsaki, a yayin da kuma ta yitsaye tsayin daka kan sanya buƙatun Najeriya sama da komai."

Jawabin Sarkin Kano a Lagos

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ce ba zai taimaki wannan gwamnatin ta Shugaba Tinubu ba.

A ranar Laraba ne dai Sarki Muhammadu Sanusi II a yayin taron tunawa da fitaccen lauyan nan ɗangwagwarmaya na Najeriya, Chief Gani Fawehinmi karo na 21 a Lagos.

Sanusi ya ce zai iya yin bayani a kan 'yan wasu abubuwa game da abubuwan da Najeriya ke ciki da hasashen abin da zai iya faruwa da kuma yadda za a iya kaucewa hakan, to amma ya ce ba zai yi hakan ba, domin idan ya yi hakan zai taimake su, shi kuma ya ce ba zai taimake su ba.

Mai martaban ya ce ya yanke shawara cewa ba zai yi magana a kan tattalin arziki ko sauye-sauyen da gwamnatin ke yi ba ko ma ya yi bayani a kan komai, ''saboda idan na yi bayani hakan, za taimaki gwamnatin, to amma ba na son in taimaki gwamnatin nan.''

Ya kara da cewa, ''Abokanaina ne, to amma idan ba sa yin abu kamar abokanai, ni ma ba zan dauke su kamar abokanai ba.''

''Ba ma su da mutane masu kima da za su zo su yi bayanin abin da suke yi ba. Ba zan taimaka ba,'' in ji Sarkin Kano.