Champions League: Wane jan aiki ne a gaban Arsenal?

    • Marubuci, Phil McNulty
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Chief football writer
  • Lokacin karatu: Minti 6

Ƙwarewar Luis Enrique wajen gina ƙungiya na nufin cewa Arsenal na da jan aiki a gaba a wasanta na ƙarshe a gasar zakarun Turai wato Champions League da ƙungiyar Paris Saint-Germain.

PSG ce ta samu nasara a wasan da aka yi a daren ranar Laraba, duk da cewa canjaras aka yi, amma PSG ce ta yi nasara da jimillar ƙwallo 6-4.

Tun a minti na uku ne ɗan asalin Georgia, Khvicha Kvaratskhelia ya kwaso ƙwallo ta gefe sannan ya jefa wa dodon raga Ousmane Dembele, wanda shi kuma ya ƙarasa ta zuwa cikin raga.

Duk da ƙoƙarin da Harry Kane ya yi na rama ƙwallo daga baya, hakan bai sauya wani abu ba.

Jim kaɗan bayan haka ne ƴan wasan PSG suka ɓarke da murnar samun nasarar zuwa karawar ƙarshe a gasar ta Champions League - wadda za ta zama dama ga ƙungiyar ta kare kambinta wanda a kakar da ta gabata ta doke Inter Milan da ci 5-0.

Wanda hakan ya ƙara jaddada ƙungiyar a amatsayin ɗaya daga cikin ƙungiyoyi mafi ƙarfi a duniya.

Arsenal za ta zo da ƙarfin gwiwa a wasan ƙarshe da za ta buga bayan shekara 20, to amma tabbas da gaske ne za su fuskanci babban ƙalubale a karawar ƙarshen da za a yi ranar 30 ga watan Mayu a ƙasar Hungary.

Saboda idan Arsenal na son ta yi nasara, to wajibi ne ta rusa tsarin Luis Enrique, wanda shi ne ginshiƙin tsara ƙayatacciyar ƙwallon da PSG ke bugawa.

'Fasihin da ya gyara PSG'

Ɗan ƙasar Spaniya ne kuma shi ne ginshiƙin sabon salon ƙwallon da PSG ke bugawa, wanda ya samo asali bayan tafiyar fitattun ƴan wasa irin su Lionel Messi da Kylian Mbappe da kuma Neymar, waɗanda ake ganin suna ji da kansu amma suka gaza samar da sakamako.

Luiz Enrique, wanda ya lashe kofin zakarun Turai da ƙungiyar Barcelona a 2015 ya buƙaci ƴan wasansa su ajiye jiji da kai a gefe - ko kuma ya kawar da waɗanda suka ƙi ji.

Bayan maye gurbinsu, sai ya tattaro ƴan wasan da suka dace masu hazaƙa, ya gina su kan tsarin ɗa'a da aiki tare, wanda a yanzu wannan ne abin da zai wahalar da Arsenal.

Kuma jagoran wannan tafiyar tasu shi ne Marquinhos.

Ɗan wasan na tsakiya ɗan asalin ƙasar Brazil ya tafi PSG ne daga Roma a 2013, inda ya tsira daga aikin da Enrique ya yi na kawar da shahararrun ƴan wasa masu jiji da kai, saboda mai horaswan yana da basirar gano ƙwarraen dan wasa idan ya gan shi.

Ɗan wasan ya gane yadda zai yi wasa tare da takwaransa William Pacho, wanda ya taka rawa wajen hana ɗan wasan Munich Harry Kane komai har sai ƙarshe-ƙarshe lokacin da dan Ingilan ya samu damar kai hari.

Haɗuwar Kvaratskhelia da Dembele ya yi armashi a awasan, yayin da Desire Doue mai shekara 20 - ɗaya daga cikin matasa masu haskawa a PSG - ya riƙa addabar ƴan wasan Bayern Munich, inda ya riƙa kai hare-hare masu hadari bayan komawa daga hutun rabin lokaci.

Bugu da ƙari ɗan wasan da ya zama cikakamo shi ne Marquinhos wanda a ko da yaushe yake tsayawa daidai inda ya kamata kuma yake wasansa a natse da ƙwarewa.

A ƙarshe kuma sai tsakirar PSG: Vitinha, Fabian Ruiz da Joao Neves waɗanda su ne ke kitsa komai.

Ƙwallon da Ruiz ya bayar gabanin wadda Dembele ya zura, abu ne mai matuƙar ƙayatarwa - daga nan kuma sai ya koma tsare gida babu-ji babu-gani kamar yadda Enrique ya buƙata, wani abu da ya zamo daidai da yadda ƙungiyar ke son lamurra su wakana.

Za a iya cewa Luis Enrique ya samu PSG ne a warwatse, inda ya tsinto duk ɓaraguzan ya haɗa ta wuri ɗaya kuma ta zauna daidai yadda ake so.

Tsohon ɗan wasan Liverpool Stephen Warnock ya shaida wa BBC cewa: "Zai yi wahala ga kowane mutum ya ce PSG ba za ta iya yin nasara ba a Budapest. Suna da ƙarfi ta kowane ɓangare. Naƙasu ɗaya da nake ganin suna da shi shi ne mai tsaron raga Matvei Safonov.

"Ɗaya daga cikin ƙalubalen da Arsenal za ta fuskanta shi ne ratsa bayan PSG. Wannan na nufin dole Bukayo Saka da Leandro Trossard, waɗanda za su buga gefe da gefe, su yi ƙoƙarin danna ƴan wasan bayan na PSG kuma su kasance tare da su koda yaushe, sannan kuma suna buƙatar su yi ƙoƙarin dannan su su wuce."

Warnock ya ƙara da cewa: "Zai yi matuƙar wahala ga Arsenal su danne waɗannan ƴan wasa na PSG, domin ba za ka iya tare su na tsawon lokaci ba.

"Abu ɗaya da za a iya cewa a nan shi ne idan har ka danne su, to akwai Bradley Barcola da Doue da kuma Kvaratshelia wadanda suka ƙware wajen tunkarar difendu kai tsaye, shi kuma Dembele zai iya yanke difenda shi kaɗai.

"Duk ta yadda ka kalle su, tara ne masu hazaƙa kuma za ka sha wahala wajen gano raunin su. Idan ka kalla baki ɗaya a cikin ƙungiyar sai ka ga wane ne na yarwa?"

PSG ta nuna gwanacewarta a lallasawar da ta yi wa Bayern Munich 6-5 - ƴan wasan gabasu suka nuna azama a falle na farko, sannan a lokacin da aka zo falle na biyu masu tsaron baya suka nuna dagiya wajen tabbatar da cewa Bayern Munich ba ta je ko ina ba.

Irin wannan ƙwazo ne suka nuna a karawar kwata-fainal da ƙungiyar Liverpool, inda suka yi nasara a filin wasa na Anfiel su biyu a jere cikin kaka biyu, inda suka tarwatsa katangar baya ta Liverpool suka tsere da nasara 4-0 kan zakarun na Ingila.

'Bayern ta haɗu ne da waɗanda suka fi ƙarfinta'

Hazaƙar PSG ta tattara ne a kan Dembele - matashi mai tsada wanda ya gaza samun wuri a Barcelona, amma Luiz Enrique ya sauya shi zuwa matashin da ya lashe kyautar Ballon d'Or.

Idan ana son ganin aikin Enrique a PSG, to a kalli Dembele.

Sai dai duk da gwanintar da PSG suka nuna a wasansu da Bayern, abin bai zo musu da suaƙi ba.

Bayern ba ta cire rai ba ko da na minti ɗaya, lamarin da ya tayar wa PSG hankali.

Matsalar kawai ita ce Bayern ta hadu da waɗanda suka fi ƙarfinta.

Har zuwa ƙarshen wasan ƴan wasan PSG ba su nuna gajiya ba, kuma ba su nuna jiji da kai ba. Duk wata ƙwallo mai hatsari da Bayern ta garo zuwa cikin da'irar PSG za ka iske mutum ɗaya ko biyu sun yi kanta sun kawar da ita.

Wannan ne abin da ya zama wajibi Arteta ya san yadda zai yi akai idan aka je Budapest.

Aikin da ke gaban Arsenal shi ne ta doke ƙungiyar da ita ce mafi ƙwarewa a nahiyar Turai.