Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda aka kashe fiye da mutum 50 a Filato
Aƙalla mutum 50 ne aka sake kashewa a wani hari da wasu ƴan bindiga suka a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato.
Hukumomin gwamnatin jihar ta Filato sun ce an kai harin ne a cikin daren Litinin a garin Zike da ke yankin Kwall a Karamar hukumar ta Bassa.
Mai bai gwamnan jihar Filato shawara kan harkokin tsaro Admiral Shipi Gakji mai ritaya ya tabbatar wa BBC cewa an kai harin ne a cikin dare, wayewar garin Litinin kuma adadin waɗanda aka kashe "ya zarce 40."
Sai dai Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ta Filato ta tabbatar wa BBC cewa adadin waɗanda suka rasa rayukansu a harin ya kai mutum 51.
"Maharan sun shiga ne suka buɗe wuta ne kan mutane suna barci suka ji ruwan harsasai,"
"Sun kashe mutane a gidaje da kuma kan titi, yanzu an ƙidaya gawarwaki 51, in ji Hon. Sunday Abdu Shugaban Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Filato.
Ya ƙara da cewa al'ummar yanki na cikin hali da ɗarɗar tare da jimamin abin da ya faru.
Wani shugaban al'umma a yankin na kwall ya shaida wa wani gidan tallabin mai zaman kansa cewa maharan sun shammaci tawagar 'yan banga da jami'an tsaro da ke sintiri inda sai suka bari sai da suka je rangadi a wani kauyen, sai suka afkawa garin na Zike.
Ya ce duk da cewar jami'an tsaron sun juyo amma suka yi nasarar fatattakar maharan amma dai koda aka yi hakan mai afkuwa ta afku, domin sun riga sun kashe mutane 36 nan take yayin da wasu huɗu suka mutu daga bisani.
Haka kuma akwai wasu mazauna garin da suka samu raunuka kuma suke karbar magani a asibiti.
Wannan na zuwa ne kimanin makonni biyu bayan wani hari da ƴan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar ta Filato, wanda ya yi sanadin kashe fiye da mutum 50 da tarwatsa wasu da dama, lamarin da ya girgiza kasar tare ya jawo alawadai daga sassa daban-daban cikin har da fadar shugaban kasar.
Me hukumomi suka ce
Gwamnatin jihar Filato ta yi allawadai da harin na baya-bayan nan.
Kwamishinan yaɗa labaran jihar Joyce Ramnap ta ce hare-haren babbar barazana ce ga rayukan al'umma da kuma zaman lafiyar jihar.
Babu dai wata sanarwa kawo yanzu daga ɓangaren ƴansandan jihar.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Amnesty International ta yi allawadai da harin tare da kira ga shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kada kwamitin bincike na musamman domin gano gazawar jami'an tsaro wajen kawo ƙarshen zubar da jinin a jihar Filato.
Ƙungiyar reshen Najeriya ta ce dole a kawo ƙarshen zubar da jinin al'umma tare da hukunta masu kai hare-haren.
Filato jiha ce mai al'umma masu mabambantan ƙabila da addini, wadda ta daɗe tana fama da rikici mai nasaba da siyasa da addini da kuma ƙabilanci.
Sau da yawa akan zargi makiyaya da laifin kai irin waɗannan hare-hare a matsayin ramuwar gayya a rikicin da suke yi da manoma, sai dai a lokuta da dama sukan musanta hakan.
Hukumomi a baya sun sha kafa kwamitoci domin magance matsalar, amma duk da haka, lamarin ya ci tura.