Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea na son Marc Guehi, Man United da Chelsea da Newcastle na son Mateta
Chelsea na tunanin dan wasan baya na Ingila mai taka leda a Crystal Palace, Marc Guehi, 24, ya koma kungiyar maimakon Tottenham a lokacin bazara. (TBR Football)
Newcastle United ta taya dan wasan gaba na Sweden, Alexander Isak mai shekara 25 kan kudi £150m. (Fichajes)
Chelsea na tattaunawa kan sayar da dan wasan tsakiya na Brazil, Andrey Santos, mai shekara 20, wanda ke zaman bashi a Strasbourg, za a sayar da shi a karshen kakar wasanni. (Teamtalk)
Arsenal ta so daukar 'yan wasan gaba hudu kafin a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasa a watan Janairu, to amma hakan bai yi wu ba saboda rashin samun wadanda suka cancanta. (Mail)
Newcastle ta yi watsi da batun dan wasan tsakiya na Ingila mai taka leda a Galatasaray Kieran Trippier, mai shekara 34. (Caughtoffside)
Manchester United da Chelsea da Newcastle na son mai kai hari na Faransa da ke taka leda a Crystal Palace, Jean-Philippe Mateta, mai shekara 27, wanda kawo yanzu bai rattaba hannu kan kowacce yarjejeniya ba. (TBR Football)
Ana sa ran Chelsea ta rage makudan kudin da ta lafta a kan dan wasan tsakiya na Ingila Kiernan Dewsbury-Hall, mai shekara 26, bayan an gagara tattaunawa akan sayar da shi a watan Janairu. (Football Insider)
Manchester United ta shirya rage fam miliyan 27 kan kyautar kudi ta gasar Premier League a wannan kakar. (Football Insider)
Wolves ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fam miliyan 62 kan dan wasan tsakiya na Brazil Matheus Cunha, a makon da ya gabata, kan kwantiragin shekara hudu da rabi. (Mail Plus)
Stuttgart na son manajan Como Cesc Fabregas, a matsayin sabon manajansu,idan Sebastian Hoeness, ya bar kungiyar ta Bundesliga a kakar wasa. (Bild, via Football Transfers)