Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wace rawa Arewa za ta taka a zaɓen Najeriya na 2027?
Muhawara ta sake kaurewa a Najeriya kan rawar da yankin arewacin ƙasar zai taka a babban zaɓe mai zuwa na shekarar 2027, yayin da 'yansiyasar yankin ke ganin sai da goyon bayansu ɗantakara zai yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa.
Hakan na zuwa ne bayan tsohon taimaka wa shugaban ƙasar a fannin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed ya yi wata hira, inda yake cewa nan da wata shida yankin zai fitar da matsayarsa.
Duk da cewa Hakeem ba shi ne mai magana da yawun al'ummar yankin ba, ana kallon sa a matsayin ɗaya daga cikin manya saboda tsohon matsayinsa na mai magana da yawun ƙungiyar dattawan yankin ta Northern Elders Forum (NEF).
Kodayake bai faɗa da bakinsa ba, ana ganin ya ajiye muƙamin nasa na gwamnatin Bola Tinubu ta jam'iyyar APC ne domin yin adawa da gwamnatin.
"Nan da wata shida Arewa za ta fayyace matsayarta," kamar yadda aka gan shi cikin wani bidiyo yana yana faɗa.
"Idan sauran yankuna na son a yi tafiyar tare da su, shikenan. Idan ba haka ba kuma, za mu kama gabanmu kawai. Abin da muka sani dai shi ne, babu wani mutum da zai iya zama shugaban ƙasar Najeriya ba tare da goyon bayan Arewa ba."
Ba Hakeem kawai ba, 'yansiyasar yankin sun sha maimaita wannan kalaman duk lokacin da zaɓe ya ƙarato.
'Amma da sharaɗi'
Tsarin siyasar Najeriya ya sa dole ne kowane ɗantakara ya karaɗe lungu da saƙo kafin ya iya samun ƙuri'un da yake buƙata.
Masana harkokin siyasa a ƙasar na ganin kalaman na Hakeem da ire-irensa na kan hanya amma idan aka cika sharaɗi ɗaya.
"Rawar da Arewa za ta taka a zaɓen 2027 ba ta da wani bambanci da wadda ta saba takawa, kuma hakan zai yiwu ne kawai idan ta ci gaba da zama dunƙulalliya, mai alƙibla ɗaya," a cewar Malam Kabiru Sufi na kwalejin share fagen shiga jami'a ta jihar Kano.
"Idan dai aka cika wannan sharaɗi, to duk wani ɗantakara ko ɗan Arewa ne sai ya nemi goyon bayan 'yan arewacin kafin ya yi nasara."
Ya bayar da misalin haɗakar da jam'iyyun siyasa suka yi kafin babban zaɓen 2015, inda jam'iyyun CPC da ACN da ANPP da wani ɓangare na APGA da wasu gwamnonin PDP suka kafa APC mai mulkin Najeriya a yanzu.
"Idan aka samu rarrabuwar kai kuma, to Arewa za ta zama kamar wani taron tsintsiya ne ba shara, " in ji Sufi.
Me ya sa 'yan Arewa ke tutiya?
Malam Sufi ya ce ɗaya daga cikin dalilan da suka sa 'yan arewacin Najeriya ke jin cewa sai da su za a ci zaɓe shi ne yawan al'umma.
A zaɓen 2023 da ya gabata, sahihan ƙuri'un da 'yantakara huɗun farko suka samu a jihohin arewaci sun zarta na kudanci da kusan miliyan biyar.
Bola Tinubu na APC, da Atiku Abubakar na PDP, da Peter Obi na LP, da Rabiu Kwankwaso na NNPP, sun samu jimillar ƙuri'u miliyan 13,716,667 a jihohin arewacin Najeriya. Sun samu jimillar 9,020,741 a jihohin Kudu.
Bola Tinubu da ya lashe zaɓen ya samu jimillar 5,346,404 a jihohin Arewa, yayin da ya samu 3,206,969 a jihohin Kudu.
"Indai Arewa ta sake yin abin da ta yi a 2015, tabbas dole ne sai an nemi goyon bayanta, amma idan aka samu rarrabuwar kai za ta zama mushen gizaka - ana yi mata kallon za ta iya amma kuma ba za ta iya ba," kamar yadda Sufi ya bayyana.
To ko Arewan za ta iya magana da murya ɗaya?
Farfesa Abubakar Ma'azu, masanin harkokin siyasa ne a jami'ar Maiduguri kuma yana ganin za ta iya yin hakan.
"Idan aka duba, waɗanda suka kafa APC sun fara yunƙurin ne tun a 2011. Abin bai yiwu ba amma suka shiga zaɓe a haka kuma suka sha kaye. Sai daga baya suka gano kurensu kuma suka yi nasara a 2015 bayan cim ma haɗakar," in ji shi.
Za a iya cin zaɓe da ƙuri'un Arewa kawai?
Kamar yadda 'yan Arewa ke tutiya da cewa sai da goyon bayansu za a ci zaɓen shugaban ƙasa, haka ma sai ɗantakara ya samu ƙuri'u a kudanci kafin ya yi nasara.
Kafin haɗakar APC ta kayar da PDP mai mulki, tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi takara har sau uku ba tare da nasara ba, har sai bayan ya samu goyon bayan wasu jam'iyyu daga Kudu.
Buhari ya fara yin takara ne a APP a 2003, ya sake yi a 2007 a jam'iyyar bayan ta zama ANPP, sai a 2011 kuma ya yi a CPC.
Ana ganin shigar jam'iyyar ACN ta Bola Tinubu cikin haɗakar APC ce ƙashin bayan nasarar Buhari saboda yadda take da tasiri a jihohin kudu maso yamma da Yarabawa ke da rinjaye.
Kazalika, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023 ya samu ƙuri'u mafiya yawa a arewaci (4,834,767) sama da kudanci (1,751,047), amma duk da haka bai yi nasara ba.
"Dole ne ɗantakara ya karaɗe ƙasa baki ɗaya, ya samu ƙuri'u a Kudu da Arewa kafin ya samu kowace irin nasara," in ji Farfesa Ma'azu.