Yadda aka fara yaƙin neman zaɓe a Kamaru

Asalin hoton, Michel Mvondo/BBC
An fara yaƙin neman zaɓe a Kamaru, gabanin zaɓen shugaban ƙasar da za a yi a ranar 12 ga watan Oktoba, kuma ƴan takara sun gudanar da gangami a sassa daban-daban duk da cewa ba a ga shugaban ƙasar mai shekara 92, Paul Biya ya fara nasa gangamin ba.
Yayin da zaɓen ke ƙaratowa ɗaya daga cikin ƴan takara 12 da aka tantance domin shiga zaɓen, Caxton Seta Ateki, ya janye tare da sanar da goyon bayan sa ga Bello Bouba Maigari, wani tsohon na hannun daman shugaba Biya, wanda kuma ya fito daga yankin Arewa mai ƙuri'u masu yawa.
"Bayan nazari da idon basira da kuma tuntuɓar waɗanda suka dace, ina sanar da janyewa ta daga takara da kuma goyon bayan Mr. Bello Bouba Maigari," in ji sanarwar Mr. Ateki.
Ya ce ya ɗauki matakin ne saboda kiraye-kirayen da ake ta yi tsakanin ƴan adawa cewa a yi haɗaka domin goyon bayan ɗan takarar da ya fi cancanta don ƙalubalantar shugaba Paul Biya.
A wajen ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa a Yaoundé, babban birnin ƙasar Mr. Maigari ya yi alƙawarin kafa gwamnatin haɗin kai inda kowanne mutum zai bayar da gudunmuwa ga ci gaban ƙasar sa.
Ya ce "Lokaci ya yi na kafa tarihi," yana mai neman ƴan takarar su haɗa ƙarfi da ƙarfe domin ɓullo da wata haɗaka da za ta kai ƴan adawa ga nasara.
Sai dai duk da ƙawancen da aka ƙulla tsakanin Maigari da Ateki, ministan harkokin cikin gida, Paul Atanga Nji ya ce an riga na wuce lokacin da hukumar zaɓe za ta iya amincewa da duk wata haɗakar jam'iyyu.
Ya yi zargin cewa akwai wasu ƴan takara masu neman tayar da zaune tsaye ta hanyar kawo cikas ga tsarin zaɓen da gudanar da zanga zanga da kuma yaɗa sakamakon ƙarya.
Yayin da ƴan takarar shugaban ƙasa a zaɓen mai zuwa suka fara gangamin neman zaɓe a ranar Asabar, ba a ga shugaba Paul Biya yana gangami ba.
Ƴan kwanaki kafin fara yaƙin neman zaɓen, shugaba Biya ya tsallake zuwa Turai, inda bayanai ke cewa zai yi wasu harkokin kansa.
Amma an ga yadda ministocin gwamnatinsa suka fantsama sassan ƙasar domin nema masa magoya baya.
Amma shugaba Biya ya wallafa wani bidiyon sa da aka haɗa da ƙirƙirarriyar basira, inda aka ganshi yana lissafa nasarorin gwamnatinsa da kuma ɗaukar sabbin alƙawurra.
Bayan shafe aƙalla shekara 43 a kan mulki, shugaba Biya ya sake yuƙurowa domin neman nasara.
"Shugaban ƙasa ne wanda tun muna matasa ya riga ya yi mana komai na rayuwa,'' In ji wani masoyin Biya a birnin Yaoundé.
Nan da makonni biyu nan gaba, ƴan takara za su zagaya sassan ƙasar domin neman goyon bayan su.










