Me hana Sule Lamido fom ɗin takarar shugabancin PDP ke nufi?

Lamido

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 5

Da yammacin ranar Litinin ɗin nan ne, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamiɗo ya yi ƙorafin cewa ya je sayen fom na neman shugabancin jam'iyyar PDP amma an ƙi sayar masa.

Sai dai tsohon gwamnan jihar ta Jigawa, Sule Lamido ya ce babu gudu babu ja da baya kan yunƙurinsa na tsayawa takarar shugabancin jam'iyyar PDP duk da kasancewar bai samu damar mallakar fom ɗin tsayawa takarar ba.

Wannan dai na zuwa ne ƴan kwanaki bayan da gwamnonin jam'iyyar PDP suka ayyana tsohon ministan ayyuka na musamman, Kabiru Tanimu Turaki a matsayin ɗantakarar shugabancin jam'iyyar ba tare da hamayya ba daga yankin arewa maso yamma, to amma jiga-jigan ƴan jam'iyyar a yankin suka yi watsi da ayyanawar.

Uwar jam'iyyar ce dai ta amince da miƙa wa shiyyar muƙamin shugabancin jam'iyyar, amma da sharaɗin sai an tuntuɓi masu ruwa da tsaki a yankin.

Hakan dai na ƙara fito da rikicin da ke jam'iyyar ta PDP ne a fili musamman a daidai lokacin da ya rage mata ƴan makonni ta shirya babban taronta na ƙasa a watan Nuwamba wanda yake cike da taƙaddama.

Shin ko me ya sa aka ƙi sayar wa da Sule Lamiɗon fom ɗin? Me hakan yake nufi? Mene ne alaƙar hakan da batun takarar Kabiru Turaki da ke fuskantar turjiya daga gaggan ƴan jam'iyyar da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya?

Yadda aka yi min kora da hali - Sule Lamiɗo

A zantawarsa da BBC, Lamido ya ce an yi masa kora da hali a hedikwatar jam'iyyar ta PDP.

"Na zo hedkwatar PDP ne domin mallakar fom na takarar shugabancin PDP, amma na samu ofishin da ya kamata in je a kulle, da na tambaya sai aka ce min a hannun gwamnan Adamawa ne zan samu fom ɗin. Yanzu ana nufin sai na je Yola ne zan samu fom na takarar?"

Ya ce ba ya fata a kai ga matakin da za a hana shi shiga takarar, "domin ina tunanin rigimar cikin gida ne, kuma za mu iya samun maslaha a cikin gida. Amma idan hakan bai yiwu ba, to na san me zan yi," in ji shi.

Sule Lamido ya ce a shirye yake ya tsaya takarar shugabancin jam'iyyar a zaɓen da za a yi lokacin babban taron jam'iyyar na cikin watan Nuwamban a birnin Ibadan na jihar Oyo.

Tsohon ministan harkokin wajen Najeriyar, ya sha alwashin tafiya kotu idan har aka ƙi sayar masa da Takardar tsayawa takarar.

Tanimu Turaki ya sayi fom ɗin takarar PDP

PDP

Asalin hoton, Official Peoples Democratic Party (PDP) Nigeria

Bayanan hoto, Lokacin da Kabiru Tanimu Turaki ya mayar da fom ɗinsa na takarar
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yayin da a hannun ɗaya aka ƙi sayar wa da tsohon gwamnan Jigawa fom ɗin takarar shugabancin jam'iyyar ta hamayya wato PDP, shi kuwa tsohon ministan ayyuka na musamman, Kabiru Tanimu Turaki ya yanki nasa fom ɗin.

Da yammacin ranar Litinin ne jam'iyyar PDP ta wallafa wata sanarwa da ma hotunan lokacin da Kabiru Turakin ya je hedikwatar domin sayen fom ɗin.

"Ga ni na dawo da fom kamar yadda dokokokin jma'iyyarmu ta PDP suka tanada," in ji Kabiru Tanimu.

Jam'iyyar PDP ta sanar da ɗage tantance ƴan takara daga ranar Talata zuwa wani lokaci a gaba duk da cewa jam'iyyar ba ta faɗi dalilin yin hakan ba.

Sanar da Kabiru Tanimu Turaki a matsayin ɗantakarar maslaha daga arewacin Najeriya ya bar baya da ƙura, inda wasu daga cikin shugabannin jam'iyyar PDP na shiyyar arewa maso yammacin ƙasar, shiyyar da Turaki ya fito suka yi watsi da matakin da gwamnoni suka dauƙa.

Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Sokoto, Muhammad Bello Aliyu na cikin shugabannin da suka yi fatali da matakin da gwamnonin suka ɗauka, saboda a cewarsa, ba a ba su damar zama su tattauna ba, gabannin tsayar da Turaki haka ma an samu wasu jiga-jigan jam'iyyar daga jihar Kebbi da suka yi fatali da maslahar.

Me hakan ke nufi?

A game da abin da wanan sabuwar rigimar ke nufi, Dokta Kabiru Sa'id Sufi, malami a kwalejin ilimi da share fagen shiga jami'a da ke Kano kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum ya ce ana neman fama karaya ne a yunƙurin gyara targaɗe.

"Mun ɗauka cewa tunda aka zo batun zaɓen shugabanci, to matsalolin da jam'iyyar ke ciki sun kusa zuwa ƙarse musammman ganin har an yi ƙoƙarin rarraba muƙamai zuwa shiyya-shiyya, amma kuma sai hakan ya bar baya da ƙura.

"Yanzu haka an fara samun ƙorafi daga ɓangarori da dama, ciki har da daga waɗanda ake ganin ba su da wata matsala."

Ya ce hana Sule Lamido sayen fom ɗin takarar shugabancin jam'iyyar babban al'amari, inda ya ce hakan ya ƙara haifar da rashin gamsuwa a tsakanin ƴaƴan jam'iyyar.

"Dama akwai wasu da suke ganin an lasa musu zuma a baki a arewacin ƙasar na tsayawa takara, sai daga baya suka ga ba da gaske ake ba. Idan aka duba za a ga akwai rashin gamsuwa daga ɓangarori da yawa. Ko ɓangaren Shekarau ma sun nuna rashin gamsuwa da yadda ake tafiyar da al'amura."

Ita dai jam'iyyar PDP, wadda ita ce babbar jam'iyyar hamayya a ƙasar ta fara fama da rikice-rikicen cikin gida ne tun bayan da ta sha kaye a hannun APC a zamanin da tsohon shugaban ƙasar, Marigayi Muhammadu Buhari ya doke shugaban ƙasar na wancan lokacin, Goodluck Jonathan.

Abin da zai iya faruwa

Yanzu hak dai wasu na zargin akwai masu saka hannu a rigimar ta PDP, inda wasu ke zargin babbar jam'iyyar ƙasar a yunƙurin jefa ta cikin rikici da hana ta sukunin ballanta ta shirya shiga zaɓe.

Kabiru Sufi ya ce yanzu haka akwai manyan ɓangarori biyu a wannan rikita-rikitar da ake yi.

"Wasu na tunanin cewa akwai wasu ƴan waje da suka hana jam'iyyar sakat a baya da suke neman sake bi ta wata hanyar domin tabbatar jam'iyyar na ci gaba da zama cikin matsala."

"Wasu kuma na ganin ai waɗanda suke ciki ne da suke yunƙurin magance matsalolin baya, amma sai kuma suke haifar da wasu matsalolin a yanzu. Koma dai mene ne, wannan na nuna cewa akwai matsala babba wajen samar da shugabanci da zai samu karɓuwa baki ɗaya."

A game da abin da zai iya faruwa bayan zaɓen, masanin siyasar ya ce akwai wasu matakai da suke da muhimmanci ga duk wanda ya lashe zaɓen:

  • Irin karɓuwar da zai samu wajen waɗanda ba su ji daɗi ba
  • Matakan da zai ɗauko wajen jawo su jiki
  • Matakan da zai ɗauki wajen matsalolin baya.

Sai dai Sufi ya ce PDP na buƙatar mutum jajirtacce, "wanda zai iya ɗaukar waɗannan matakan, to lallai shugabancin zai shiga tsaka mai wuya."

Ya ƙara da cewa PDP na buƙatar gyara domin ci gaba da kasancewa babbar jam'iyyar hamayya, "idan kuma ta gaza magance matsalolinta, to sai dai ADC ta karɓi ragamar babbar jam'iyyar hamayya."