Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda 'talauci' ke ingiza mutane suna sayar da ƙodarsu a Myanmar
- Marubuci, BBC Burmese
- Lokacin karatu: Minti 6
"Ina son mallakar gida sannan na biya tarin basukan da ake bi na - wannan shi ne dalilin da ya sa na yanke shawarar sayar da ƙodata," a cewar Zeya, wani ɗan barema a wata gona a Myanmar.
Farashin kayayyaki sun yi tashin gwaron zabo a ƙasar bayan juyin mulkin 2021, lamarin da ya haifar da yaƙin basasa. Baya iya ciyar da iyalansa kuma ya faɗa cikin masifar bashi.
Suna zaune a gidan surukarsa a wani ƙauye mai cike da bukkoki mai nisan tafiyar ƴan sa'o'i a mota daga babban birnin ƙasar, Yangon.
Zeya, wanda muka sauya sunansa domin ɓoye shi, ya ce ya san wasu ƴan ƙauyen da suka sayar da ƙodarsu.
"Kuma suna nan kalau da su babu abin da ya same su," in ji shi. Daga nan sai ya riƙa tuntuɓar abokansa.
Yana ɗaya daga cikin mutum takwas da suka shaida wa BBc cewa sun sayar da ƙodarsu bayan da suka yi bulaguro zuwa Indiya.
Safarar sassan jikin ɗan'adam babbar matsala ce a yankin Asia, kuma labarin Zeya ya bayar da haske kan yadda ake safarar.
Yadda ake shirya safarar
Saye da sayar da sassan jikin ɗan'adam haramtaccen al'amari ne a Myanmar da Indiya, amma ya ce cikin sauƙi ya samu mutumin da ya bayyana da wanda ya ''tsara shirin''.
A Indiya, idan wanda ya bayar da ƙodar da wanda aka bai wa ba ƴan'uwan juna ba ne, dole ne su nuna hujjar tausayawa da jinƙai sannan su yi bayanin dangantat da ke tsakaninsu.
Zeya ya ce wanda ya tsara shirin kan ƙirƙiri takardun boge, waɗanda kowa a ƙauyen na da su, ɗauke da cikakkun bayanan iyalansu.
"Ya sanya sunana cikin ƴan uwan wanda za a bai wa ƙodar," in ji shi.
Ya ce wanda ya tsara shirin ya sanya sunanasa a matsayin wanda zai bayar da ƙodar ga wani da suka haɗa dangi ta hanyar aure - ''wato wanda ba ɗan'uwan jini ba ne, amma akwai ɗan ziri a tsakanin''.
Ya ce mutumin ya ɗauke shi zuwa wurin wanda zai sayi ƙodar a Yangon.
A nan ne wani mutum da ya bayyana kansa a matsayin likita ya gama cike takardu, annan ya gargadi Zeya cewa zai biya kuɗi idan aka ƙare aikin.
BBC ta tuntuɓi mutumin daga baya, wanda ya ce aikinsa shi ne ya tababtar da cewa za a iya yi wa mutum irin wannan aiki, ba wai batun dangantae bai saya da mai sayen ƙodar ba.
Zeya ya ce an shaida masa cewa za a biya shi kyats (kuɗin Myanmar) miliyan 7.5, kwatankwacin dala 1,700 zuwa 2,700 cikin wasu shekaru masu zuwa.
Ya ce an ɗauke shi zuwa arewacin Indiya domin yin aikin, an kuma yi aikin a wani babban asibiti.
Dole ne a samu amincewar kwamitin bayar da dama - da asibiti ko gwamnati suka kafa - domin yi wa ƴan ƙasashen waje dashe a Indiya.
Zeya ya ce wasu mutum huɗu sun tattauana da shi kafin yi masa aikin, ta hanyar tafinta.
"Sun tambaye ni ko ni nayi niyyar bayar da ƙodar bisa raɗin kai, ba tilastani aka yi ba," in ji shi.
Ya ce ya faɗa musu cewa ɗan'uwansa zai bai wa ƙodar kuma an amince da dashen.
Zeya ya tuna lokacin da likitan ya yi masa allurar kashe raɗaɗi kafin ya fita hayyacinsa.
"Ba a samu wata matsala bayan tiyatar ba, sai dai kawai ɗn zafin da na riƙa ji idan ina tafiya," in ji shi, inda ya ce ya zauna a asibiti na mako guda kafin a sallame shi.
'Mahaifiyar boge'
Wani da ya taɓa bayar da ƙodar, Myo Win - wanda shi ma muka ɓoye sunansa na asali - ya faɗa wa BBC cewa ya faɗa wa masu binciken cewa ɗan'uwansa zai bai wa ƙodar.
"Wanda ya tsara aikin, ya ba ni takarda, kuma ina iya tuna abin da aka rubuta a kan takardar ," in ji shi, inda ya ce an faɗa cewa ya ce wanda zai bai wa ƙodar mijin ƴar'uwarsa ne.
"Likitan da zai min aiki ya kira mahaifiya, amma wanda ya tsara aikin ya shirya min mahaifiyar boge domin amsa kiran,'' in ji shi.
Matar da ta amsa kiran ta tabbatar wa likitan cewa zai bayar da ƙodar ne ga mijin ƴar'uwarsa bisa amincewarta.
Myo Win ya ce an yi masa tayin kuɗi irin wanda ka yi wa Zeya, amma an bayyana su da "kuɗin sadaukarwar", kuma dole ya bai wa wanda ya tsara aikin kashi 10 cikin 100 na kuɗin.
Duka mutanen sun ce an basu kashi ɗaya bisa uku na kuɗin kafin fara aikin. Myo Win ya ce a lokacin da ya shiga ɗakin tiyatar abin da ke ransa shi ne: "Dole fa na bayar da ƙodar nan, tun da na riga na karɗin mutanennan''.
Ya ce ya zaɓi ya sayar da ƙodarsa ne, saboda yadda yake fama da tarin basussuka da kudin maganin jinyar matarsa.
Rashin aikin yi ya ƙaru a Myanmar tun bayan juyin mulki, inda masu zuba jari aga ƙasshen waje suka fice daga ƙasar.
A 2017, kashi ɗaya bisa huɗu na al'ummar ƙasar na zaune cikin talauci - amma zuwa 2023, adadin ya ƙaru zuwa rabin al'ummar ƙasar, a cewar hukumar raya ƙasashe ta Majalisar Dinkin Duniya, UNDP.
Myo Win ya ce wanda ya shirya sayar masa da ƙodar bai ce masa yin hakan laif ba ne. ''Inda na da sani, ba abin da zai sa na yi. Ina tsoron abin da zai sa na ƙare rayuwata a gidan yari.
BBC ba za ambata sunan wani mutum ko wata ƙungiyar mai hannu a ciki domin kare su da kuma kariyar wakilanmu da suka yi hira da su.
Haka kuma wani mutum a Myanmar, da muka ɓoye sunansa, ya faɗa wa BBC cewa ya taimaka wa kusan mutum 10 a suka sayi ko sayar da ƙodarsu ta hanyar tiyata a Indiya.
Ya ce yakan tura mutane zuwa wata ''hukuma'' a Mandalay da ke tsakiyar Mynamar, wanda ya ce ita ce ke shirya yadda aikin ke wakana.
Kame a Indiya
Dashen sassan jiki ya ƙaru da fiye da kashi 50 cikin 100 a faɗin duniya, tun 2010, inda a kowace shekara ake yin kusan 150,000, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya.
Amma WHOn ta ce sassan jikin da ake sayarwa kashi 10 kawai cikin 100 na dashen sasan jikin da ake buƙata a duniya.
Sayar da sassan jiki laifi ne a kusan duka ƙasashen kuma abu ne mai wahala magance matsalar.
A 2007, WHO ta yi ƙiyasin cewa kashi 5 zuwa 10 na dashen sassan jiki da aka yi, ya faru ne ta ɓarauniyar hanya, kuma alƙaluman ka iya ƙaruwa.
A shekarun baya-bayan nan an riƙa samun bayanan sayar da ƙona sakamakon talauci a yankunan Asiya ciki har da Nepal da Pakistan da Indonesia da Afghanistan da Indiya da kuma Bangladesh.
Indiya ta jima da kasancewa cibiyar likitanci kuma matsalar sayar da ƙoda a ƙasar na ci gaba da ƙaruwa, bayan ƙaruwar rahotonnin kafofin yaɗa labarai da binciken 'yan sanda na baya-bayan nan.
A watan Yulin da ya gabata, ƴansandan Indiya sun ce sun kama wasu mutum bakwai kan zargin sayar da ƙoda, ciki har da wata likita ƴan Indiya da mataimakinta.
Ƴansanda sun yi zargin cewa mutanen kan shirya wa talakawan Bangladesh sayar da ƙodarsu, ta hanyar yin amfani da takardun jabu don samun amincewar dashen.
Dr Vijaya Rajakumari, da ke aiki a babban asibitin Indraprastha Apollo da ke Delhi, ana zargin ya gudanar da ayyukan ne a matsayin babban likita mai ziyara a wani asibiti na daban, Yatharth, mai nisan kilomita kaɗan.
Lauyanta ya shaida wa BBC cewa zarge-zargen "ba su da tushe balle makama kuma babu wata shaida da ke nuna", cewa ta yi tiyata ne kawai bayan amincewar kwamitocin bayar da izini, kuma tana yin aiki ne bisa doka.
A cewar dakardun belinta, ba a zarge ta da shirya takardu na jabu ba.
Asibitin Yatharth ya shaida wa BBC cewa duka ayyukan da ya yi bisa hujja ya gudanar da su kuma ya ce zai iya bai wa kowa damar ganin takardun bayanan aikinsa.
'Babu da-na-sani'
A watan Afrilun da ya gabata, wani babban jami'in ma'aikatar lafiya ya rubuta wa jihohin Indiya gargaɗin "ƙaruwar" dashen da ya shafi ƴan ƙasashen waje, sannan ya yi kiran ƙara sanya idanu.
A ƙarƙashin dokokin Indiya, ƴan ƙasashen waje da ke son ba da gudummawa ko karbar sassan jiki dole ne su sami takardu, gami da waɗanda ke nuna alaƙar da ke tsakanin masu bayarwa da wanda za a bai wa, sannan ofishin jakadancin ƙasarsu a Indiya ya tabbatar da bayanan.
BBC ta tuntubi ma'aikatar lafiyar Indiya da ƙungiyar dashen sassan jiki da nama, da kuma gwamnatin sojin Myanmar domin jin ta bakinsu, amma ba ta samu amsa ba.
Wani mai fafutikar kula da lafiyar jama'a a Myanmar, Dr Thurein Hlaing Win, ya ce: "doka ba ta da tasiri."
Ya ƙara da cewa akwai buƙatar masu hannu da shuni su san illar da ke tattare da hakan, waɗanda suka haɗa da zubar jini a lokacin tiyata da kuma lalata wasu sassan sassan jiki, ya ƙara da cewa akwai buƙatar kulawar da ta dace.