An kashe ɗan tsohon shugaban Libya Saif al-Islam Gaddafi

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Nick Springate
- Lokacin karatu: Minti 2
Rahotanni sun ce an kashe Saif al-Islam Gaddafi, ɗa ga tsohon shugaban Libya marigayi Kanar Muammar Gaddafi.
Kamfanin dillancin labarai na Libya ya ce shugaban tafiyar siyasar Saif ne ya sanar da rasuwarsa a ranar Talata.
Saif al-Islam mai shekara 53, shi ne wanda a baya aka yi yakinin cewa zai gaji mahaifinsa marigayi Gaddafi.
‘Yar’uwar Saif ta shaida wa kafar Talabijin ta Libya cewa ya rasu ne a kusa da kan iyakar kasar da Algeria, sai dai ba ta bayyana yadda ya rasun ba.
Babu tabbas kan yadda lamarin ya faru, inda kafafen yada labarai a kasar ta Libya ke bayar da rahotanni mabambanta.
Saif al-Islam Gaddafi ya kasance mutum mafi tasiri kuma wanda aka fi tsoro a Libya bayan mahaifinsa Muammar Gaddafi, wanda ya mulki kasar daga shekarar 1969 har zuwa lokacin da aka kifar da gwamnatinsa kuma aka kashe shi a shekarar 2011.
Saif, wanda aka haifa a shekarar 1972 ya taka muhimmiyar rawa a gabar Libya da kasashen Yamma a shekarun 2000 har zuwa lokacin da aka kifar da gwamnatin mahaifinsa.
Bayan kifar da mahaifinsa, Saif al-Islam Gaddafi - wanda aka zarga da taka muhimmiyar rawa wajen murkushe zanga-zangar adawa da gwamnati - ya sha dauri a hannun wata kungiyar masu dauke da makami na kimanin shekara shida a birnin Zintan.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kotun hukunta manyan laifuka ta yi yunkurin gurfanar da shi kan zargin aikata laifukan take hakkin dan’adam sanadiyyar rawar da ya taka a yunkurin murkushe masu zanga-zanga a shekarar 2011.
A shekarar 2015, wata kotu a Libya ta yanke masa hukuncin kisa duk da ba ya nan.
Ya tsara manufofin Libya da kuma jagorantar muhimman tattaunawar cimma yarjeniyoyi duk da cewa ba ya rike da wani mukamin gwamnati, cikin irin wadannan yarjeniyoyi har da wadda ta sanya mahaifinsa ya jingine shirinsa na mallakar makamin nukiliya.
Cimma yarjejeniyar ta sanya kasashen duniya sun cire takunkuman da suka dora wa kasar ta Libya, kuma wasu sun rika yi wa Saif kallon mutum mai kokarin kawo sauyi a kasar.
Saif ya sha nanata cewa bai yi niyyar gadar mulki daga mahaifinsa ba, inda ya ce mulki “ba gona ba ce da za a gada”.
Sai dai a shekarar 2021 ya sanar da aniyarsa ta takarar shugaban kasa a wani zabe wanda aka dage ba tare da sanya sabon lokacin da za a gudanar da shi ba.











