Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An ci Brazil da Argentina a wasan neman shiga kofin duniya
An doke tawagar Brazil karo na biyar a wasan neman shiga gasar kofin duniya da za a yi a 2026, bayan da Paraguay ta doke ta 1-0.
Ɗan wasan Inter Miami, Diego Gomez ne ya ci wa Paraguay ƙwallon bayan minti na 20 a Asuncion a karawar da Brazil ta kasa kai hari a minti 45 ɗin farko.
Ita kuwa Argentina ta yi rashin nasara 2-1 a hannun Colombia a wasan neman shiga wasannin da za a yi a Amurka da Canada da kuma Mexico a 2026.
Brazil ta yi amfani da mai tsaron ragar Liverpool, Alisson da ɗan wasan Newcastle, Bruno Guimaraes da na West Ham, Lucas Paqueta da uku daga Real Madrid da suka haɗa da Rodrygo da Endrick da kuma Vinicius Jr.
''Ina son na roki gafara a wajen magoya baya, na san cewar abin ba sauki, amma za mu kara ƙwazo,'' in ji Vinicius kamar yadda ya sanar da gidan talabijin Globo na Brazil.
Mai shekara 24 ya ci wa Real Madrid sama da ƙwallo 20 a kowacce kaka uku baya, amma biyar ya ci wa Brazil daga karawa 35, wanda ya kasa zura ƙwallo a raga a kofin duniya a 2022 a Qatar.
An bai wa Dorival Jr aikin horar da Brazil a cikin watan Janairu, inda tawagar ta yi rashin nasara a kwata fainal a Copa America.
Da wannan sakamakon Brazil, mai kofin duniya biyar tana ta biyar a teburin Kudancin Amurka, wadda ta ci wasa uku daga karawa takwwas da ta yi.
Ita kuwa Colombia ta ɗauki fansa a kan Argentina, wadda ta doke ta a wasan karshe ta lashe Copa America a Amurka a wata biyu da ya wuce.
Karo na biyu da Argentina ta yi rashin nasara a fafatawa 18 tun bayan da ta ɗauki kofin duniya a Qatar a 2022.