Yadda ake yaudarar ƴan Kenya domin yi wa Rasha yaƙi a Ukraine

Asalin hoton, Kuloba family
- Marubuci, David Wafula
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Newsday
- Aiko rahoto daga, Nairobi
- Lokacin karatu: Minti 8
Mahaifiyar David Kuloba ta gargaɗe shi game da zuwa Rasha bayan ya karɓi aiki a matsayin mai gadi da wata hukumar ɗaukar ma'aikata ta Kenya ta tallata.
Da farko dangin da ke zaune a ungwar Kibera da ke babban birnin Kenya sun yi farin ciki lokacin da ya ce ya sami aiki a ƙasashen waje.
Matashin mai shekara 22 ya kasance yana yin aikin yau da kullun a Nairobi - daga sayar da gyaɗa zuwa ayyukan gine-gine - kuma ya daɗe yana fatan samun aiki a yankin Gulf.
Amma da mahaifiyarsa ta tambayi ƙasar da zai je, amsar da ya bayar ta girgiza ta.
"Ya nuna mini wayarsa ya ce: 'Duba, Rasha ce," Susan Kuloba ta shaida wa shirin Newsday na BBC.
"Na ce masa: 'Ba ka ga abin da suke nunawa a talabijin game da Rasha ba? Ba shi da kyau," in ji ta.
Amma ɗanta ya dage cewa tayin na gaskiya ne, inda ya shaida mata cewa an yi masa alƙawarin sama da dala 7,000 (£5,250) idan ya iso - kuɗin da zai sauya rayuwar matashin da ba shi da ƙwaƙƙwarar hanyar samun kuɗin shiga.
Duk da rashin amincewa da ta nuna , ya tafi Rasha a cikin watan Agusta ba tare da ya gaya mata ainihin ranar tafiyarsa.
Ta kaɗu lokacin da ya tuntuɓe ta daga baya, ya ce ya zo ya aiko da hotonsa sanye da cikakkun kayan yaƙi.
"Ya ce mini: 'Mama, aikin da aka ce mu zo mu yi an canza, amma wannan ɗin ma ba laifi," in ji ta.

Asalin hoton, Kuloba family
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ɗan nata ya bayyana cewa an bai wa shi da wasu mutanen Kenya horo na tsawon makonni biyu - kuma yana kan hanyarsa ta zuwa yankin da ake gwabza faɗa a Ukraine, wanda Rasha ta mamaye a shekarar 2022.
A cikin ƴan kwanaki, ya gaya mata cewa an yi wa shi da wasu kwanton ɓauna a yankin da sojojin Rasha ke iko da shi. Ta roke shi ya dawo gida.
"Na ce: 'David, don Allah ka bar wurin.' Ya gaya mani: 'Ta yaya zan tafi ? na sanya hannu kan kwantiragi. Ki ba ni aƙalla shekara ɗaya''
"Sai na samu saƙon da nake tsoro," in ji Misis Kuloba.
A ranar 4 ga watan Oktoba. David ya aike mata da saƙon murya yana mai cewa yana shirin shiga yaƙi idan kuma bai tsira ba, yana son ta samu cikakkun bayanan klwantiraginsa na aikin sojan Rasha, wanda aka rubuta da Rashanci.
Ya buƙace ta da ta kai takardun zuwa ofishin jakadancin Rasha idan wani abu ya same shi.
Wannan shine karo na ƙarshe da ta ji daga gare shi.
A cikin rudani da firgita, ta nemi taimako daga wurin abokin ɗanta, wanda ya gaya mata cewa ya ji David ya mutu.
"Na tambayi abokinsa: 'Ta yaya ka sani?' Ya ce: 'Bari in ba ku lambar wakilin da ya karɓe mu a Rasha.'
Misis Kuloba ta aikawa lambar saƙo - daga farko an amsa mata ne cikin harshen Rashanci. Lokacin da ta bayyana kanta, mutumin ya gaya mata cikin Turanci cewa David ya ɓace, ana fargabar ya mutu.
"Ban ji dadin faɗa muku haka game da ɗanku ba," in ji wakilin.

Asalin hoton, Kuloba family
Ta nemi a nuna mata hoton gawarsa, ko kuma ba ta tabbacin cewa David na cikin ɗakin ajiye gawa. Babu wanda ya zo.
Wadda ta ke magana da shi ya gaya mata cewa "ya yi nisa sosai", kuma ya ba ta shawarar cewa ta yi tafiya zuwa Rasha da kanta, ko kuma ta aika wani dangi, abin da ta ce iyalin ba za su iya yi ba.
Daga baya, ya shida mata mata cewa tana da "yancin samun diyya" na mutuwar ɗanta amma kuma, ba tare da an gabatar mata da wata takarda ba.
Misis Kuloba ta ce ta kasa samun tabbaci a hukumance daga hukumomin Rasha a kan batun David. A lokacin da ta ziyarci ofishin jakadancin Rasha da ke Nairobi, jami'an da ke wurin sun gaya mata cewa ba sa hulɗa da sojoji.
Ba ta da masaniyar abin da za ta yi a gaba, tana cike da baƙin ciki: "Yaya za mu fara? Don ba mu san komai ba, ɗan farina ne, na dogara gare shi."
Mahaifin wani ɗan Kenya da ya je aiki a Rasha ya shaida wa BBC cewa an ɗauke shi aiki ne bisa fahimtar cewa zai zama direba - babu alaƙa da faɗa da makami.
Matashin dai ya samu rauni ne a ƙasar Ukraine kuma ya shiga matuƙar damuwa da ya kasa yin magana tun da ya koma gida makonni biyu da suka gabata. BBC ta amince da kada ta bayyana sunansa domin kare lafiyarsa.
Sai dai mahaifinsa ya gano cewa dansa ya tafi ƙasar Rasha ne bayan samun labarin cewa ya samu rauni.
"Ya yi nuni da cewa mutane za su je, kuma na yi ƙoƙarin nuna masa rashin amincewa ta," mahaifin ya shaida wa BBC. "Ina bin yakin tun farko, hankali na bai kwanta ba."
Wakilai sun yi alƙawarin kusan dala 1,500 a wata, in ji shi - "kuɗi ne mai armashi" ga ƙwararren direba a Kenya.
Daga baya ɗan nasa ya gaya masa cewa kamar David Kuloba, na tsawoya samu horon makonni biyu ne kacal kafin a tura shi fagen daga.
"Ya ce an ji masa rauni a daji, kuma ya yi kwanaki biyar bai samu magani ba, yana amfani da maganin kashe radadi," in ji mahaifin.
Daga ƙarshe an kai shi bakin iyaka inda ya samu agajin farko daga baya aka kai shi St Petersburg.
Ya bayyana yadda ya ga "gawarwakin wasu mayaka a warwatse" ya kuma bayyana cewa da yawa irin sa sun rattaba hannu kan kwangiloli na shekara guda ba tare da cikakkiyar fahimtar sharuddan ba, in ji mahaifin.
A watan da ya gabata, ministan harkokin wajen Kenya ya ce kimanin ƴan ƙasar Kenya 200 ne aka san suna yi wa ƙasar Rasha yaƙi kuma ya amince da cewa har yanzu cibiyoyin ɗaukar ma'aikata suna aiki.
Hakan ya biyo bayan labarin da aka samu a watan Satumba cewa an kama wani matashin ɗan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Kenya a Ukraine, yana mai cewa an yaudare shi ya shiga rundunar sojin Rasha.
Yanzu dai gwamnati ta ce ana binciken wasu hukumomin ɗaukar ma'aikata, kuma tuni aka dakatar da lasisin wasu.
Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Kenya Sylvanus Osoro ya shaida wa BBC cewa, "Wasu hukumomi na yaudarar matasa da alƙawarin biyan maƙudan kuɗaɗe. Gwamnati na bin diddigin hukumomin da ke da alaƙa da wannan zamba."
A cikin kimanin hukumomi 130 da aka yi wa rajista a Kenya, kusan biyar ne aka sanya wa ido, inda aka dakatar da uku, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike ka wasu biyu, in ji shi.
Kwamitin tsaro da harkokin ƙasashen waje na majalisar ne ya ɗauki nauyin binciken lamarin kuma ana sa ran hukumomin da aka gayyata za su zayyana yadda suka ɗauki matasa aiki da bayanan da suka bayar da kuma yadda aka gabatar da kwangiloli, inji Osoro.
Amma iyalan da ke da ƴan uwa da ke fafatawa da sojojin Rasha ba zato ba tsammani, sun soki gwamnatin ƙasar kan jinkirin mayar da martani, suna masu cewa ba su samun wani taimako.
Da yake tsokaci kan abin da ake yi na mai do da waɗanda aka yaudara zuwa fagen daga, Osoro ya ce dole ne a bi hanyoyin diflomasiyya.
"Da amincewarsu suk ke sanya hannnu kan kwangiloli, ko da ba su san abin da kwangilar ta ƙunsa ba ," in ji shi. "Ta hanyar diflomasiyya ne kawai za a iya warware wannan lamarin. Ana gudanar da aiki ta wannan ɓangaren."
Ya ce an samu bayannan duk waɗanda aka sani abin ya shafa kuma jami'ai na tabbatar da yanayin da aka sanya hannu kan kwangilar. Sai dai ya ki tabbatar da adadin mutanen Kenya nawa ne suka mutu.
"Ba zan ba da irin wannan rahoton ba. Wannan ba nawa bane," in ji shi. "Abin da zan iya cewa shi ne ana ci gaba da aiki."
Osoro ya ce, ana shirin samar da sabbin dokoki domin tsaurara matakan da suka dace kan hukumomin ɗaukar ma'aikata, ciki har da yin bincike mai tsauri kafin a ba da lasisi.
Batun ya wuce Kenya. Hukumomi a ƙasashen Afirka da dama sun ba da rahoton cewa an tuntuɓi matasa da tayin aiki mai tsoka a Rasha wanda daga baya ya kai ga ɗaukarsu aikin soja.
Iyalai da dama suna ɗari-ɗari wurin yin magana a bainar jama'a, suna tsoron tsangwama da kuma rashin tabbas game da tasirin shari'a ga ƴan uwansu da ke ƙasashen waje.
A Afirka ta Kudu dai ya zama babbar badaƙala bayan da aka yi zargin cewa wata ƴar tsohon shugaban ƙasar Jacob Zuma na da hannu wajen ɗaukar ma'aikata. Ta dai musanta aikata wani laifin.
Jami'an Ukraine sun sha yin gargaɗin cewa duk wanɗanda ke yi wa Rasha yaƙi za a ɗauke su a matsayin mayaƙan ɓangaren hamayya, kuma hanya ɗaya tilo da za su iya bi ita ce su miƙa wuya inda kuma za a ɗauke su matsayin fursunonin yaƙi.
Misis Kuloba har yanzu ba ta da wani tabbaci a hukumance kan makomar danta. Tana son a dawo da gawarsa idan ya mutu.
"Ni kawai zuciyata ta karaya," in ji ta. "Ya so ya taimake mu, ya yi tunanin zai aje ne ya yi aiki mai inganci."










