Mene ne tukwicin zaman lafiya a yaƙin Isra'ila da Hamas?

Gaza war

Asalin hoton, Getty images

Bayanan hoto, Kiraye-kirayen ƙasashen duniya na a tsagaita wuta a Gaza na ƙaruwa inda Majalisar Ɗinkin Duniya ta zartar da wani ƙuduri da ba lallai a yi aiki da shi ba a ranar Laraba
    • Marubuci, Daga Jeremy Bowen
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Editan BBC kan al'amuran duniya a Ƙudus

Yayin da wunin rana ya ƙare, mutum ba shakka, zai ji tsira da rai cikin dare, tamkar wata karama ce a Zirin Gaza.

Falasɗinawa "na roƙon a tabbatar da tsaron rayuka", kamar yadda Philippe Lazzarini, shugaban hukumar kula da Falasɗinawa 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya, babbar hukumar ba da agaji da ke aiki a Gaza, ya rubuta game da wani "matsanancin abin takaici, maras ƙarewa... jahannama a doron ƙasa".

Lamarin tamkar wata masifa ce ga mutanen da Hamas ta kama tana garkuwa da su, da kuma ga dangin mutanen da aka kashe. Yaƙi wani mugun ramin wuta ne da ke jefa ɗan'adam cikin masifaffen raɗaɗi. Sai dai zafinsa na iya kawo wasu sauye-sauyen da za a ga kamar ba za su yiwu ba.

Hakan ya faru a yammacin nahiyar Turai bayan Yaƙin Duniya na Biyu, Tsoffin abokan gaba biyu waɗanda suka yi ta karkashe juna tsawon ƙarnoni a baya, daga bisani suka zaɓi su zauna lafiya. Ko yaƙin Gaza zai fargar da 'yan Isra'ila da Falasɗinawa su kawo ƙrshen rikicin da ya shafe tsawon ƙarni a kan mallakar ƙasar da ke shimfiɗe a tsakanin Tekun Bahar Rum zuwa Kogin Jordan?

Matar marigayi Muhammad Abu Shaar

Gaza war

Asalin hoton, GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Mutum 18,600 aka kashe a Gaza tun fara yaƙin, a cewar alƙaluman ma'aikatar lafiya ta ƙarƙashin mulkin Hamas

Na yi ta kallon wani bidiyo na wata mata da tsananin takaici ya gigita ta, lokacin da take zaune a kusa da gawar mijinta, Muhammad Abu Shaar. Ganin Isra'ila da Masar ba sa barin 'yan jarida su shiga Gaza, ban iya ganawa da ita ba. Amma na yi ƙoƙarin samo sunanta, wanda ba a wallafa ba a kusa da na mijin da ƙananan yaranta da suka rasu.

A cikin bidiyon, kamar dai tana fata, ko ta yaya, ƙarfin ɓacin ran da take ciki zai dawo da shi duniya.

"Na rantse, mun yi alƙawarin cewa za mu mutu tare. Yanzu ga shi ka mutu ka bar ni. Yanzu yaya za mu yi, don Allah? Muhammad, ka tashi! Don Allah, don ma'aikin Allah abin ƙaunata, wallahi na rantse da Allah, ina son ka. Don Allah ka tashi. 'Ya'yanmu Nour da Aboud suna nan tare da kai. Ka tashi, don Allah."

'Ya'yan biyu na tare da babansu ne saboda dukkansu su ukun Isra'ila ta kashe su. Wani hari ta sama ya ɗaiɗaita gidan da suke fata zai ba su mafaka a Rafah.

Israeli family

Asalin hoton, Family handout

Bayanan hoto, Yonatan Zeigan (hagu) ya bar aiki inda ya koma fafutukar zaman lafiya tamkar mahaifiyarsa fitacciyar 'yar fafutukar zaman lafiya Vivian Silver (a tsakiya), wadda aka kashe a harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Na ziyarci Yonatan Zeigen a gidansa da ke Tel Aviv. Gida ne na jin daɗin rayuwa mai cike da kayan wasan 'ya'yansa. Cikin hotunan danginsa na iya shaida mahaifiyarsa, Vivian Silver, wadda tana ɗaya daga cikin manyan 'yan fafutuka a Isra'ila na cimma zaman lafiya da Falasɗinawa. Vivian tana gidan danginta a kibbutz Be'eri, da ke kan iyaka da Gaza, lokacin da Hamas ta kai hari ranar 7 ga watan Oktoba.

Karon farko da na gamu da Yonatan, kwanaki kaɗan bayan harin da aka kai musu a kibbutz, yana fatan an ɗauki mahaifiyarsa an kai ta Gaza a matsayin garkuwa.

Lokacin da ya ji kukan jiniyar da ke gargaɗin an kawo hari ta sama a Tel Aviv, ya buga wa Vivian wayar tarho. Suka koma kan WhatsApp a lokacin da suka ji ƙarar harbin bindiga da abubuwan fashewa a kibbutz, suna fatan idan ba ta yi hayaniya ba, Hamas za ta tsallake gidan.

Ya karanto saƙonnin da suka yi musaya, da farko cikin barkwanci sai kuma kwatsam abu ya rikiɗe zuwa magana ta haƙiƙa mai cike da nuna so da ƙauna lokacin da ta fahimci cewa kisan kiyashi na faruwa.

"Ta rubuto mini, sun shigo cikin gidan, lokaci ya yi da za mu daina tsokana mu yi bankwana da juna," ta faɗa min.

"Ni ma na rubuta mata amsa cewa 'Ina ƙaunar ki, Umma. Ba ni da sauran kalami, ina tare da ke'. Daga nan sai ta ce, 'Ina jin ka har cikin zuciyata'. Daga nan shi kenan kuma, wannan ne saƙon ƙarshe."

Israeli family

Asalin hoton, OREN ROSENFIELD

Bayanan hoto, Wani zane na jikokin Vivian da ke cewa, "Ina tsoron cewa kakata za ta mutu"

Washe gari, na je gidanta a kibbutz kuma na ga an ƙone shi gaba ɗaya. Sai da aka shafe makonni kafin masu bincike su iya gano sauran gangar jikin Vivian Silver a cikin toka a ɗakin laɓewa. Yonatan ya bar aikinsa a matsayin jami'in kyautata zamantakewa ya koma fafutukar zaman lafiya.

"Sun shigo cikin ƙasata sun kashe mahaifiyata ne saboda ba mu da zaman lafiya. Don haka, a gare ni, wannan kawai wata manuniya ce cewa abin da muke buƙata kenan," in ji shi.

"Hakan na iya faruwa a kowanne ɓangare. Bala'o'i kamar wannan na haifar da sauye-sauye a duniya. Kuma na yi imani zai kai ga wata kyakkyawar makoma a gaba."

Issa Amro

Issa Amro Bafalasɗine ne ɗan fafutuka a Hebron da ke Gaɓar Yamma. Birni ne mai tsarki ga Musulmai da Yahudawa, waɗanda ke ganin darajarsa a matsayin wurin da aka binne Annabi Ibrahim. Wuri ne da ya saba ganin ɓarkewar tarzoma tsawon shekaru gommai.

Issa sananne ne a Hebron kuma sojojin Isra'ila, waɗanda ke tursasa aiki da wata dokar hana fita ga Falasɗinawan da ke zaune a kusa da matsugunnan Yahudawa da ke tsakiyar birnin, na ɗaukan sa a matsayin mai neman fitina. Ya faɗa mini an tsare shi kuma an yi masa duka bayan hare-haren 7 ga watan Oktoba.

A Palestinian peace activist

Asalin hoton, KATHY LONG/BBC

Bayanan hoto, Ɗan fafutuka Issa Amro ya ce rayuwa ga Falasɗiwan da ke Gaɓar Yamma ta ƙara zama mai wahala tun bayan 7 ga watan Oktoba

Kamar Yonatan Zeigen a Tel Aviv, Issa Amro ya yi imani cewa yaƙin zai iya haifar da wata dama ga 'yan Isra'ila da Falasdinawa su samu ingantacciyar rayuwa mafi aminci.

"Ina jin damammaki ne guda biyu. Ko dai mu zaɓi mu zurfafa ko mu ƙara munin lamarin, ko kuma mu mayar da shi wata dama ta warware wannan rikici da kawo ƙarshen mamaye, da warware zaman wariyar al'umma, mu sanya zama tare ya kasance mai yiwuwa saboda masalahar amfani da dakarun tsaro ta gaza… zaman lafiya ne kawai mafita."

Yiwuwar samun zaman lafiya

Duk yaƙe-yaƙen da aka yi a ciki da kewayen Gaza tun da Hamas ta karɓi iko a can cikin shekara ta 2007, sun kawo ƙarshe ne ta hanya iri ɗaya, da Yarjejeniyar tsagaita wuta.

Yarjeniyoyin tsagaita wutan, duka na zuwa ne wawar ɓaraka wadda za ta bayar da tabbacin samun yaƙi na gaba tsakanin Isra'ila da Hamas. Hakan na faruwa ne saboda babu wani yunƙuri da aka yi don kawo ƙarshen rikicin tsawon ƙarni guda tsakanin Falasɗinawa da Isra'ilawa.

Kashe-kashe da ruguje-rugujen da ake yi a wannan yaƙin irin waɗanda suka sha bamban ne da sauran ta yadda babu wani da zai yi gangancin cewa akwai daidan da za a koma kai.

Wannan karo dole ne ya kasance na daban. Yawan karɓar hakan a tsakanin Falasɗinawa da 'yan Isra'ila shi ne abin da ya fi damun al'ummar duniyar da ke waje.

Palestinian activist

Asalin hoton, ISSA AMRO

Bayanan hoto, Bafalasɗine ɗan fafutuka Issa Amro ya faɗa wa BBC an ɗaure hannuwansa katamau lokacin da dakarun sojin Isra'ila suka tsare shi ranar 7 ga watan Oktoba har sai da ya yi shaci

Matsalar ita ce a yarda wacce makoma za a yi ƙoƙarin samar. Gwamnatin Isra'ila na da nufin cimma masalahar diflomasiyya da Amurka, ƙawarta mafi muhimmanci, game da abin da zai faru bayan tsagaita wuta.

Shugaba Joe Biden ya fusata kan abin da ya kira "hare-haren bam ba-ji-ba-gani" da Isra'ila ke yi a Gaza.

Duk da haka, ya ci gaba da goyon bayan Isra'ila, kamar ya yadda ya faro tun lokacin da aka fara yaƙi, ta hanyar tura jiragen ruwan yaƙi masu ɗaukar jiragen sama na sojoji da aika ɗumbin makamai da kuma hawa kujerar na-ƙi ga ƙudurorin Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke neman a tsagaita wuta.

A madadin haka, Joe Biden na son Isra'ila ta amince da cewa mafita guda ɗaya kawai ita ce ta farfaɗo da tattaunawa don kafa ƙasar Falasɗinawa mai 'yancin kanta. Wannan ce manufar yarjejeniyar zaman lafiya ta Oslo, wadda ta gaza aiki bayan shafe shekaru ana tattaunawa.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu bai yi magana mai yawa ba kan yadda za a mulki Gaza, idan da kuma lokacin da aka ayyana samun nasara a kan Hamas. Sai dai ya ƙi amincewa da shirin Joe Biden.

Wani abu da bai canza ba a tsawon dogon tarihin siyasar Netanyahu shi ne adawarsa ga batun kafa ƙasar Falasɗinawa mai 'yancin kanta da yarjejeniyar Oslo ta yi ƙoƙari amma ta gaza samarwa.

Samun nasara gaba ɗaya da kuma miƙa wuya ba tare da wani sharaɗi ba ga duk wanda aka bari da rai daga ɓangaren Hamas su ne manufofin Isra'ila. Shafe Hamas daga doron duniya, kamar yadda Mista Netanyahu ya yi imani, ita ce hanya kawai da za a kuɓutar da mutanen da ake garkuwa da su.

Sa'o'i ƙalilan kafin Joe Biden ya ce luguden bama-baman da Isra'ila ke yi, ba-ji-ba-gani, Benjamin Netanyahu ne ya fara nasa jawabi.

"Ba zan bari Isra'ila ta maimata kuskuren da ta yi na Oslo ba," ya ce. "Bayan gagarumar sadaukarwar fararen hulanmu da sojojinmu, ba zan bar damar shiga Gaza ga waɗanda ke ba da ilmi don aikata ta'addanci ba da goyon bayan ta'addanci da samar da kuɗin aikata ta'addanci. Gaza ba za ta kasance a hannun Hamastan ko Fatahstan ba."

Fatahstan wani shaguɓe da ake bayyana Hukumar Falasɗinawa, mai adawa da Hamas, wadda kuma ta yarda da Isra'ila har ma take aiki tare da ita kan harkokin tsaro.

Siyasar cikin gidan Isra'ila na da alaƙa da lissafin Benjamin Netanyahu. Alƙaluman ra'ayoyin jama'a na nuna cewa 'yan Isra'ila da yawa ne ke ɗora masa alhaki kan gazawar tsaro da ta tattara bayanan sirrin da suka janyo Hamas ta kutsa cikin Isra'ila da irin wannan ƙarfi.

Ta hanyar ninka adawarsa ga samun 'yancin Falasɗinawa, Mista Netanyahu na ƙoƙarin sake samun yarda daga Yahudawa masu tsananin kishin ƙasa da tsaurin ra'ayi, waɗanda ke mara wa gwamnatinsa baya.

Gaza barrier

Asalin hoton, Fred Scott

Bayanan hoto, Katangar Bethlehem - hoto daga Fred Scott

Yonatan Zeigen, ɗan marigayiya mai fafutukar samar da zaman lafiya Vivian Silver, ya ce mahaifiyarsa za ta cika da ƙunci da ta yi tsawon rai, ta ga ɓarkewar yaƙin nan, saboda ta yi imani cewa yaƙi ba ya haddasa komai sai wani yaƙin.

"Ina jin za ta ce 'ba da yawuna ba'… yaƙi, idan mun zama sokwaye ba, kamata ya yi ya zama wani matakin cimma nasara, haka ne? Amma dai muna jin wannan yaƙi wani sanadi ne kawai, na ramuwar gayya."

Yonatan yana jiyo samun wata dama, ta sake shigar da batun zaman lafiya cikin manufar siyasar Isra'ila.

Masu fafutukar zaman lafiya sun yi tashe a Isra'ila har zuwa lokacin da aka riƙa ɓata musu suna yayin da hargitsin Falasɗinawa da makamai ya ɓarke bayan yarjejeniyar Oslo ta karye a shekara ta 2000.

Batun cimma zaman lafiya da Falasɗinawa, sai ya ɓace daga harkokin siyasar al'ummar Isra'ila. A yanzu, Yonatan na fatan, batun na ƙwanƙwasa hanyar dawowa.

"Ba shakka. Ko kalmar ma ba ka isa ka furta ba. Amma yanzu mutane na tattaunawa game da hakan."

Issa Amro, Bafalasɗine ɗan fafutuka a Hebron, ya faɗa min cewa rayuwa a can ta daɗa zama mai wahala ga Falasɗinawa tun bayan hare-haren 7 ga watan Oktoba.

"Abin ya yi muni sosai. Ya yi muni da kamar ninki goma. An samu ƙarin tarnaƙi. Ƙarin tarzoma. Ƙarin razanarwa. Mutane kwata-kwata ba sa cikin aminci.

Mutane ba su da isasshen abincin da za su Mutane ba su da damar samun rayuwar zamantakewa. Ba makarantu. Ba makarantun rainon yara, ba zuwa aiki. Wani hukunci ne a kan kowa da kowa ga duk wanda ke cikin yankin da aka yi matuƙar taƙaice shi."