Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'An mayar da mata tamkar ganimar yaƙi a Sudan'
Rahotannin ƙungiyoyi da hukumomin kare hakkin bil'adama sun nuna cewa mayaƙan rundunar RSF na aikata fyaɗe a birnin Khartoum da kuma yankin Darfur.
Shugaban yanki na na wata ƙungiyar kare hakkin mata, Hala Al-Karib ta faɗa wa BBC cewar rahotannin da ake samu na yawaitar fyaɗe da kisan gilla na da matuƙar firgitarwa.
Ta ce "Ana samun maimaicin abin da ya faru ne a Yammacin Darfur da Nyala da Zelenji, da kuma abin da ya faru a Khartoum gabanin watan Afrilu."
"Dakarun RSF sun karɓe iko da birane...kuma a kowace sa'a muna samun rahotanni na cin zarfai. Duk inda mayaƙan RSF suka ƙwace suna ɗaukar mata da yara ne a matsayin ganima."
"A irin wannan yanayi ne ake cin zarafi ta hanyar lalata a cikin gidajen mutane. Ana yi wa mata fyaɗe a cikin gidajensu. Wannan wata ɗabi'a ce da mayaƙan RSF suka daɗe suna aikatawa."
Mayaƙan na RSF sun ƙwace garuruwa da ma'aikatun gwamnati da kuma sansanonin soji da dama a Wad Madani, wanda shi ne babban birnin jihar Gezira ta tsakiyar ƙasar, bayan gwabaza faɗa.
Artabu ya ƙara ƙazancewa daga ranar Litinin bayan da mayaƙan RSF suka kai farmaki a jihar, wadda take ta yammaci Khartoum.
End of Ƙarin labaran da za ku so ku karanta:
Majalisar Dinkin Duniya ta zargi ƙungiyar da yi wa mutane kisan gilla a Yammacin Darfur bayan gano manyan ƙaburbura - inda a ciki aka gano gawawwakin mata da yara.
Haka nan MDD ɗin ta ce aƙalla yara miliyan uku ne aka tursasa musu yin gudun hijira a cikin wata tara da suka gabata, wanda hakan ya sanya Sudan ta zama ƙasar da yara suka fi shiga tasku a faɗin duniya.
RSF ta dage kan cewa za ta ci gaba da ƙwace yankuna daga hannun gwamnati, wani abu da ke haifar da tsoron ci gaba da tafka ta'asa kan al'umma.
Wata mata da ke zama a gabashin ƙasar ta Sudan ta shaida wa BBC cewar tana magana da mutanen da har yanzu suke a yankin na Wad Madani.
Ta ce "Lamari ya ƙazance a yankin,"
"Kowa a fusace yake. Mutanen Sudan ba su da mai kare su - muna jin tamkar an yi watsi da mu."
"Mayaƙan na kamawa da kashe maza a yankin Darfur da ƴan ƙabilar Nuba saboda ƙabilarsu. Mayaƙan sun haɗa kai da RSF. Su kuma mayaƙan na RSF sun mayar da hankali wajen aiwatar da kisan ƙare-dangi kan ƴan ƙabilar Nuba da kuma mutanen Darfur - suna musu wannan kisa ne kasancewar su baƙaƙe ƴan Afirka."
Wata masaniya kan tsatso da asalin al'umma a jami'ar Toronto, Nisrin Elamin ta ce "tsoma bakin ƙasashen duniya da mugun nufi" shi ne ki iza wutar yaƙin na Sudan.
"Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta riƙa bai wa RSF kuɗaɗe. Mun samu sahihan bayanai da ke cewa tana samar musu da makamai."