Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
A dakatar da jana'izar sirri ga masu zanga-zangar Najeriya da aka kashe - Amnesty
Ƙungiyar Amnesty international ta nemi hukumomin Najeriya su "gaggauta dakatar da shirinsu na gudanar da jana'iza cikin sirri ga ɗumbin mutanen da aka kashe a zanga-zangar #EndSARS" tare da yin cikakken bincike.
Matakin ya zo ne bayan wata takardar hukuma da aka kwarmata mai nuna cewa gwamnatin jihar Legas ta amince da biyan $77,000 don binne ɗumbin mutane su 103 da aka kashe a zanga-zangar EndSars ta 2020, lamarin da ya janyo fushin al'umma a ƙasar.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ɗin ta nemi a gudanar da bincike mai zaman kansa kuma duk waɗanda aka samu da hannu "a gurfanar da su gaban shari'ar adalci."
Wata sanarwa da daraktan ƙungiyar na Najeriya, Mallam Isa Sanusi ya fitar, ta ambato Amnesty na cewa jazaman ne sai gwamnati ta gudanar da binciken ƙwararrun masu gano sanadin mutuwa a kan mutanen da aka kashe yayin zanga-zangar EndSars su 103.
Kuma "a wallafa sunayensu da yadda aka yi suka mutu."
“Abin takaici ne yadda gwamnatin jihar Lagos ta gaza ko ta bayyana cewa tana riƙe da gawawwakin mutanen da aka kashe a zanga-zangar #EndSars a hannunta tun cikin watan Oktoban 2020."
Sai dai gwamnatin ta fitar da wata sanarwa a watan da aka yi tarzomar Endsars inda ta nemi iyaye su je su gani, ko za su shaida tare neman a ba su makusantan nasu. Hukumomi sun ce babu wanda ya je ya ce mamatan 'yan'uwansa ne kuma akwai buƙatar a fitar da su daga ɗakunan ajiyar gawa.
Wata takardar yarjejeniyar binne gawa 103 tsakanin gwamnatin jigar Legas da wani kamfani, da aka bankaɗo a ƙarshen mako ce ta tono wannan zance.
Takardar, ta ƙunshi wata kwangila da ma’aikatar lafiya ta jihar ta bai wa wani kamfani a kan kudi naira miliyan 61,285,000.
Kuma takardar ta bayyana ƙarara cewa an bayar da kwangilar ne domin binne gawa 103 na mutanen da suka mutu a zanga-zangar Endsars da ta faru a 2020.
Tun farko, mutane sun yi tunanin cewa takardar da aka gani tana waɗari a shafukan sada zumunta ta bogi ce, amma bayanin da gwamnatin jihar Legas ta fitar da yammacin ranar Lahadi ya tabbatar da sahihancinta.
Sai dai cikin sanarwar da ta fitar, gwamnatin jihar ta Legas ta ce gawawwakin ba na mutanen da ake zargin sun rasu a mashigin Lekki ba ne, wato Lekki tollgate.
Sanarwar ta kuma ce “Bayan zanga-zangar Endsars, da rikici tsakanin al’umma a unguwannin Fagba, Ketu, Ikorodu, Onota, Ekporo, Ogba, Isolo da Ajah, hukumar kula da muhalli da lafiyar al’umma ta jihar Legas ta tsinci gawawwakin mutane, ciki har da na masu yunƙurin ɓalle gidan yarin Ikoyi.”
“Gawa 103 da aka ambata a takardar na cikin waɗanda rikici ya ritsa da su ne a waɗannan wurare, ba daga gadar Lekki ba, kamar yadda ake zargi.”
Gwamnatin ta jihar Legas ta ce masu neman tayar da zaune tsaye ne kawai suke ƙoƙarin yi wa shirin jana’izar ɗumbin mutane wata mummunar fassara.
Labari ya fara bazuwa ne a ƙarshen mako cewar gwamnatin Legas na shirin yin jana’izar mutanen da aka kashe a lokacin zanga-zangar Endsars, bayan da wani mutum ya wallafa takardar a shafinsa na twitter.
A watan Oktoban 2020 zanga-zanga ta ɓalle a Legas da ma wasu biranen Najeriya domin nuna adawa da ‘zaluncin ‘yan sandan SARS', lamarin da daga baya ya ƙazance ya zama tarzoma.
Lamarin ya yamutse ne bayan ɓata-gari sun ƙwace zanga-zangar ta Endsars, suka fara fashe-fashe da ɓarnata dukiyar gwamnati da ta al’umma.
Taƙaddama daga bisani ta ɓarke bayan an zargi jami’an tsaron Najeriya da buɗe wuta a kan masu zanga-zanga a wata ranar Talata a gadar Lekki da ke birnin na Legas.
Kungiyar Amnesty international ta yi zargin cewa sojojin Najeriya sun kashe masu zanga-zangar lumana aƙalla 12.
Gwamnatin jihar ta Legas dai ta sha musanta zargin, haka nan ma rundunar sojin ta Najeriya.