Real Madrid za ta gabatar da Mbappe ranar Talata a Bernabeu

Kylian Mbappe

Asalin hoton, Getty Images

Ƙungiyar Real Madrid ta sanar cewar ranar Talata za ta gabatar da Kylian Mbappe a gaban magoya bayanta a Santiago Bernabeu.

Shugaban Real Madrid, Florentino Perez ne zai ja ragamar gabatar da ɗan ƙwallon, inda ake sa ran Mbappe zai fara da saka hannu kan ƙunshin ƙwantiragi.

Ƙyaftin ɗin tawagar Faransa zai gana da ƴan jarida da zarar Real Madrid ta yi bikin gabatar da shi gaban magoya baya.

Kylian Mbappe ya amince da komawa Real Madrid daga Paris St-Germain, bayan da yarjejeniyarsa ya kare ranar 30 ga watan Yuni.

Tun cikin watan Fabrairu ɗan ƙwallon tawagar Faransa ya amince baka da baka da cewar zai koma Sifaniya, sannan cikin watan Mayu aka sanar da zai bar PSG a karshen kakar da ta kare.

Tun farko an tsara cewar Mbappe mai shekara 25zai koma Real Madrid ranar 1 ga watan Yuli, lokacin da aka buɗe kasuwar cinikayyar ƴan ƙwallo a La Liga.

To amma a lokacin ana buga gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2024 tare da tawagar Faransa a Jamus.

Sifaniya ce ta fitar da Faransa a zagayen kwata fainal a Euro 2024, inda ƙwallon ɗaya Mbappe ya ci a gasar, itama a bugun fenariti.

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mbappe ya lashe kofin duniya a 2018, kuma shi ne kan gaba a yawan cin ƙwallaye a PSG mai 256 a raga, tun bayan da ya koma ƙungiyar aro daga Monaco a 2017.

Ya amince da yarjejeniyar da za ta kare a Real zuwa karshen 2029, zai ke karbar £12.8m a kowacce kaka da karin ladan £128m da za a biya cikin shekara biyar, kuma zai rike kudin tallace-tallacensa.

Ɗan kasar Faransa zai samu damar buga tamaula tare da Luca Modric, yayin da ɗan ƙwallon Croatia zai kara sa hannu kan yarjejeniyar kaka ɗaya a Real Madrid.

Modric, mai shekara 38, ya shiga wasa daga baya ranar Asabar da Real Madrid ta lashe Champions League na 15 jimilla, bayan da ta doke Borussia Dortmund a Wembley.

Ƙwantiragin tsohon ɗan wasan Tottenham zai kare a karshen watan nan a Real Madrid, amma ana sa ran za a tsawaita masa kaka daya.

Real Madrid ce ta lashe La Liga na bana na 36 jimilla da tazarar maki 10 tsakani da Barcelona, wadda ta yi ta ukun teburin babbar gasar tamaula ta 2023/24.