An aiwatar da hukuncin kisa kan masu fafutuka hudu a Myanmar

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a Myanmar sun aiwatar da hukuncin kisa kan wasu mutum hudu masu fafutukar kare tsarin dimokradiyya, matakin irinsa na farko a kasar cikin gomman shekaru.
Wadanda aka yanke wa hukuncin kisan sun hada da Phyo Zeya Thaw, da marubuci kuma mawallafi Kyaw Min Yu, da Hla Myo Aung da kuma Aung Thura Zawor, matakin da ya janyo mummunar suka daga kasashen duniya.
Gwamnatin mulkin soja ta Myanmar ta sanar da hukuncin kisa kan mutane hudun ne a watan Yuni, kuma ya biyo bayan hambarar da gwamnatin farar hula da sojojin suka yi ne a shekarrar 2021.
Sun dai hambare zababbiyar gwamnatin da jam'iyyar ta National League for Democracy da Aung San Suu Kyi ke jagoranta ne a watan Fabrairun bara, matakin da ya haifar da gagarumar zanga-zanga wadda sojojin suka murkushe cikin hanzari.

Asalin hoton, Getty Images
Wata kafar yada labarai mai suna Global News Light of Myanmar mallakin gwamnatin kasar ta ce an kashe muane hudun saboda an same su da laifukan da suka hada da bayar da umarni da yin shirye-shirye da kuma yin kulle-kullen aikata munanan laifukan ta'addanci.
Sai dai ba ta bayyana yadda aka kashe su ba da lokacin da aka aiwatar da hukuncin a kansu ba.
Mutanen hudu sun hada da Kyaw Min Yu mai shekara 53, wani tsohon mai fafutukar kare hakkin dan Adam wanda ya sha dauri a shekarun baya, da kuma Phyo Zeya Thaw mai shekara 41, wanda tsohon dan majalisa karkashin jam'iyyar NLD, kuma na hannun daman Aung San Suu Kyi ne.
Sauran mutum biyu sune Hla Myo Aung da Aung Thura Zaw - wadanda aka yanke wa hukuncin kisan saboda samun su da laifin kashe wata mata da ake tuhumar tana sanar da gwamnatin mulkin sojan bayanan sirri.
Wata kungiyar da ke kare hakkokin fursunonin siyasa ta ce tun bayan juyin mulkin kasar Myanmar, hukumomi sun kama mutum fiye da 14,800, kuma mutum fiye da 2,100 sun rasa rayukansu a hannun sojojin da ke mulkin kasar.










