Shin ruwan zuma na da amfani ga lafiyarku?

Zuma

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, Ana ba da shawarar shan zuma a daidai saboda har yanzu yana da yawan adadin suga kuma yana haifar da karuwa ciwon suga

Mene ne ruwan zuma?

Ruwan zuma wani ruwa ne mai launin zinari da ƙudan zuma ke samarwa daga kashinta da aka tattara, ruwan zuman na zama a saƙar zuman saboda samar da abinci ga ƙudan zuman a lokacin hunturu.

A tsohuwar Girka, an kwatanta zuma a matsayin 'abincin alloli', yayin da a ƙasar China kuma aka ɗauke ta a matsayin magani.

Bayanan amfanin ruwan zuma wajen gina jiki

A cikin ɗanyen sigar ta, zuma ta ƙunshi amino acid da antioxidants da bitamin da ma'adanai da sukari. Tana kuma da abun da ake kira fructose, wanda ke sanya ruwan zuman zaƙi fiye da sukari amma tare da matsakaicin glycemic index (GI) wanda ke nuna yadda kowane abinci mai gina jiki ke shafar matakin sukarin jininmu (glucose) sai kuma ya taƙaice shi.

Cokali ɗaya na ruwan zuma ya ƙunshi:

• Sinadarin sa kuzari wato kalori 58kcal / 246KJ

• Abinci mai gina jiki gram 15.3

• Sukari gram 15.4

• Furotin gram 0.1

• Kitse gram 0g

Zuma a saƙarta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƙudan zuma ne ke samar da ruwan zuma ta hanyar tattara kashinta, sannan ta adana ruwan a saƙarta

Amfanin ruwan zuma

Amfanin ruwan zuma ga lafiyar jiki ya dogara ne akan yadda ake sarrafa shi da kuma ingancin furanni da ƙudan zuma suke tarawa.

Danyen ruwan zuma, wadda ba a gasa da wuta ba, ko da kitse, ko wanda ba a tace ba ta fi amfani a jiki akan ruwan zuman da aka sarrafa saboda wadda ba a sarrafa ba tana da sinadren da ta zo da shi na gina jiki.

An yi amfani da ruwan zuma a kai a kai a matsayin maganin da ke taimakawa wajen magance raunuka da na ulcer da ƙonewa da kuma hana ci gaban kwayoyin cuta.

Zuma yana da wadataccen sinadarai kamar flavonoids.

An ba da rahoton cewa Flavonoids yana da maganin kashe kwayoyin cuta kuma wasu suna kallon zuma ya fi ƙoshin lafiya kan sukari.

Duk da haka, ruwan tana haifa da adadin kuzari me yawa kuma zai iya haɓaka yawan sukarin da ke jinin jikin mutum wanda yasa aka ba da shawarar a dinga amfani da ruwan zuman kaɗan ba dayawa ba.

Shin ruwan zuma ya fi sukari?

Ruwan zuma yana da matsakaicin glycemic index (GI) wanda ke nuna yadda kowane abinci mai gina jiki ke shafar matakin sukarin jininmu kuma yana iya taƙaicewa amma shi sukari bai da wannan.

Ruwan zuma ya fi sukari zaƙi, saboda haka yana da kyau mutum ya taƙaice shansa dayawa, kuma duk cokali ɗaya na ruwan zuwa yana haifar da kuzari dayawa wato yana da calories sosai, wanda shima aka ce a dinga amfani da ruwan zuman kaɗan.

Idan mutum ya fi son amfani da ruwan zuma, toh ya yi ƙoƙari ya na amfani da wanda ba a sarrafa ba wato ɗanyen ruwan zuamn kenan wanda ya ƙunshi ƙarin bitamin da sauran sinadarai masu gina gida fiye da farin sukari, amma kuma an shawarci mutane da zu yi amfani da kaɗan ba dayawa ba.

Honey and sugar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ruwan zuma ya fi farin sukari zaƙi, saboda haka kaɗan ya kamata ana amfani da shi.

Shin ruwan zuma na kowa ne?

An kwantanta ruwan zuma a matsayin wanda ya fi farin sukari zaƙi wanda hakan yasa aka shawarci mutane da su dinga amfani da kaɗan

Babu wani muhimmin amfanin ruwan zuma ga mutanen da ke da ciwon suga ko kuma waɗanda ke ƙoƙarin rage yawan sukarin da ke cikin jininsu saboda duka suna shafar yawan sukari da ke cikin jinin mutum.

Bugu da ƙari, an ce bai kamata yara ƙasa da shekara guda ba suna amfani da zuman da aka sarrafa ba ko ɗanyen ta saboda zai iya gurɓata musu ciki abin da ake kira 'botulism'

Duk da cewa yawancin mutane sun fi son amfani da ruwan zuma, ba kowa ne ya kamata yana amfani da shi ba