Ƴan majalisa da gwamnatin Najeriya za su ja daga kan ƙarin haraji

National Assembly

Asalin hoton, NASS/Facebook

Lokacin karatu: Minti 3

Bisa ga dukkan alamu za a kai ruwa rana tsakanin ɓangaren shugaban ƙasa a Najeriya da majalisar wakilan ƙasar, bayan da ƴan majalisar suka yi watsi da wasu buƙatu na sauye-sauye kan harajin da ake neman ƙara lafta wa ƴan ƙasar.

Wannan ya biyo bayan wata zazzafar muhawara da aka yi tsakanin ƴan majalisar wakilan bayan gabatar da wani ƙuduri da aka yi wa karatun farko da ke neman a ƙara yawan haraji kan ƴan Najeriya a wasu sassan rayuwarsu.

Majalisar dai ta yi kira ne ga gwamnatin tarayya da ta dakatar da yunƙurin nata ne domin a cewarta babu wani dalilin da ya tilasta yin hakan, inda ta ce tsarin tattalin arziƙin ƙasar a halin yanzu bai haifar wa ƴan ƙasar da komai ba illa rashin aikin yi da tsadar rayuwa.

Hon Ali Sani Madakin Gini shi ne shugaban marassa rinjaye a majalisar kuma yana ɗaya daga cikin waɗanda ke adawa da matakin na gwamnatin tarayya inda ya ce talakawan ƙasar na cikin wani mawuyacin hali kuma duk wani yunƙuri na ƙara masu haraji zai ƙara jefa su cikin wani mummunan yanayi:

''Abinci ya yi wuya, mutane ba su da lafiya ba su da yadda za su kai kansu asibiti, sa'annan kuma ga tsadar man fetur ga kuma yadda darajar Naira ke ƙara durƙushewa, saboda haka a matsayinmu na ƴan majalisa da aka zaɓa domin kare muradin ƴan ƙasa muna ganin wannan ƙari da ake niyyar yi bai dace ba a halin yanzu.''

Hon Sani ya ƙara da cewa duk da majalisa ta amince da cewa gwamnati mai ci ta samu matsaloli da dama a ƙasa kuma mafi yawan abubuwa ba sa tafiya yadda ya kamata a ƙasar, amma ƙarin haraji ba mafita ba ne.

Bayan adawa da wannan ƙuduri ya fuskanta a majalisar, masu fafutuka irin su Kwamared Kabiru Dakata na ƙungiyar CAJA, mai rajin tabbatar da shugabanci na gari a Najeriya ya ce tsarin jari-hujja ake ƙara ɗora ƙasar a kai.

Ya ce: ''Irin waɗannan tsare-tsaren da wannan gwamnatin ta fitar su ne suka sanya ɗaukacin ƴan Najeriya suka fita daga hayyacinsu, talauci ya yi wa kowa katutu kuma an mayar da kowa talaka da ƙarfi da yaji, duk abin da kake siya kafin zuwan wannan gwamnati yanzu ya ninka kuɗinsa sau huɗu.''

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kwamared Kabiru ya kuma yi nuni da cewa ƴan Najeriya sun tagayyara kuma har yanzu gwamnati ba ta ɗauki matakan sawwake masu mawuyacin halin da suke ciki ba, sai dai a kodayaushe a ce abubuwa za su inganta amma har yanzu lamura ba su daidaita ba.

''Cikin ƴan watanni da suka gabata BBC ta yi hira da Kashim Shettima inda ya ce a ba su wata shida zuwa shekara ɗaya abubuwa za su inganta, amma daga wannan lokaci zuwa yanzu abubuwa sun ƙara taɓarɓarewa kuma babu alamar cewa za a iya nemo bakin zaren.'' In ji shi.

Masana harkokin siyasa da shugabanci a Najeriya dai sun ce ya kamata gwamnatin ƙasar ta yi la'akari da halin da talakawanta ke ciki, ta kuma duƙufa wurin samar masu da mafita,

Cikin shekara ɗaya da ƴan watanni da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi tana jagorancin Najeriya ta kawo sauye-sauye da dama a fannin tattalin arziki wanda hakan ya ƙara ta'azzara wahalar rayuwa ga mafi yawan ƴan ƙasar, ko da yake ta ce tana ɗaukar waɗannan matakai ne domin ta inganta tattalin arzikin ƙasar amma dai har yanzu ƴan Najeriya ba su gani a ƙasa ba.