Trump ya faɗi waɗanda ba zai ba muƙami ba a gwamnatinsa

Lokacin karatu: Minti 2

Yayin da ake ci gaba da hasashe a Amurka kan wadanda za a dama da su a sabuwar gwamnatinsa, Donald Trump zababben shugaban kasar ya sanar a kafar sada zumunta cewa ba zai yi aiki da wasu mutum biyu ba a tsohuwar gwamnatinsa.

Wato tsohuwar Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley da tsohon sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, wadanda Mista Trump ya ce ba su cikin lissafin sabuwar gwamnatinsa da zai kafa.

Donald Trump ya gode masu kan aikin da suka yi wa kasa, yana mai cewa ya ji dadin aiki da su amma a saƙon da ya wallafa a kafar sada zumuntarsa ta Truth, Mr Trump ya ce Nikki Haley da Mike Pompeo ba su cikin wadanda zai yi aiki da su a sabuwar gwamnatinsa.

A lokacin zaben fitar da gwani na Republican, Ms Haley ta caccaki Trump inda a wani lokaci ma ta danganta shi da marar hankali – kafin daga bisani ta janye daga takarar, wanda ya ba Trump damar zama dantakara ɗaya tilo a Republican.

Mr Pompeo wanda shi ma ya rike mukamin daraktan hukumar leken asirin Amurka karkashin shugabancin Trump, an yi ta yadawa a kafofin sada zumunta na intanet cewa shi za a ba muƙamin sakataren tsaron Amurka.

Trump ya ce za su kawo masa cikas ga muradunsa na 'Amurka ce farko'

A yayin da yake aiki ta bayan fage kafin rantsar da shi a ranar 20 ga Janairu, Trump zai gana da shugaba Joe Biden a kwanaki masu zuwa.

A ranar Laraba ne shugaba Biden zai karɓi bakuncin Trump, kamar yadda fadar White House ta sanar.

Ganawar za ta haɗa masu hamayya da juna wuri ɗaya a wani mataki na haɗa kan ƙasa bayan kammala yaƙin neman zaɓe da ake gani mafi jan hankali da suka yi ta caccakar juna a tarihin Amurka.

Tun a ranar Asabar ofishin yaƙin neman zaɓen Trump ya sanar da kwamitin karɓar mulki ƙarƙashin jagorancin mutum biyu tsoffin na hannun daman Trump Steve Witkoff da kuma tsohon sanata a jihar Georgia.