Yadda ambaliya ta janyo lalacewar amfanin gona a Najeriya

Lokacin karatu: Minti 3

Yayin da aka fara bikin ranar abinci ta duniya, mamakon ruwan sama da aka fuskanta a yammaci da tsakiyar Afirka ya haddasa ambaliyar ruwa a cikin 'yan watannin nan, da ya shafi miliyoyin mutane, musamman yadda suka yi yi asarar gonakinsu.

Najeriya na daga cikin ƙasashen da aka fuskanci wannan matsala, ta yadda rashin tsayayyen sauyin yanayi ya ƙara ta'azzara matsalar karancin abinci a kasar, sakamakon ambaliyar ruwan da aka fuskanta a kasar.

Wasu gonaki 2 da BBC ta ziyarta a yankin arewa maso gabashin Najeriyar ta shaida yadda fari da ambaliyar ruwa suka janyo asarar kayan amfanin gona mai dimbin yawa.

Halin da gonakin suka shiga

Mema Fwa da mai shekaru 55 ƴar jihar Adamawa da ta shafe shekaru 25 ta na noma, ta ce basu taɓa ganin lalacewar kayan amfanin gona ba kamar na damunar bana ba.

Ta ce gabain ambaliyar ruwa ya rutsa da gonarta, komai ya lalace sakamakon ambaliyar ruwa da suka fuskanta a yankin nasu.

“Na sha wahala sosai sakamakon fari a watanin da suka gabata, a lokacin da amfanin ya fara futowa, sai ambaliyar ruwa ta zo ta lalata daukacin gonar, ko kadan ban ji dadi ba, domin yanzu bazan iya samarwa da iyalina abin da za su ci ba, in ji Mema Fwa.

Shi ma wani manomi da ke jihar Taraba da ke maƙwabtaka da jihar Adamawa, Rabi’u Musa mai shekaru 36 ya ce fiye da shekara biyu ya fadada ƙarmar gonarsa zuwa kadada 30. Kuma yana fatan samun buhu dubu na buhun masara a bana, bayan da ya ƙarɓi bashin banki.

Sai dai wannan murna tasa, ta koma ciki sakamakon ƙarancin ruwan sama na tsawon kwanaki 40, karshe ma sai ya kasance bashi ya biyo shi, da kuma kokawar yadda zai kula da fiye da mutum 40 da ke ƙarƙashinsa.

Sannan ya ce “Mun yi azumi, muna raba masara ga mutane, don neman sauki a wajen Allah. Mutane masu yawa sun rasa jarinsu, wasu kuma sun ma haƙura kacokan. A gaskiya ban ji daɗi ba ko kaɗan. A duk sanda na je gonata, sai na dawo da ciwon kai. Ji na ke yi kamar zan yanke jiki na fadi”, a cewar Rabi’u Musa''

Me hukumomin jihohin ke cewa?

A cewar hukumar majalisar ɗinkin duniya da ke kula da abinci da noma ta ce yan Najiriya miliyan 22 ne ka iya fuskantar yunwa a bana. Sai dai ta ce adadin ka iya karuwa har sau hudu nan da shekarar 2030.

Kouacou Dominique Koffy, ya ce “sauyin yanayi na haifar da koma baya a bangaren tattalin arziki ga manoma. Kuma akwai bukatar a sauya tsarin noma da ake yi a Najeriya na damuna da rani, a koma amfani da sabbin dabaru.

Sadiq Muhammed kwamishinan muhalli ne a jihar Adamawa ya ce suna daukar matakai don shawo kan sauyin yanayin ciki har da samar da ingantatun iri.

Har ila yau ya ce “gwamnatin jiha, ta samar da wani kwamitin samar da abinci wanda ni kaina ina daya daga cikin yan kwamitin, wanda zai wayar da kan monoman, tare da hada hannu da cibiyar bincike da ke Ibadan da za su koya musu amfani da iri da ke jure fari”, inji shi.

Kaso mai yawa na abincin da ake samu a Najeriya na zuwa ne daga arewacin ƙasar, inda yankin arewa maso gabashin ƙasar ke kan gaba wajen samar da shinkafa, da masara da rogo.

A bana jihohhi irinsu Borno, da Adamawa da karin wasu jihohin 27 tuni ambaliyar ruwa ta lalata fiye da rabin miliyan na kadadar gonakin da ake da su a wuraren.