Munanan gobarar tankokin man fetur huɗu a Najeriya

...

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Hatsarin wata tankar dakon man fetur a kan hanyar Abuja, babban birnin Najeriya zuwa Kaduna ya haifar da asarar rayuka sama da 80, yayin da wasu da dama suka samu rauni.

Wannan na zuwa ne ƙasa da shekara ɗaya bayan samun irin wannan hatsari a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin ƙasar, wanda shi kuma ya kashe kusan mutum 200.

Irin waɗannan haɗurra na neman zama ruwan dare duk kuwa da gargaɗin da hukumomi da ɗaiɗaikun mutane ke yi.

Ana alaƙanta yawan samun hakan da rashin ingantattun hanyoyi, da rashin bin dokokin hanya, sai kuma talauci da ke addabar al'umma.

A cikin watannin biyar da suka gabata a Najeriya, an samu haɗarin tankokin mai a lokuta huɗu a faɗin ƙasar da suka yi sanadiyyar asarar rayuka 265, kamar yadda ministan yaɗa labaran Najeriya, Muhamamd Idris ya bayyana.

Ga lokutan da haɗurran suka faru da kuma asarar rayukan da aka yi:

1) Suleja, jihar Neja - 18 ga Janairu 2025

Tankar mai na ci da wuta

Asalin hoton, @nemanigeria/X

A ranar 18 ga watan Janairu ne hukumomi a Jihar Neja da ke arewa ta tsakiya a Najeriya suka tabbatar da mutuwar mutane aƙalla 98 sakamakon fashewar tankar mai a garin Dikko da ke karamar hukumar Gurara a jihar Neja.

Sun kuma ce aƙalla mutane 55 da suka samu raunuka a hatsarin na kwance a babban asibitin Suleja da babban asibitin Sabon Wuse da cibiyar kiwon lafiya a matakin farko da ke garin Dikko.

Wannan shi ne hatsarin tankar dakon man fetur na baya-bayan nan da ya girgiza ƙasar.

2) Taura, Jihar Jigawa - 15 ga watan Oktoba 2024

Fashewar tankar mai

Asalin hoton, FRSC

Hukumomi a jihar Jigawa sun tabbatar da cewa aƙalla mutane 181 ne suka mutu yayin da aƙalla 80 su ka jikkata sakamakon fashewar wata tankar dakon man fetur a garin Majiya na ƙaramar hukumar Taura.

Babbar jami'ar hukumar kiyaye haɗurra a Jigawa, Aishatu Sa'adu, ta ce hatsarin ya faru ne ranar Talata da daddare bayan da direban tankar ya kauce wa wata babbar mota ɗauke da tumatur.

A cewar ta hakan ya sa direban tankar ya faɗa gefen titin har kan motar ya rabu da gangar jikinta, lamarin da ya sa fetur ɗin da yake dako ya malale titi da kwatoci a gefen hanyar.

Shi kuma kakakin rundunar 'yansanda a Jigawa, DSP Lawan Adam, ya ce bayan tankar ta faɗi sai mutane suka yi dafifi a wurin domin kwasar man da ya zuba a ƙasa bayan sun ci ƙarfin jami'an tsaron da ke korarsu a ƙokarin kauce wa tashin gobara.

Shaidu sun faɗa wa BBC cewa tankar ta yi kusan awa biyu tana ci da wuta kafin jami'an kashe gobara su yi nasarar kashe ta.

3) Agaie, jihar Neja - 8 ga watan Satumba 2024

Tankar mai da ta kama da wuta

Kwana ɗaya bayan fashewar tankar dakon man fetur a jihar Oyo, a ranar 8 ga watan Satumban 2025, aƙalla mutane 59 ne suka mutu bayan wata tankar mai ta yi taho mu gama da wata motar da ke ɗauke da mutane da kuma shanu.

Hukumar bayar da agaji ta jihar Neja ta ce haɗarin ya faru ne da safiyar ranar lahadi wanda ya kai ga fashewar tankar da motar ɗaukan kaya da ma wasu motocin.

4) Egbeda, Jihar Oyo - 7 ga watan Satumba 2024

Tankar mai da ya ƙone bayan fashewa

Asalin hoton, Andrew Gift / BBC

A ranar Asabar, bakwai ga watan Satumban 2024, wata tankar man fetur ta kama da wuta a kan titin Ibadan zuwa Ife a ƙaramar hukumar Egbeda da ke jihar Oyo wanda ya yi sanadiyyar ƙonewar motoci huɗu da wasu gidaje.

Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Mista Yemi Akinyinka ya ce binciken farko ya nuna cewa wutar ta kama ne bayan mazauna yankin sun fara yunƙurin ɗibar man fetur ɗin da ke malelewa wanda ya kai ga mutane da dama sun samu raunuka, da dama kuma ya raba su da muhallansu.