Yadda Tiktok ke amfana da bidiyon da 'yan Syria ke yin bara

Wani binciken BBC ya gano cewa shafin sada zumunta na TikTok na amfana da kusan kashi 70 cikin dari na abin da ake sadaukarwa ta hanyarsa ga daruruwan mutanen da ke zaune a sansanonin 'yan gudun hijira a kasar Syria.

A kowace rana Mona Ali Al-Karim tare da 'ya'yanta shida mata kan hau shafin Tiktok, inda suke rokon abubuwan bukatu daga masu kallonsu.

Iyalan kan zauna a cikin tantinsu inda suke shafe sa'o'i suna maimaita kalmomin ''Ku taimaka mana, ku ba mu, ku agaza mana''.

An kashe mijin Mona a wani hari ta sama da aka kai masa. Takan kuma yi amfani da shafin TikTok wajen samun kudin da take kula da 'yarta Sharifa mai lalurar makanta.

Abubuwan da suke bararsu na intanet ne, amma ana iya sayensu da kudi na zahiri, sannan ana cire su daga shafin a matsayin kudi.

Masu kallonsu kan zabi saya musu kyaututtuka na intanet kamar 'furanni, da 'lion' da 'universes' wadanda a zahiri kudinsu zai kai dala 400 zuwa 500.

Iyalan Mona daya ne daga cikin daruruwan iyalai da ke yin bara a shafin na TikTok.

A farkon wannan shekarar wani bidiyo irin wannan ya fara bayyana a shafukan masu amfani da TikTok a fadin duniya, a yayin da wasu ke tunanin cewa 'yan damfara ne, tuni wasu suka fara taimakawa.

Keith Mason, wani dan Birtaniya mai fada a ji a TikTok, ya bayar da tallafin dala 330 ga wasu iyalai da ke bara a shafin.

Keith ya ce 'ya'yan mutumin da ya bai wa sadaka sun yi murna da farin ciki.

''Duk da cewa babansu ya rasa kafafunsa da hannunsa daya sakamakon wani hari ta sama, uba ne da ke kokarin gina iyalansa'', in ji Keith.

Ta yaya suke ke cire kudin?

Ta yaya mutanen da suka rasa muhallansu sakamakon yakin basasa, suka mallaki manyan wayoyi, kuma suke samun intanet tare da hawa shafin TikTok a kowacce rana?

Dan jaridar Syria Mohammed Abdullah ya shaida mana cewa ya gane daya daga cikin sansanin 'yan gudun hijirar da aka nuna a bidiyon, wanda ya ce yana birnin Idlib da ke arewa maso yammacin Syria.

Mun bukaci da ya ziyarci sansanin, yayin da kuma ya hallara a sansanin ya samu iyalai da dama na bara kai-tsaye a shafin TikTok, kamar dai iyalan Mona.

Ya kuma hadu da Hamid, wani matashi da ke taimaka wa iyalai 12 a sansanin domin su yi amfani da shafin.

Shi ke sayar musu da wayoyin, ya kuma samar musu da intanet, sannan ya kula musu da shafin na TikTok, tare da cire musu kudaden da suke samu sakamakon barar da suke yi, su kuma biya shi lada.

Sai dai Hamid ya ce mafi yawan kyaututtukan da ake samu a shafin, TikTok ne ke wawure su kafin ya isa asusunsa na banki.

''Zaki wato 'lion a intanet' ita ce kyauta mafi daraja, wadda ta kai dala 500. Amma a lokacin da ta iso garin Al-Dana sai ta koma dala 155'', in ji Hamid.

Tawagarmu ta biyiyi shafuka fiye da 300 wadanda ake gudanarwa kai-tsaye. kuma mun tarar cewa wasu da yawa kan samu fiye kyautar da dala 1,000 a cikin sa'a guda.

To amma iyalan sun ce sukan samun 'yan kwabbai ne daga zunzurutun kudaden da ake sadaukar musu.

Dowkan Hamdan Al-Khodr na bukatar tara kudin da za a yi wa 'yarsa aikin tiyatar zuciya, bayan shafe kwanaki takwas yana bara kai-tsaye a shafin TikTok ya samu dala 14.

"Bayan haka yanzu na hakura," in ji shi. "Saboda mutane na zargina da cewa ina yi musu karya, domin kuwa a ganinsu zuwa yanzu na samu kudin da nake bukata''

To ina kudin yake tafiya?

Abin da TikTok ke yanka

A watan Yuni, mun aike wa TikTok sako inda muka tambaye su cewa kashi nawa suke dauka a kowacce kyauta da aka bayar ta hanyar shafinsu. Amma ba su ce komai ba.

Don haka muka gwada da kanmu.

Mun shiga shafin TikTok kai-tsaye ta wani shafi da muka bude a Syria, sannan muka tura kyauta ta kusan dala 106 daga wani shafin a birnin Landan.

Bayan da muka kammala, sai muka ga kudin da ke cikin asusun namu na Syria dala 33 ne. TikTok ya dauki kashi 69 cikin 100 na adadin kyautar da muka tura.

Bayan wannan gwaji, sai muka je domin cire kudin namu dala 33 a wani shago da ake cire kudi a kasar.

Su ma sai suka dauki kashi 10 cikin 100, sannan wakilin da ke shiga tsakani kamar Hamid shi ma ya dauki kashi 35 cikin 100 na abin da ya saura.

Wannan ya sa muka tsira da dala 19 daga cikin dala 106 da aka aiko wa shafin namu.

Iyalai da dama sun shaida mana yadda ake biyansu kudade 'yan kalilan.

A yayin da suke kwashe sa'o'i masu yawa kai-tsaye a shafin, Marwa Fatafta daga kungiyar kare hakkin masu amfani da shafukan intanet ta ce suna adawa da tsare-tsren TikTok na cutarwa da ci-da-gumin marasa galihu da ke amfani da shafin.

"Ci-da-gumin mabarata"

Domin gwada yadda TikTok ke amfani da tsarinsa na kare hakkin kananan yara, mun yi amfani da manhajar in-app domin kai rahoton shafuka 30 da ke nuna yadda kananan yara ke bara.

Sai shafin na TikTok ya ce ''ba a saba wa dokar kowane shafi ba."

A lokacin da BBC ta tuntubi TikTok din kai-tsaye, sai ya rufe duka shafukan. Kuma kamfanin bai yadda aka yi hira da shi ba, amma ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar.

"Mun yi matukar damuwa game da labarai da zarge-zargen da BBC suka yi a kanmu, kuma mun dauki matakan da suka dace. Wannan ba abu ne da za mu lamunce da shi a shafinmu ba, kuma muna ci gaba da karfafa dokokinmu game da ci-da-gumin mabarata''.

TikTok shi ne shafin sada zumunta da ke saurin bunkasa a fadin duniya, inda yake da masu amfani da shafin kimanin biliyan 3.9 a fadin duniya. Ya kuma samu fiye da dala biliyan 6.2 daga abin da masu amfani da shi ke kashewa.

Taimaka wa Iyalai

Mun tuntubi kungiyoyin agaji da ke aiki a Syria domin tabbatar da cewa iyalan da muka yi hira da su sun samu taimakon kungiyoyin, a maimakon amfani da shafin TikTok.

Wata kungiyar agaji a kasar mai suna Takaful Alsham ta ce za ta rika samar da kayayyakin bukatu ga iyalan cikin watanni uku masu zuwa.

A yayin da, daruruwan iyalai ke amfani da shafin TikTok a kowacce rana domin neman kudi, kamfanin na kwashe kaso mafi yawa daga kudaden.