Soyayya daga kurkuku: Yadda Musulmi ɗan Afghanistan ya auri Bayahudiya

Lokacin karatu: Minti 7

Lokacin da Kabul ta faɗa hannun Taliban a watan Agustan 2021, duniya ta ga hotunan yadda al'amura suka hargitse sa'ar da 'yan Afghanistan suka yi cincirindo a filin jirgin sama, ido-rufe suna ƙoƙarin tserewa.

A Washington DC, babban birnin Amurka, wani tsohon jami'in lafiya a sojan ruwa mai suna Safi Rauf baki alaikum ya fara wani ƙoƙari na ƙashin kansa: don taimaka wa abokan zama da na aiki waɗanda aka ritsa da su a Afghanistan.

Ya taɓa tunanin cewa a yayin da hidimar kuɓutar da rayuka ba, zai gamu da abokiyar ƙaunarsa - kuma kasancewarsa, Musulmi zai kamu da soyayyar wata bayahudiya wadda addininsu da rayuwarsu suka sha bambam.

"Na ɗan ja aji kafin na fara bai wa wani mutum guda taimako," kamar yadda yake iya tunawa. "Hakan kuma ya yi min rana. Daga nan na taimaki wani, sannan na ƙara taimaka wa wani.

Kwatsam sai lamarin ya zama wani gagarumin aiki, ga ɗaruruwan mutane ƙasa a Afghanistan da kuma mu 'yan gommai a Washington."

Safi, wanda aka haifa a wani sansanin 'yan gudun hijira sannan ya yi ƙaura zuwa Amurka a matsayinsa na matashi, ya samu kansa kace-kace a tsakiyar wani aikin ceto cikin tashin hankali.

A irin wannan hali na tsanani ne ya gamu da Sammi Cannold, wata darakta a dandalin wasan daɓe cikin birnin New York wadda ido-rufe take ƙoƙarin ganin an fitar da wani abokin danginsu daga birnin Kabul.

"Ni gaba ɗaya babu wanda na sani," Sammi ta ce. "Daga nan, sai na ga wani shirin talbijin na musamman game da ayarinsu Safi. Na aika masa rubutaccen saƙo a kan ko zai taimaka mini. Inda ya ce abin da ya fi dacewa shi ne na je Washington na shiga aikin sa-kai da ayarin jami'ansa."

Don haka, ta haɗa kayanta a jaka, ta hau jirgin ƙasa zuwa birnin Washington DC, kuma na tafi kai tsaye zuwa cikin cibiyar aikace-aikacen, cike da maza tsoffin sojoji. "Ina rayuwa ne cikin ruguntsumin gidan raye-raye," ta ƙyalƙyale da dariya. "Wannan wani babban tsallen baɗake ne."

Sammi ba ta san komai ba game da Afghanistan, amma tana da ƙwarewar da cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ta zama wadda ba za a iya damawa ba tare da ita ba.

"Na saba aiki da takardar tattara lissafi a kwamfuta da harkokin sadarwa. Don haka na zama jami'ar sadarwa. To, ya za a yi?"

Shauƙi ana tsaka da hargitsi

Duk da yanayin aikin gaggawa da hargitsin da ake ciki a cibiyar aikace-aikacen, wani abu kuma da ke faruwa.

"Akwai shaƙuwa? Ina jin amsar ita ce e," Sammi ta amsa. Ta tuna lokacin da ta duba shekarun Safi a shafin matambayi-ba-ya-ɓata don ganin ko "ya kai minzalin zuwa zance."

"Na duba sunan Safi a Google da shekarunsa saboda aiki ya sa ya rame a lokacin kuma duk tsufansa ya fito idan aka kwatanta da yanzu," ta ƙara cewa.

Doguwar tafiyarmu ta farko gaba ɗaya da ƙarfe 3 na dare, a lokacin during a tense night waiting for evacuees to clear Taliban checkpoints. They wandered through Washington's monuments until they reached the Lincoln Memorial.

"Sai na riƙa ji tamkar fim ne," in ji Sami. "Sai na fara tunanin shin zan iya aure da mutumin nan ne?"

Sai daga bisani suka samun damar haɗuwa har suka sumbaci juna, inda suka haɗu suna yi magana sosai a bakin titi cikin shauƙin junansu da ƙaruwar kusanci.

Safi ya ce, "Sai Sammi ta riƙa cewa ko zan kai ta wajen iyayena."

Sai dai shi Safi da danginsa duk Musulmai ne, ita kuma Sammi Bayahudiya ce. Amma duk da haka, sun ci gaba da soyayya.

"A taƙaice dai Safi ya yi nisa a soyayya," in ji Sammi. "Kuma sai ya kasance mai matuƙar sha'awar waƙoƙi musamman salon waƙar Les Mis, ɓangaren da na fi ƙwarewa."

Gidan yari

A watan Disamban 2021, Safi ya tafi Kabul domin gudanar da ayyukan jinƙai tare da ɗan'uwansa, duk da an hana shi zuwa, amma Safi ya dage sai ya je tare da cewa ƙungiyar Amnesty ta musu alƙawarin kariya daga illar Taliban.

Amma a ranar da ta kamata su gama aikin ne Taliban ta kama Safi da ɗan'uwansa da wasu ƴan ƙasashen waje guda biyar.

Da farko sai aka ware shi, shi kaɗai a waje ɗaya, "a wani ƙaramin ɗaki aka ajiye ni da bai wuce tsawo da faɗin ƙafa shida ba. Babu taga babu gado," in ji shi.

Ita kuma Sammi tana can New York tana fargaba, tana ta duba shi a taswirar Google domin sanin inda yake. Duk lokacin d ta duba sai ta ga yana hedkwatar hukumar leƙen asirin Taliban.

"Ban san birnin Kabul ba sosai, amma na san yana cikin wani hali mara kyau," in ji ta.

Bayan makonni, sai Safi ya nemi wani mai gadi ya zama abokinsa, inda ya riƙa ba mutumin kuɗi, yana ba shi dama yana waya da Sammi a ɓoye.

Daga ɗan ɗakin da yake tsare, sai ya riƙa hawa kafaɗar ɗanuwansa domin samun layin sadarwa da zai yi taɗi da Sammi, ko ya tura mata saƙon: "Kina lafiya? ina sonki."

"Sun samun damar yin waya ta farko ne bayan kwana 17," in ji Sammi. "Jin muryasa da tabbatar da cewa yana raye kaɗai babban abin murya ne. Sai dai kuma akwai fargabar abin da zai iya faruwa da shi idan aka gane muna waya."

"Kwana 70 ban ga hasken rana ba. Kullum muna can kurkukun ƙarƙashin ƙasa da ni da wasu ƴan ƙasashen waje bakwai, har wani ya fara tsananin rashin lafiya."

"Duk da cewa akwai tsananin tashin hankali, akwai ɗan sauƙi idan na tuna waƙar."

Amma duk da wahalar da yake ciki, sun ci gaba da gaisawa da Safi ta waya a ɓoye.

Ganin iyaye

An ɗauki lokaci ana tattaunawa da Taliban, amma a rana ta 70, sai suka amince su saki Safi. Sammi ta ce akwai lokacin da Taliban ta yi barazanar kashe Safi idan Amurka ba ta yi abin da take so ba.

"Daga baya sai aka ce da ni da iyayen Safi mu je Qatar domin a can ake ne tattaunawar."

Sai Sammi ta tafi Qatar, inda ta haɗu da iyayen Safi a can a karon farko.

"Ba su ma taɓa gani ko jin labarina ba, amma haka muka ci gaba da zama tare na kusan mako biyu."

"Kasacewar iyayen ba sa jin Ingilishi sosai, sai aka amince ni ne zan riƙa magana a madadin danginsa."

Da farko da suka gane cewa ɗansu musulmi yana soyayya da Bayahudiya sun yi, "amma wataƙila saboda yanayin da ake ciki, sai ba su ce komai ba. Na yi mamakin yadda suka amince da ni cikin sauƙi har muka saba muka zama ɗaya."

Bayan kwana 105 sai aka saki Safi, ya koma suka ci gaba da soyayyarsu da Sammi.

Ci gaba da rayuwa

Sun ci gaba da rayuwa a Amurka, inda suka tare a gida ɗaya, sannan daga bisani suka yi aure, inda ak cakuɗa al'adun Afghanistan da na Yahudawa wajen bikin.

Daga cikin baƙin da suka halarci bikin akwai ƴan Afganistan da Yahudawa da ƴanuwan da abokan arziki.

Darasi a soyayya

Sami ta yi amannar cewa matsalar da suka shiga ta taimaka wajen ƙara musu ɗankon soyaya. "Muna zaman lafiya fiye da yawancin ma'aurata da sani, saboda idan na tuna cewa na kusa rasa shi, sai ya zama duk abubuwan da suke faruwa a yanzu ba su cika damuna ba."

A wajen Safi, shi kuma kullum cikin godiyar Allah yake. "Duk abin da muke ciki a yanzu, ba zai kai abin da muka fuskanta a baya ba. Kasancewata a raye kaɗai ma abin farin ciki ne."