Yadda za ku iya samun kuɗi ta hanyar WhatsApp

Lokacin karatu: Minti 2

Kamfanin Meta da ya mallaki manhajojin WhatsApp da Facebook da Instagram sun sanar da cewa za su fara yin tallace-tallace a kan shafin WhatsApp.

Wannan dama ce ga ajin masu hulɗa da dandalin guda uku da suka haɗa da masu yin bidiyo da masu sha'awar kasuwanci da ƴan kasuwa domin samun kuɗi daga WhatsApp ɗin.

Kamfanin Meta, a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin cewa mutanen guda uku a yanzu haka za su iya samun kuɗi daga kafar.

Ajin farko zai mu'amila da mutanen da za su rinƙa biyan kuɗi domin kallon bidiyo a kan WhatsApp da ake kira "biyan kuɗi domin kallon tasha".

Kashi na biyu kuma shi ne wanda Meta ya bayyana da tashoshin yin tallace-tallace da suka bayyana da "tashoshin talla".

Kaso na uku shi ne na tallata haja a kan dandamalin WhatsApp da ake kira "Status" ga masu amfani da manhajar ta WhatsApp.

Dukkannin waɗannan hanyoyi ne da WhatsApp zai yi amfani da su wajen bai wa jama'a damar tallata hajarsu ta hanyar da ba za ta shafi fannin aikewa da saƙon rubutu ba a kafar.

"Mun daɗe muna tunanin fito da hanyoyin da masu hulɗa da WhatsApp za samu kuɗi a manahajar ba tare da hakan ya shafi ingancin saƙonnin rubutu ba a manhajar.

"Mun yi imanin cewa lokaci ne na fara shirin da kuma sanar da shi.," in ji Meta.

A ƙarƙashin ajin ''Tashar Yaɗa saƙonni'' Meta zai bai wa masu hulɗa ta WhatApp damar kallon abubuwan da suke sha'awar kallo ta hanyar biyan kuɗi a duk wata.

Harwayau, Meta zai bai wa abokan hulɗar tasa damar sauraron duk nau'in labaran da suke so ciki har da na wasanni.

A ƙarƙashin tashar tallace-talalce kuma, kamfanin na WhatsApp zai ba da dama ga mutane su tallata hajarsu ta hanyoyi da dama a farashi daban-daban.

Hakan zai bai wa mutanen da dama zarafin ganin irin hajar da wasu ke tallatawa.

Tallata hajar a kan dandamalin "Status" zai bai wa mutane damar yin tallan kamar dai yadda suka saba yi a Instagram.

Haka kuma Meta zai bai wa abokan hulɗarsa damar sanin hajoji.

Kamfanin na Meta ya kuma ƙara da cewa mutanen da ke amfani da WhatsApp za su amfana daga tattaunawa da waɗanda ke son tallata hajarsu.

Meta ya kuma ce akwai tsarin da zai samar da tsaro ga masu amfani da WhatsApp ta yadda ba bu buƙatar nuna damuwa da wani ko wata da za su saci bayananku.

"Za mu buƙaci bayananku kamar sunan gari ko ƙasa ko harshe idan muna son nuna tallan hajojin naku a dandamalin "Status" da ke WhatsApp.

"Sai dai kuma ba za mu bayar da lambobin wayoyinku ba ga mutanen da kuke son yi wa tallan," in ji Meta.