Dalilai takwas da suka sa Tinubu ya ci zaɓen Najeriya

Jagaban

Asalin hoton, @ASIWAJUTINUBU

    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja
    • Aiko rahoto daga, Abuja

A Najeriya hukumar zaɓen ƙasar ta sanar da Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki a matsayin sabon zaɓaɓɓen shugaban Najeriya, bayan fafatawa mai zafi tsakanin manyan 'yan takara huɗu a jumullar su 18.

Da asubahin wayewar garin Laraba ne shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar da tsohon gwamnan na Jihar Legas, a matsayin wanda ya ci zaɓen da ƙuri'a miliyan 8,794,72.

Bola Tinubu fitaccen ɗan siyasa ne a Najeriya wanda ya shahara a fagen siyasa da mulki a ƙasar.

Ya daɗe yana shirya wa kansa dabaru domin zama shugaban Najeriya musamman wajen gina 'yan siyasa da dama a faɗin ƙasar.

To sai dai akwai wasu dalilai da dama da masana ke ganin su ne suka janyo wa ɗan takartar nasara a zaɓen na bana.

Farfesa Tukur Abdulƙadir na Jami'ar Jihar Kaduna na ganin daga cikin dalilan akwai;

Haɗin kan gwamnonin Arewa

Jagaban

Asalin hoton, Twitter/Ahmad Lawan

Gwamnonin Arewa sun taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar Tinubu, tun daga matakin zaɓen fitar da gwani har zuwa matakin babban zaɓe.

Dakta Kole Shettima na Gidauniyar MacAthur ya ce goyon bayan da ɗan takarar ya samu musammn daga gwamnonin Arewa ya taimaka masa matuƙa wajen samun nasara.

A baya-bayan nan dai an ga yadda wasu gwamnoni daga jihohin Arewa suka nuna adawa ga duk wani mataki dai zai kawo nakasu ko cikas ga zaɓen ɗan takarar.

Dakta Kole ya ce duk da cewa Bola Tinubu bai samu nasarar cinye duka jihohin gwamnonin ba, amma ya samu ƙuri'u masu yawan gaske domin kuwa bambancinsa da ɗan takarar da ya ci wasu daga cikin jihohin bai taka kara ya karya ba.

Rarrabuwar kan 'yan hamayya

Jagaban

Asalin hoton, FACEBOOK/ BOLA AHMED TINUBU

Wani abu da za a iya cewa ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar ɗan takarar shi ne samun rarrabuwar kai daga ɓangaren 'yan hamayya.

Dakta Kole Shettima ya ce ''idan aka duba adadin ƙuri'un da 'yan hamayya suka samu ya kai miliyan 13 da ɗoriya, ya yin da shi kuma Tinubu ya samu ƙuri'a miliyan takwas da ɗoriya.''

''Idan ka duba duka 'yan adawa sun fito ne daga babbar jam'iyyar adawa ta PDP, to da a ce sun dunƙule waje guda sun shiga zaɓen dole za su kayar da shi'', in ji Dakta Kole.

Idan za a iya tunawa dai Peter shi ya yi wa Atiku takarar mataimaki a zaɓen 2019, sai kuma Kwankwaso wanda shi ma a shekarar 2022 ne ya fice daga jam'iyyar PDP tare da shiga jam'iyyar NNPP.

Fitowa takara ƙarƙashin jam'iyya mai mulki

Jagaban

Asalin hoton, Twitter/Bola Tinubu

Bola Ahmed Tinubu ya fito takara ne ƙarƙahin jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar.

Farfesa Tukur Abdulƙadir na ganin hakan ya taimaka musamman wajen samun karɓuwa tare da tallata shi daga gwamnonin APC mai mulki.

Kuma shugaban ƙasar da kansa ya sha halartar tarukan yaƙin neman zaɓensa tare da kiran a zaɓe shi, wanda hakan ba ƙaramin tasiri ba ne ga nasarar ɗan takarar.

Gogewarsa a fagen siyasar ƙasar

Bola Tinubu ya daɗe yana jan zarensa a fagen siyasar ƙasar, wanda haƙiƙa hakan ya taimaka masa matuƙa wajen samun nasarasa a wannan zaɓe.

Dakta Kole ya ce tun lokacin Abiola Tinubu yake siyasa ''domin kuwa ya yi sanata sannan ya yi gwamna har sau biyu, ya kuma yi amfani da damarsa a lokacin da yake gwamna ya gina 'yan siyasa.''

''Haka kuma bayan saukarsa daga gwamna ya yi ta gina kyakkyawar alaƙa da 'yan siyasa musamman daga sassan arewacin ƙasar waɗanda kuma su ne suka taimaka masa a yanzu wajen samun nasararsa'', in ji Dakta Kole.

Adawa da batun sauyin kuɗi

A ƙarshen shekarar da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta ɓullo da batun sauyin fasalin wasu takardun kuɗin ƙasar, inda a farkon shekarar da muke ciki aka fara aiwatar da shi.

Lamarin ya yi matuƙar tayar da hankalin 'yan ƙasar tare da sanya su cikin matsin tattalin arziki.

Amma kasancewarsa ɗan takarar jam'iyya mai nulki, bai hana shi fitowa ƙarara ya nuna adawa da matakin ba, a yayin da a gefe guda ɗan takarar PDP ya nuna goyon bayansa ga matakin, in ji Farfesa Tukur Abdulƙadir.

Daukar mataimaki Musulmi

Jagaban

Asalin hoton, Twitter/Bola Tinubu

Kasancewar Bola Tinubu ya fito daga yankin kudancin ƙasar, yana buƙatar ɗaukar mataimaki daga arewacin ƙasar matuƙar yana son samun ƙuri'un 'yan arewacin ƙasar.

Kuma kasancewar Musulmai su ne suka fi yawa a yankin arewacin ƙasar, idan Tinubu bai ɗauki Musulmi daga Arewa ba, to zai yi wahala 'yan Arewa su zaɓe shi'', in ji Farfesa Tukur Abdulƙadir.

Ya ƙara da cewa kasancewar Najeriya ƙasa ce mai martaba ɓangaranci, Bola Tinubu ya yi nazari sosai wajen ɗaukar mataimaki, domin kuwa da bai ɗauki ɗan takara Muslumi ba, da zai yi wuya 'yan arewacin ƙasar su zabe shi.

Samun goyon bayan Yarabawa.

Jagaban

Asalin hoton, Twitter/Bola Tinubu

Dakta Kole Shettima ya ce ɗan takarar ya samu goyon bayan al'ummar Yarabawa kasancewar ya fito daga yankinsu.

''Haƙiƙa jihohin Yarabawa sun ba shi goyon baya, musamman a yankin kudu maso yammacin ƙasar, domin kuwa duk da cewa bai ci jihohin Legas da Osun ba, amma babu wata gagarumar tazara tsakaninsa da 'yan takarar da suka ci jihohin biyu'' in ji Dakta Kole.

Alaƙar Yarabawa da Hausawa

Alaƙa tsakanin 'yan Arewa da Yarabawa ta taimaka wajen samun nasarar Bola Tinubu.

A cewar Farfesa Tukur daɗaɗdiyar alaƙar kasuwanci da addini tsakanin Yarabawa da Hausawa ta taimaka wajen samun karɓuwar ɗan takarar a yankin arewacin ƙasar.

Ya kuma ce tarihi ya nuna cewa al'umomin biyu sukan haɗa kai a ɓangaren siyasar ƙasar musamman wajen kafa gwamnati.