Ƴan wasan Afirka shida da ake ganin za su yi bajinta a gasar Olympics

Blessing Oborududu da Faith Kipyegon da kuma Biniam Girmay celebrate victories in their respective disciplines

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Faith Kipyegon ta Kenya (tsakiya) ta riga ta samu lambobin yabo na zinare biyu na Olympics, yayin da Blessing Oborududu (hagu) da Biniam Girmay (dama) na da burin lashe lambobin yabo karo na farko a birnin Paris
    • Marubuci, Rob Stevens
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Africa na da burin karya tarihi ta hanyar lashe lambobin yabo 50 karo na farko a gasar Olympics ta Paris na shekarar 2024.

A cikin wasanni 32 da za a yi karawa 329, nahiyar na da dama da yawa wajen lashe waɗannan lambobin yabo daga gasar a Paris babbar birnin Faransa.

Yayin da wasu ƴan wasa suka samu nasara a sauran gasar da aka yi na Olympics, wasu kuma na shirin kafa sabon tarihi ga ƙasarsu ko ga wasannin motsa jiki.

Saboda haka ne sashen wasanni na BBC Africa ya nazarci wasu ƴanwasan nahiyar Afrika shida da ake ganin za su yi bajinta a gasar.

Faith Kipyegon daga Kenya

Faith Kipyegon, ƴar ƙasar Kenya mai shekara 30, ta taɓa lashe lambobin yabo biyu na zinare, sannan ta kafa tarihi har sau huɗu a duniya cikin wata 13 da suka gabata, yanzu kuma ta nufi birnin Paris domin karawa a gasar.

Tana da burin lashe lambar yabo ta zinare karo na uku a gasar Olympics wasan tseren mita 1,500 na mata, wanda babu wani dan wasan Afirka da ya taɓa samun lambar yabo har sau uku a jere a gasar.

A farkon wannan watan, Kipyegon ta rage tarihin da ta kafa a tseren mita 1,500 a gasar Diamond League da aka yi a birnin Paris. Haka kuma za ta shiga gasar gudun mita 5,000 a wasannin gasar wannan shekarar.

Bayan lashe lambobin yabo biyu a gasar kofin duniya na bara, Kipyegon na da burin maimaita nasarar da ta samu a gasar Olympics, tare da tabbatar da matsayinta na sarauniyar wasan.

Letsile Tebogo ɗan Botswana

Letsile Tebogo riƙe da tutar Botswana yayin ya yake murnar lashe lambar yabo ta azurfa a gasar tsere ta duniya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A shekarar da ta gabata, Letsile Tebogo ne ɗan Afrika na farko da ya lashe tseren mita 100 a gasar tsere ta duniya

Letsile Tebogo, shi ne mutum na farko daga Botswana da ya kafa tarihin tsallake shinge a daƙiƙa 10 a tseren mita100.

Tebogo ya bayyana kansa a babban mataki a bara lokacin da ya karbi lambobin yabo biyu a gasar tsere ta duniya.

Ya lashe lambar yabo ta azurfa a tseren mita 100 da lambar yabon tagulla a tseren mita 200.

Ya rasa mahaifiyarsa a lokacin da yake da shekara 21.

Tebogo zai iya zama mutum na farko a Afirka da zai lashe lambar yabo a tseren mita 100 ko mita 200 a gasar Olympics tun bayan Frankie Fredericks da ya lashe a sheakarar 1996.

Biniam Girmay ɗan Eritrea

Biniam Girmay tare da magoya bayansa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Girmay ya kasance yana samun girmamawa daga 'yan Eritriya kuma magoya bayan kasarsa suna yawan zuwa domin nuna masa goyon baya a tserensa a Turai

Shi ne baƙin fata na farko da ya kafa tarihi yayin da ya lashe mataki na farko a tseren keke a gasar Tour de France.

Girmay ya kasance tauraron ƙasar Eritrea.

Dan wasan mai shekara 24 yana da burin lashe lambar yabo a gasar Olympics.

Shin matashin mai shekara 24 zai iya zama cikin mutum biyu da suka fi zarra a gasar tseren keke sannan ya kasance mafi wannan bajinta a yankin Gabashin Afrika a gasar Olympics domin ɗorawa a kan kyautar tagullar da ya samu a 2004?

Tseren kilomita 273 zai kasance mafi ƙalubale ga ɗanwasan.

Blessing Oborududu daga Najeriya

Blessing Oborududu, 'yar wasan kokawa ce ta Najeriya da ke da lambobin yabo na Afrika 14 da lambar yabo ta Commonwealth guda hudu, ta samu lambar azurfa a gasar kilo 68 a Tokyo 2020 wanda ta nuna bajinta.

Yanzu tana da shekaru 35, za ta kara a gasar Olympics wanda take da burin lashe lambar yabo da kuma samun nasara a fagen wasanta.

Tana matsayi na shida yayin da Koumba Larroque ta Faransa ke gabanta.

Hugues Fabrice Zango daga Burkina Faso

Hughes Fabrice Zango riƙe da lambar yabo na zinare da ya lashe

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A bara Hugues Fabrice ya lashe zinare a wasan da aka yi a Budapest da tsallen mita 17.64 a Budapest

Ɗanwasan mai shekara 31 na Burkina Faso, shi ne na farko da ya ci wa ƙasar lambar yabo ta tagulla a wasan tsalle uku ɓangaren maza a birnin Tokyo na Japan shekara uku da suka wuce.

Zango ya sake wuce wannan bajintar inda ya zama gwarzo a shekarar da ta gabata da tsallen mita 17.64 a Budapest.

'Yankallo sun yi masa maraba lokacin da ya sauka gida Ouagadougou, kuma ya zama ɗanwasa na farko da ya samu babbar lambo yabo mafi daraja ta ƙasar - Officer of the Order of the Stallion.

Ƙwararre mai digirin digirgir a fannin latironi, Zango na son ya zama wani madubi ga sauran 'yanwasan ƙasarsa.

Abin da ya sa a gaba shi ne cigaba da kafa tarihi a madadin ƙasarsa Burkina Faso.

Fatima Zahra El Mamouny ('yar Morocco)

Fatima Zahra El Mamouny ta zama 'yarwasan karya jiki ta farko daga Afirka da zama gwarzuwa a watan Mayun 2023

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fatima Zahra El Mamouny ta zama 'yarwasan rawar karya jiki ta farko daga Afirka da zama gwarzuwa a watan Mayun 2023

Wadda aka fi sani da B-girl El Mamouny, 'yar Moroccon ta kafa tarihin zama 'yarwasan da ta fara samun gurbi a wasan rawar karya jiki na gasar Olympics.

Kwamatin shirya gasar sun ƙaddamar da shi ne a 2024 saboda jawo hankalin matasa.

Mai shekara 24 ɗin ta yi suna ne a titunan birnin Rabat, duk da cewa da farko iyayenta ba su goyon bayanta.

Masu rawar za su fafata ne cikin karawar mutum biyu-biyu, inda za su dinga nuna ƙwarewarsu kuma a ba su maki.