'Na yi asarar komai' - Yadda gobara ta jefa mutane cikin ƙunci a Amurka

Hipolito Cisneros ya na duba ɓaraguzan gidansa da gobara ta laƙume a California
Bayanan hoto, Hipolito Cisneros ya na duba ɓaraguzan gidansa da gobara ta laƙume a California
    • Marubuci, Max Matza & Christal Hayes
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, Altadena, California
  • Lokacin karatu: Minti 6

Ƙwararren mai dafa abinci, Daron Anderson ya saba shaida wa mutane cewa an haife shi ne a ɗakin girki.

Mutumin mai shekara 45, an haife shi ne a gida mai lamba 295 a unguwar West Las Flores, inda ya ci gaba da zama tare da mahaifiyarsa har zuwa makon nan.

A ranar Alhamis ya shiga domin gane wa kansa ɓarnar da gobara ta yi a yankin Altadena da ke arewa maso gabashin Los Angeles, wajen da ɗakin girkinsa yake.

Ya je wajen ne da fatan ko zai iya ganin abin da ya yi saura daga kayan dafa abincin da yake amfani da su, bayan ɓarnar da gobara ta yi a yankin, wadda rahotanni suka ce ita ce mafi muni a tarihin yankin.

Gobarar ta kashe aƙalla mutane 16 ta kuma tarwatsa unguwanni da dama, tare da korar dubban mutane daga muhallin su.

A tsallaken titi kuwa, a gida mai lamba 296 da ke kallon gidan Daron, gidan ƙawarsa ce Rachel, wanda ya ƙone ƙurmus, haka shi ma gidan da ke gaba mai lamba 281, inda suka saba zuwa domin biki tare da iyalan su, ya ƙone.

Budurwarsa da ke zaune a rukunin gidajen da ke kusa da na Daron ma ta yi asarar gida da duk kayayyakinta. A can ma mutane ne ke dubawa ko za su yi nasarar samun sauran wasu abubuwan amfani a cikin kayayyakin nasu da gobarar ta cinye.

Gobarar ta afka yankin ne ranar Talata a cikin dare.

Daron sanye da baƙar riga yana zagaye a wajen da gobara ta yi ɓarna.
Bayanan hoto, Daron sanye da baƙar riga yana zagaye a wajen da gobara ta yi ɓarna.

Gobarar da guguwa mai ƙarfi ta ruruta, ta yi ɓarna sosai.

Daron na tsaye a gaban gidansa da misalin ƙarfe 6 na yamma, inda ya ke ƙoƙarin ɗauke sauran kayyakinsa don kada guguwa ta kwashe su.

A tsallake kuma a gida mai lamba 296 na unguwar West Las Flores, Rachel Gillespie tana ci gaba da cire kwalliyar da ta yi domin bikin kirsimati, ita ma don gudun kada ta yi asarar kwalliyar.

Suka kalli juna cikin damuwa sannan ta ce ''da alama abin zai yi muni fa''

Taswirar gidan Daron da gobara ta lashe
Bayanan hoto, Taswirar gidan Daron da gobara ta lashe

A lokacin damuwar su ba ta wuce ta ɓarnar da guguwa za ta iya yi ba.

Ba su san cewa abin da zai biyo baya zai zamo ɓarna mafi muni da gobarar daji ta yi wa jihar Los Angeles a tarihi ba, lamarin da kuma ya zamo barazana ga birni na biyu mafi girma a Amurka.

Gobarar da ta lashe yankuna a Altadena, ta ƙone dubban gidaje da masana'antu, da kuma mutane aƙalla 16. Ya zuwa ranar Asabar kashi 15 kawai cikin ɗari na gobarar aka kashe.

A yammacin Los Angeles, wutar ta ƙone mafi yawan unguwanni da kuma kashe aƙalla mutane biyar.

Bayanan bidiyo, Ma'aikatan kashe gobara na tserewa a lokacin da wuta ke neman kama su.

Maƙwabcin Daron da ke zaune a gida mai lamba 281, Dillon Akers, yana wajen aiki a wani babban shagon sayar da kaya a lokacin da hayaƙi ya fara tashi a gidansa.

Dillon mai shekara 20 ya garzaya gida bayan samun labarin abin da ke faruwa, amma ko da ya isa sai ya samu ƴan‘uwansa na ficewa daga gidan.

Shi da kawunsa sun riƙa kwashe sauran kayansu da suka haɗa da abinci da magunguna da kuma kayan sawa.

Ana cikin haka sai Dillon ya gane cewa ya ɓatar da makullansa, inda ya ci gaba da lalube yana haskawa da fitila, har daga bisani ya gano shi.

Hoton Dillon da taswirar gidansa
Bayanan hoto, Hoton Dillon da taswirar gidansa

Ko a lokacin da yake neman makullin nasa, Dillon yana da yaƙinin cewa hukumar kashe gobara za ta yi nasarar shawo kan gobarar da ta tunkari gidan da yake zaune tare da mahaifiyarsa da kakarsa da kuma ƙannensa biyu.

Dillon ya shaida faruwar gobara a baya, amma a wannan karon ya ga yanayi na daban.

"Na tsorata matuƙa," in ji Dillon.

A ranar Laraba, Dillon ya ce shi da mahaifiyarsa ne mutane na ƙarshe da suka bar unguwar West Las Flores. Kuma ƙila su ne na ƙarshe da suka fita wajen da rai.

Bayan kwana ɗaya kuma hukumomi sun sanar da cewa sun gano wata gawa a wajen.

.
Bayanan hoto, Taswira da kuma hoton gidan Rachel wanda gobara ta kone kurmus

Rachel da Daron sun fice daga unguwar aƙalla sa'oi biyu kafin Dillon ya fita. Wani mutum ne ya tilasta wa Rachel barin wajen.

Rachel ta yi nasarar ficewa tare da kyanwoyinta biyar da wasu kayan sawa.

Daron ma ya kwashi abubuwan da zai iya ɗauka da suka haɗa da jitar kiɗan da ya saya yana ɗan shekara 14, da kuma hoton ƴan gidan su suna tsallaka titi a birnin London.

Hoton BBC mai nuni da yadda gobarar ta yi ɓarna
Bayanan hoto, Hoton BBC mai nuni da yadda gobarar ta yi ɓarna

Ƙananan yankuna da unguwanni irin su Altadena ne suka fi yawa a Los Angeles.

Kowacce safiya mutane na ziyarar kantin shan shayi na The Little Red Hen Coffee Shop kafin tafiya wajen aiki.

Mazauna yankin da dama sun bayyana irin yadda al'ummar yankin ke tashi cikin ƙaunar juna da kuma kula da juna, ta yadda ƙananan yara ke girma su ci gaba da rayuwar su a kan tituna.

Amma a yanzu da yake shiga yankin a karon farko bayan ɓarnar da gobarar ta yi, Daron ya kasa gane wasu wuraren da a baya ya saba zuwa.

Taswirar yankin da gobarar Eaton ta yi ɓarna a Altadena
Bayanan hoto, Taswirar yankin da gobarar Eaton ta yi ɓarna a Altadena

Babban gidan da ya bayar ya zamo matattarar iyalai da dama ya ƙone ƙurmus. Duk wasu abubuwan tarihi da ya saba da su sun kau. Ya riƙa nuna kayan da maƙwabta suka yi asara.

Ya ɗauki hotunan gidansa da na Rachel da kuma titin da suke bi tare da Dillon.

A ƙofar gidan budurwarsa kuma, Daron ya naɗi bidiyo da ya tura wa ƴan‘uwa, kana daga baya ya kira budurwar tasa a waya yana sanar da ita halin da ake ciki.

Cikin rawar murya ya ce mata ''Mun rasa komai da muke da shi a nan''

Daron ya tsinko lemo don ya sake shukawa
Bayanan hoto, Daron ya tsinko ‘yayan lemo da yake son ta sake shukawa

Akwai wasu ƴan tsirarun abubuwa da gobarar ba ta cinye ba.

A gidan ƴar‘uwarsa a West Las Flores Drive, ya samu wasu kayayyakin buƙata da wutar ba ta lalata ba.

Ya kwashe wasu daga cikin furannin da ta yi kwalliyar kirsimati da su kafin annobar, saboda tunanin ko babu komai za su faranta mata rai idan ya kai mata su.

A ƙofar gidansa ma akwai tukunyar ƙasa da aka shuka furanni a ciki, wadda ita ma babu abin da ya same ta.

Akwai kuma wata bishiyar lemu wadda ba ta ƙone ba, kuma akwai lemu da yawa a jikinta.

"Idan na samu dama zan ƙara shuka bishiyar nan," Daron ya ce, yayin da yake taɓa lemun.

Ya ƙara da cewa "Wannan wata hanya ce ta buɗe sabon babin rayuwa."