Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ya kamata a bar ƴan Najeriya su ɗanɗana kuɗarsu - Buba Galadima
A ranar 29 ga watan Mayun 2024 ne Najeriya za ta, cika shekara 25 da komawa kan turbar dimokuraɗiyya ba tare da katsewa ba, wadda kuma ake kira Jamhuriya ta Huɗu.
An shiga jamhuriya ta huɗu ne tun daga lokacin da aka rantsar da tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo a matsayin shugaban ƙasa ranar 29 ga watan Mayun 1999, abin da ya sa har yanzu ba a kuma samun juyin mulki ko wata tangarɗa ba a tsarin dimokuraɗiyyar ƙasar.
Albarkacin wannan rana ne kuma BBC ta fara bin diddigin cigaba ko koma-bayan mulkin na dimokuraɗiyya a ƙasar da ke yammacin Afirka, ta hanyar tattaunawa da shugabannin al'umma, da 'yan siyasa.
Ɗaya daga cikin irin waɗannan 'yan siyasa shi ne Buba Galadima, dattijo mai shekara kusan 75 wanda ya fara gwagwarmayar siyasa tun daga shekarar 1978.
Jigo ne a jam'iyyar adawa ta NNPP, wadda tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wa takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2023.
Kamar yadda aka saba a matsayinsa na ɗan'adawa, Buba Galadima ya caccaki gwamnatin APC ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu, wadda aka rantsar ranar 29 ga watan Mayun 2023 bayan samun nasara a zaɓen watan Fabrairu.
Buba Galadima ya ce tun kafin lokacin babban zaɓen Najeriya na 2023, a matsayinsu na ƴan adawa sun gargaɗi ƴan Najeriya kan zaɓen shugaban da ke ci a yanzu, sai dai al'umma ba su saurare su ba.
Da alama dai Buba Galadima na bayani ne a kan halin da ƙasar ta Najeriya ke ciki a yanzu, inda al'umma ke fama da tsadar rayuwa sanadiyyar matsalar tattalin arziƙi.
Rayuwa ta yi tsada a ƙasar ta Najeriya tun bayan da shugaba Tinubu ya ayyana cire tallafin man fetur, kayan masarufi sun yi tashin gwauron zabi.
Haka nan darajar naira ta ci gaba da faɗuwa idan aka kwatanta da dalar Amurka. Sai dai gwamnatin Tinubu na cewa tana yin hakan ne domin gyara tattalin arziƙi ta yadda zai amfani al'umma a gaba.
Amma Buba Galadima ya ce "a bari su (ƴan Najeriya) ɗanɗana, su ji a jikinsu".
A cewarsa hakan zai zamo darasi ga al'ummar Najeriya a lokacin zaɓe mai zuwa.
Ya ce za a iya gyara halin da Najeriya ke ciki ne kawai idan mutane sun cire kwaɗayi tare da yin abubuwan da suka kamata.
Matasa sun ba mu kunya a siyasar Najeriya
Duk lokacin da aka yi maganar neman sauyi a salon mulkin Najeriya abin da yake fara zuwa ran akasarin mutane shi ne; an ƙi a bai wa matasa dama.
Akasarin masu yin wannan magana na nufin bai wa matashi damar zama gwamna ko shugaban ƙasa, ba ɗan majalisa ko minista ba, waɗanda za a iya an fara samun sauyi a wannan fanni.
Tun daga 1999 zuwa yanzu, babu wani ɗan shekara 30 ko 40 da ya zama gwamna ko shugaban ƙasa a ƙasar da mafi yawan jama'arta matasa ne 'yan ƙasa da shekara 40 - kodayake kundin tsarin mulkin Najeriya ne bai ba su dama ba.
Wannan ta sa wata gamayyar ƙungiyyoyin matasa suka ɗauki gabarar sauya tsarin mulkin, inda suka yi nasarar shawo kan 'yan majalisa amincewa da ƙudirin Not Too Young To Run, wanda tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu a 2018.
"Mun ba su [dama] amma sun ba mu kunya," in ji Buba Galadima - daɗaɗɗen ɗansiyasa da ya shafe shekaru kusan 50 a fagen siyasa a Najeriya - yayin wata hira da BBC.
'Da na gaba ake gane zurfin ruwa'
Da aka tambaye shi game da rashin bai wa matasa dama a siyasar Najeriya, sai ya ba da amsa da tambaya shi me: "Ai daga na gaba akan gane zurfin ruwa, ta yaya za ka ɗauki [mulkin] Najeriya ka bai wa wanda ya kasa riƙe ƙaramar hukuma ko jiha?"
Buba Galadima ya fara gwagwarmyara siyasa tun yana ɗan shekara 27 da haihuwa, kuma da shi aka jam'iyyu masu yawa tare da riƙe muƙamai na cikin jam'iyyun iri-iri.
Sai dai bai taɓa hawa wata kujerar mulki ba ta hanyar cin zaɓe.
"Da a ce wanda muka gwada da shi ya kamanta, ya yi adalci, ya yi aiki, ya yi dimokuraɗiyya, to da sai hankalinmu ya kwanta. Waɗanda muka bai wa ba su tsaya sun ji maganar na gaba da su ba ballantana a ce," a cewarsa.
Daga ji an san cewa Buba na magana ne a kan wani matashi da ya taɓa riƙe babbar kujerar mulki a Najeriya, sai dai bai ambaci suna ba.
Sai dai kuma da aka tambaye shi kan abin da ya fi ba shi takaici game da siyasar Najeriya, ya ce "ƙuri'ar talaka".
"Wallahi rashin dama ta ƙuri'ar talaka ta tabbata shi ne babban abin da yake ba ni takaici. Abin da nake so na gani a Najeriya kafin na mutu shi ne ƙuri'ar talaka ƙwaya ɗin nan ya jefa ta tabbata cewa an ƙirga ta."
Daga cikin muƙaman da Buba Galadima ya riƙe a fagen siyasar Najeriya sun haɗa da zama sakataren tsohuwar jam'iyyar CPC na ƙasa, wadda ɗaya ce daga cikin manyan jam'iyyun da dunƙule suka kafa APC a 2013.
Haka nan, da shi aka kafa jam'iyyar NPN a 1978; tsohon sakataren kuɗi na jam'iyyar NRC; mamba a kwamatin amintattu na jam'iyyar APC; mataimakin shugaban yaƙin neman zaɓe na ƙungiyar Buhari Campaign Organization.