Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Najeriya ta amince da yi wa 'yan ƙasar riga-kafin maleriya
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta amince a fara yi wa 'yan ƙasar allurar riga-kafin zazzaɓin cizon sauro mai suna R21.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce an sanar da ministan lafiya da hukumar bunƙasa lafiya a matakin farko game da wannan mataki na amincewa da riga-kafin don ɗaukar matakan da suka dace na yin allurar ga jama'a
NAFDAC ta kuma buƙaci faɗaɗa gwaje-gwajen da ake yi ta yadda matakan za su ƙunshi nazarin illar da allurar ka iya yi a Najeriya.
Ta ce za a yi amfani da riga-kafin ne wajen hana kamuwa da zazzaɓin maleriya ga ƙananan yara 'yan wata biyar zuwa 'yan shekara uku da haihuwa.
Sanarwar ta NAFDAC ta ce ana samun zazzaɓin cizon sauro a duk faɗin Najeriya, kuma kashi 97% na al'ummar ƙasar ne ke cikin hatsarin kamuwa da maleriya.
A cewar rahoton zazzaɓin cizon sauro na duniya na 2021, Najeriya ce ta fi yawan masu kamuwa da cutar maleriya. Kashi 27% na masu kamuwa da zazzaɓin cizon sauro a duniya, ana samun su ne a Najeriya.
Kuma ƙasar ce ta fi yawan mutanen da suka mutu sanadin zazzaɓin maleriya a 2020.
Haka zalika, Najeriya ce take da ƙiyasin kashi 55.2% na mutanen da suka kamu da cutar zazzaɓin cizon sauro a Afirka ta Yamma cikin shekara ta 2020.