Taƙaddama tsakanin CAN da limaman Kirista kan halartar taron APC

Bishop-bishop

Asalin hoton, Other

Bayanan hoto, Mutum fiye da 30 ne da suka kira kansu bishop-bishop suka halarci taron na APC a Abuja ranar Laraba

Wasu limaman addinin Kirista da ƙungiyar Kiristoci ta CAN ta zarga da cewa "na haya ne" sun ce ba don kuɗi suka je bikin ƙaddamar da abokin takarar Bola Ahmed Tinubu ba na jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Bishop-bishop fiye da 30 ne suka halarci bikin wanda aka yi ranar Laraba a Abuja, inda ɗan takarar ya kafa hujja da su cewa yana tafiya da mabiya addinai daban-daban.

Bishop Edward Williams ɗaya ne daga cikinsu, kuma ya faɗa wa BBC Hausa cewa lallai su mutanen Allah ne kuma gayyata suka amsa.

"Mun ji maganganu da yawa cewa wai hayarmu aka yi da kuɗi. Ni babu wanda zai ɗauki hayata, maganganun nan ba gaskiya ba ne," a cewarsa.

Tun a Larabar ce ƙungiyar CAN ta ce "wasu daga cikin limaman ba ma Kirista ba ne" tare da bayyana su da cewa na haya ne.

Wasunsu ma 'yan-tasha ne - CAN

Cikin zarge-zargen da ƙungiyar Kiristoci ta CAN ta yi ta ce wasu daga cikin mutanen da suka halarci taron 'yan-tasha ne, "waɗanda da ganin tufafinsu za a gane ba bishop ba ne".

Rabaran Joseph Hayap, shi ne mataimakin shugaban ƙungiyar Kiristoci ta CAN na jihohin arewacin Najeriya da birnin Abuja, ya ce yaudara ce irin ta siyasa don neman goyon baya.

"An ɗauki mutanen da ba su dace ba, wasunsu 'yan-tasha ne, wasunsu Kirista ne, wasu ma ba Kirista ba ne, sun sayi kaya kawai sun saka" in ji shi.

"Mu da muke Kirista muna ganin bishop za mu gane. To wannan ne ya kawo mana damuwa cewa wai shin siyasar har ta yi zafi da za a yaudari mutane don a nemi goyon baya?"

CAN ta sha nanatawa cewa matakin Bola Tinubu na ɗaukar Sanata Kashim Shettima, tsohon Gwamnan Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya wanda kuma Musulmi ne, ba dace ba.

Ƙungiyar ta yi imanin cewa APC mai mulkin Najeriya ta yi watsi da muradan al'ummar Kirista saboda ƙin ɗaukar mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa mabiyin addinin, kamar yadda aka saba a siyasar Najeriya.

Sai dai APC ta sha musanta zargin tana mai cewa ta yi hakan ne kawai don samun ƙuri'a mai yawa a babban zaɓen 2023 mai zuwa.

Ya rage nasu - Bishop Edward Williams

Yayin taron, Sanata Kashin Shettima ya yaba wa Bishop-bishop ɗin kan zuwansu wurin taron.

Shi ma ɗan takarar APC Bola Tinubu ya kafa hujja da halartar malaman cewa ta nuna yana tafiya da mabiya addinai daban-daban.

A martanin da ya mayar yayin hira da BBC Hausa, Bishop Edward Williams, ya ce duk wanda bai yarda cewa su bishop ne na gaskiya ba "ya rage nasu".

"In sun ce mu ba fasto-fasto ne na ƙwarai ba ya rage nasu. Ba su suka kira mu ba, Allah ne ke kiran mutum ya yi aikinsa.

"Bai dace mutum ya buɗe baki ya dinga faɗar abubuwa haka ba. An gayyace mu ne zuwa ƙaddamar da Shettima kuma idan aka gayyace ka abu in ka ga dama ka je, in ka ga dama ka bari.

"Mun je mun ga yadda abin ya gudana. Duk wanda ya ce Allah bai kira mu ba to shi da Allah ya yi kira sai ya ci gaba."

Yadda Tinubu ya zaɓi Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa

Kashim Shettima da Bola Tinubu

Asalin hoton, APC

Bayanan hoto, An ƙaddamar da Kashim Shettima a hukumance ranar Laraba a matsayin abokin takarar Tinubu

Tinubun ya bayyana haka ne ga ƴan jarida a garin Daura yayin wata ziyarar barka da Sallah da ya kai wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

A kwanakin baya ne dai Tinubun ya ɗauki Ibrahim Masari a matsayin mataimaki duk da tun a lokacin ana ta ce-ce-ku-ce kan cewa na riƙo ne, kuma shi ma Masarin a yayin wata hira da BBC a kwanakin baya ya tabbatar da cewa a shirye yake ya bar kujerar idan aka samu wanda ya fi shi cancanta.

Tinubun ya bayyana cewa duk da bai tattauna wannan batu da Kashim Shettima ba amma ga shi ya bayyana wa ƴan jarida.

Haka ma jaridun Najeriya na ruwaito cewa shi da kansa Ibrahim Masari ya janye daga takarar a wata wasiƙa da ya aika wa jam'iyyar APC.

Kashim Shettima dai a halin yanzu shi ne Sanata mai wakiltar Mazaɓar Borno ta Tsakiya.

Ya bayar da muhimmiyar gudunmawa a yaƙin neman zaɓen Tinubu a lokacin zaɓen fitar da gwani na Jam'iyyar APC.