Yadda aka yi jana'izar Muhammadu Buhari a Daura

Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Talata ne aka yi wa marigayi tsohon shugaban Najeriya, Muhamamdu Buhari jana'iza, bayan sallar La'asar a wani fili da ke kusa da gidansa, sannan aka binne shi a cikin gidansa da ke mahaifarsa ta Daura a jihar Katsina.

Sakamakon dubban jama'a da suka halarci taron jana'izar ba a samu an fito da gawar marigayin fili ba domin a sallace ta inda aka sallace ta alhali tana cikin motar.

Bayan kammala sallar, sojoji sun ɗauki gawar zuwa inda aka binne ta a cikin gidan marigayin bayan yin faretin bangirma a karo na biyu.

An dai nannaɗe gawar Buhari da tutar Najeriya mai launin fari-kore-fari, inda kuma aka cire ta lokacin da za a saka gawar a cikin kabari sannan kuma aka bai wa ɗansa, Italian Buhari ita tare da sauran kayan girmamawa da suka hada da hular soji da takalma da kuma wuka na girmamawa.

Bisa taimakawar gwamnan jihar Katsina, Umar Raɗɗa da gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi da ƙanen Aisha Buhari, ɗan marigayin ya ɗauki gawar ya saka ta a kushewarta.

An binne gawar ne bisa al'adar mutanen Daura, inda bayan saka gawar a kabarin aka ɗora itatuwa da tabarmar kaba kafin daga bisani aka zuba ƙasa.

Bayan binnewar an yi addu'o'in nema wa mamacin gafara kafin daga ƙarshe sojoji su ƙara buga bindigar ban girman ƙarshe kamar yadda al'adarsu ta tanada.

Tunda farko dai, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ne ya tarbi gawar marigayin bayan isowar jirgin da ke ɗauke da ita bisa rakiyar Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima da iyalan mamacin.

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima tare da shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila ne suka yi rakiyar gawar daga Landan zuwa Katsina, sannan aka ɗauki gawar a mota zuwa Daura.

Dubban mutane suka halarci jana'izar tsohon shugaban ƙasar da suka haɗa da shugabannin ƙasashe da sarakuna da malamai da kuma sauran al'ummar Najeriya.

A ranar Lahadi, 13 ga watan Yuli ne Muhammadu Buhari ya rasu a birnin Landan na Birtaniya bayan shafe dogon lokaci yana jinya.

Muhammadu Buhari ya rasu ne yana da shekara 82 a duniya, shekara biyu bayan sauka daga mulkin Najeriya.

Buhari ya mulki Najeriya a matsayin soja daga watan Disamban shekara ta 1983 zuwa watan Agustan 1985 kafin tuntsurar da gwamnatinsa.

Sai dai a shekara ta 2015 Buhari ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa bayan kayar da shugaba mai ci a wancan lokaci Goodluck Jonathan.

An rantsar da shi a matsayin shugaban farar hula, inda ya yi mulki Najeriya daga ranar 29 ga watan Mayun 2025 zuwa 29 ga watan Mayun 2023.

Tun hawansa mulki a zango na farko ne yake zirya zuwa asibiti a birnin Landan domin jinya.

Kwamitin jana'izar Buhari

Tun a ranar Litinin n Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya kafa kwamiti na musamman domin jagorantar jana'izar.

Kwamitin ƙarƙashin jagorancin babban sakaten gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ne ya jagoranci shiryawa tare da tsara yadda aka gudanar da jana'izar tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Katsina.

Mambobin kwamitin su ne:

  • Ministan kuɗi
  • Ministan kasafi da tsare-tsare
  • Ministan Tsaro
  • Ministan yaɗa labarai
  • Ministan ayyuka
  • Ministan cikin gida
  • Ministan Abuja
  • Ministan Gidaje da raya birane
  • Ministan kiwon lafiya
  • Ministar al'adu
  • Bai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha'anin tsaro
  • Bai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsare-tsare
  • Babban mai taimaka wa shugaba kan harkokin siyasa
  • Babban sifeton ƴansanda
  • daraktan hukumar tsaro ta farin kaya
  • Babban hafsan tsaron ƙasar.

Yadda aka yi dafifin jiran gawar Buhari a gidansa na Daura

An ba da hutun aiki a Najeriya saboda jamami

Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranar Talata, 15 ga watan Yulin shekarar 2025 a matsayin hutu domin alhinin rasuwar tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ta fitar, wanda babban sakataren ma'aikatar, Magdalene Ajani ta sanya wa hannu, inda ta ce wannan ƙari ne kan sanarwar farko ta ayyana kwana bakwai da gwamnatin ƙasar ta yi na jimamin rasuwar.

Ministan harkokin cikin gidan ƙasar, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya yi sanarwar a madadin shugaban ƙasar, Bola Tinubu.

Ministan ya ce ƙasar ta ayyana hutun ne domin nuna irin girmamawar da gwamnatin ke yi wa tsohon shugaban, da kuma godiya ga hidima da sadaukar da ya yi domin ciyar da ƙasar gaba.

Gwamnonin arewa maso yamma sun ayyana hutu ranar Talata domin rasuwar Buhari

Ƙungiyar gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana kaɗuwarsu kan rasuwar tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari wanda ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin shekarar 2025 a birnin Landan.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, wanda shugabanta, Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda ya fitar, ta ce Buhari tamkar uba yake a gare su.

Da ma dai jihar Katsina ta ayyana ranar Litinin a matsayin hutu ƙari a kan hutun da jihohin arewa maso yammacin ƙasar da na gwamnatin tarayya suka bayar.

Shugabannin duniya da suka yi ta'aziyya

Firaministan India Narendra Modi ya shiga jerin shugabanni da kuma ɗimbim alummar da ke miƙa ta'aziyyarsu bisa rasuwar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, Modi ya jinjinawa kaifin basira da jajircewar marigayi tsohon shugaban ƙasar kan ƙarfafa alaƙar India da Najeriya a lokacin mulkinsa.

Shi ma shugaban kasar Saliyo, Julius Maada Bio, ya bayyana mutuwar muhammadu Buhari a matsayin babban rashi. Daga nan ya miƙa saƙon ta'aziyarsa ga iyalan shugaban ƙasar da shugaba Tinubu da ma ɗaukacin al'ummar Najeriya baki ɗaya.

Haka kuma tsohon shugaban Liberia, George Weah ya aike da saƙonsa na ta'aziya ga Najeriya.

Haka kuma ƙungiyar Tarayyar Afrika ta aike da saƙon ta'aziyyar rasuwar Muhammadu Buhari ga iyalansa da gwamnatin Najeriya.