Yadda Iran ke korar dubun dubatar 'yan Afghanistan bayan yaƙi da Isra'ila

    • Marubuci, Najieh Ghulami
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Persian
  • Lokacin karatu: Minti 3

A wata rana mai cike da zafin rana a watan Yuli a kan iyakar Islam Qala–Dogharoon - mahaɗar Iran da Afghanistan. Manyan motocin bas ne ke ta karakina, ana ta zube fasinjojin 'yan Afghanistan da aka kora daga Iran.

Da ƙarfin tsiya aka koro su ta yadda har yanzu wasunsu ke cikin kaɗuwa, yayin da iska mai cike da ƙura ke kaɗawa, hazo na disashe sararin samaniya.

Zaune a cikin hazon, wata matashiya ce da ta fito daga cikin motar. Ta dudduba hagu da dama cikin juyayi. Sai kuma daga baya ta ɓarke da kuka, tana dukan kai da fuskarta da hannu. Tana "wayyo Allah, wace wutar ka jefa ni?"

'Yar Afghanistan ce, amma ba ta taɓa zuwa ƙasar ba. An haifa tare da rainon ta a Iran kamar sauran dubbai. Amma yanzu, bayan yaƙin Iran da Isra'ila da ya jawo zargi, ana yi wa 'yan gudun hijira kallon masu leƙen asiri da kuma korar su.

Akan kori mutum 30,000 zuwa 50,000 a lokaci guda. Ƙungiyoyin agaji sun yi gargaɗin cewa adadin 'yan gudun hijirar zai iya kaiwa miliyan huɗu nan da ƙarshen shekara.

Akwai tantunan da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya MDD ta UNHCR ta gina da za su ɗauki muutm 7,000 zuwa 10,000, amma yanzu dubun dubata ne a ciki.

Mai ɗaukar hoto ɗan Afghanistan, Mohammad Balabuluki, ya je wurin domin gane wa idonsa abin da ke faruwa. Wani dattijo da ke riƙe da sanda ya ce: "Na fita tattaki suka kama ni, suka kai ni wani sansani, yanzu kuma ga ni a nan. Matata da 'ya'yana ba su sani ba."

Ya nemi mai ɗaukar hoton ya ba shi aron wayarsa. Sai kuma ya yi shuru cikin tunani. "Ba zan iya tuna lambarta ba," a cewarsa.

Da yawan mutanen na ɗauke ne da lambobin wayar Iran. ba su san kowa ba a Afghanistan. Da yawa ba su je wurin da kuɗi ba, babu wani kaya. Wasu sun ce har yanzu suna bin bashin albashi.

Wasu mata da miji na riƙe da wani mayafi da suka lulluɓe 'ya'yansu huɗu saboda zafin rana. Sun daɗe a haka suna gumi tsawon sa'o'i. Yaran na riƙe da juna cikin firgici, kuma wannan ne karon farko da suka shigo Afghanistan, ƙasar da ake cewa "tasu".

A cikinsu akwai wata yarinya mai shekara takwas ko tara riƙe da 'yartsanarta. "Indai ina raye, 'yartsanata za ta ci gaba da zama da ni. 'Yartsanata 'yar Iran ce. Yanzu ni na zama 'yar gudun hijira, ita dole ta zama 'yar gudun hijira."

Da yawansu sun ce ana zargin su da zama 'yan leƙen asiri masu aiki da Isra'ila. Wani mutum ya ce: "Mun shafe rayuwarmu a matsayin leburori, da haƙa ramuka, da gina gidaje, da hidima a gidaje. Amma leƙen asiri? Ba mu taɓa yin wannan ba."

Wani ya ƙara da cewa: "Korarmu wani abu ne daban. Amma zagi da duka da cin mutunci, su ne abubuwan da suka fi baƙanta min."

Mazauna yankuna sun yi ƙoƙarin taimaka musu. Sukan kawo musu ruwan sha da abinci, da kuma yin zirga-zirga da su. Amma abin ya yi yawa. Da ma Afghanistan na fama da talauci, da fari, da yunwa. Yanzu kuma sai ga wannan.

Ɗan Afghanistan kuma mai ɗaukar hoto, Mohammad Balabuluki, ya sha zuwa Islam Qala domin ɗaukar halin da ake ciki. Da aka tambaye shi ko ya taɓa ganin wani abu mai kama da wannan, ya ce a'a.

"Shekara biyu da suka wuce, na je wurin da girgizar ƙasa ta faru a Herat. Kusan mutum 2,000 ne suka mutu. Amma wannan...ganin dubban mutanen da aka jibge a wurin da babu son ransu - ya fi ƙona min rai."