Tinubu zai je Birtaniya ziyarar aiki

    • Marubuci, Alicia Curry
  • Lokacin karatu: Minti 3

Fadar Buckingham ta ce a karon farko cikin shekara 37, shugaban Najeriya zai kai ziyara aiki Birtaniya, inda sarki Charles III da sarauniya Camilla za su karɓi baƙoncin shugaban Bola Tinubu.

Shugaba Tinubu da maiɗakinsa Oluremi Tinubu sun amince su ziyarci Sarki Charles a fadarsa daga ranar 18 zuwa 19 ga watan Maris.

Ziyarar aiki da shugaban Ƙasa ke kaiwa fadar Buckingham ta kasance wata muhimmiyar hanyar inganta alaƙar diflomasiyya tsakanin ƙasashe da Birtaniya, inda ake tattauna hanyoyin cin gajiyar juna.

Rabon da shugaban Najeriya ya kai irin wannan ziyara Birtaniya tun a 1989, lokacin da Janar Ibrahim Babangida ya ziyarci mariganya Sarauniya Elizabeth II, inda ya shafe kwanaki huɗu.

Duk da cewa wannan ce ziyarar farko a hukumance da shugaba Tinubu zai kai Birtaniya, a baya ya gana da Sarki Charles, bayan lashe zaɓen Najeriya na 2023.

An tarbi Tinubu da matarsa a fadar Buckingham a watan Satumban 2024, kuma sun yi ganawa da tattauna alaƙar ƙasashensu da Sarki Charles a lokacin taron COP28 a Dubai.

Amma a ziyarar shugaban ƙasa irin wadda Tinubu zai kai Birtaniya a watan Maris, ana shirya bukukuwa da faretin ban girma, da kuma nuna muhimmancin shugaban da ya kai ziyarar ga masarautar Birtaniya.

Ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da ƙididdigar gwamnati ke nuna cewa alaƙar kasuwanci tsakanin Birtaniya da Najeriya ta ƙaru zuwa sama da fan biliyan takwas a watan Oktoban bara.

Hakan ya sa Najeriya ta zamo ƙasar da ta fi kowacce muhimmanci ta fuskar alaƙar kasuwanci a Afirika baki ɗaya.

A 2024, ƙasashen biyu suka sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar kasuwanci da zuba jari da nufin faɗaɗa alaƙar da ke tsakanin su.

Kawo yanzu ba a sanar da abubuwan da ziyarar ta watan Maris za ta mayar da hankali ba, kuma babu cikakken bayanin tsare-tsaren da aka yi, amma a yadda aka saba ana zagayawa da shugaban ƙasa wurare masu muhimmanci ga masarautar Birtaniya, da halartar babban taron manyan jami'an Birtaniya da kuma ganawa da jiga-jigan ƴan siyasa.

A 2025, Sarki Charles ya karɓi baƙoncin shugabannin ƙasashe uku da suka haɗa da na Faransa Emmanuel Macron da na Amurka Donald Trump da kuma na Jamus Frank-Walter Steinmeier. Kuma karon farko da Birtaniya ta karɓi baƙoncin shugabannin ƙasashen duniya har uku, tun bayan 1988.

Sarki Charles na da alaƙa mai kyau da Najeriya, wadda mamba ce a ƙungiyar ƙasashe rainon Birtaniya, kuma ya bayyana sha'awarsa ga turancin Pidgin da ma salon waƙar Afrobeat na Najeriya.

Kafin zama sarki, ya ziyarci Najeriya sau huɗu a matsayin yariman Wales, a 1990 da 1999 da 2006 da kuma 2018.

A 2023 aka ƙaddamar da shirin King's Trust International a Najeriya, wani shiri na magance matsalar rashin aikin yi tsakanin matasa.