Ƙungiyoyi na rububin Kolo Muani, wataƙil Morton ya je Lyon

Asalin hoton, Getty Images
Tottenham da Manchester United da Newcastle na sa ido kan ɗan wasan gaba a Paris St-Germain, Randal Kolo Muani mai shekara 26, bayan fuskantar jinkiri a tafiyarsa Juventus. (Le Parisien - in French)
Ɗan wasan gefe a Manchester United daga Argentine, Alejandro Garnacho mai shekara 21, na son tafiya Chelsea a kokarin da ya ke na barin Old Trafford. (Fabrizio Romano)
Chelsea na zawarcin ɗan wasan gaba a RB Leipzig, Xavi Simons mai shekara 22, yayin da ƙungiyar ke kafa-kafa kan musayar 'yan wasanta. (Sun)
Valencia na gab da cimma yarjejeniya da ɗan wasan tsakiya a Sifaniya, Javi Guerra, mai shekara 22, wanda ke jan hankalin Manchester United da AC Milan. (Marca - in Spanish)
West Ham ta gabatar da tayin yuro miliyan 8 kan ɗan mai tsaron raga a Botafogo da Brazil, John Victor mai shekara 29, yayinda Galatasaray da Everton da Manchester United kowanne ya nuna zawarci a baya. (Fabrizio Romano)
Lyon na tattaunawa da Liverpool kan yiwuwar cimma yarjejeniya da ɗan wasan tsakiya, Tyler Morton mai shekara 22. (Sky Sports)
Manchester City a shirye take ta sayar da ɗan wasan tsakiya Jack Grealish mai shekara 29 da James McAtee mai shekara 22, da Kalvin Phillips mai shekara 29, da kuma mai tsaron raga a Jamus Stefan Ortega, mai shekara 32, idan ta samu tayi mai kwaɓi a bana. (Athletic - subscription required)
Ɗan wasan baya AZ Alkmaar David Moller Wolfe, mai shekara 23 zai je Ingila domin a duba lafiyarsa a Wolves, kan yarjejeniyar fam miliyan 12 da ƙungiyar. (Sky Sports)
Ɗan wasan baya a Inter Milan Yann Bisseck mai shekara 24, ya yi watsi da tayin Crystal Palace kan fam miliyan 28. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Atalanta ta yi watsi da tayin fam miliyan 36.5 kan ɗan wasanta na Najeriya daga Inter milan Ademola Lookman mai shekara 27, inda ta bukaci fam miliyan 43.5. (Fabrizio Romano)
Middlesbrough ta amince da yarjejeniyar £3.5m kan ɗan wasan Blackburn Callum Brittain, mai shekara 27. (Sky Sports)










