Yadda mayaƙan RSF suka kashe majinyata 460 a asibitin Sudan - WHO

Asalin hoton, AP
- Marubuci, Lucy Fleming
- Marubuci, Richard Kagoe
- Lokacin karatu: Minti 3
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya ce dakarun RSF sun kashe ɗaruruwan fararen hula a babban asibitin el-Fasher, kwanaki bayan karɓe iko da birnin da ke Sudan.
Dokta Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce WHO ta yi ''matuƙar kaɗuwa'' kan rahotonnin kisan mutum 460 a asibitin.
Tun da farko ƙungiyar likitocin Sudan ta faɗa a ranar Talata cewa mayaƙan RSF sun ''kashe duk mutanen da suka samu a cikin asibitin, ciki har da marasa lafiya da masu zaman jinyarsu''.
Sai dai ƙungiyar ba ta bayar da alƙaluman mutanen da aka kashe ba, amma ta ce an mayar da cibiyoyin lafiyar birnin zuwa kwata ko mayanka, inda ake kashe mutane.
Haka kuma ƙungiyar Likitocin ta Sudan ta zargi RSF da yin garkuwa da wasu ma'aikatan lafiya shida - ciki har da likitoci huɗu da masanin magunguna da kuma ma'aikacin jinya ɗaya.
Ƙungiyar ta kuma bayar da rahoton cewa RSF ta buƙaci kuɗin fansa da ya kai dala 150,000 domin sakin mutanen shida.
A ranar Talata ne mayaƙan RSF suka kai wa Asibitin Saudi hari a birnin na el-Fasher.
El-Fasher ya kasance birni na ƙarshe da ya rage a hannun dakarun sojin gwamntin ƙasar a yankin Darfur, kuma a ranar Lahadi ne RSF ta ƙwace ikonsa bayan shafe wata 18 tana yi masa ƙawanya tare da haifar masa yunwa da ruwan boma-bomai.
Tun bayan ɓarkewar yaƙin Sudan a watan Afrilun 2023, an riƙa zargin ƙungiyar RSF da ƙawarta, Arab Militia a Darfur da kai wa ƙabilun da ba na Larabawa ba hare-hare - zargin da RSF ta sha musantawa.
A yanzu da RSF ta ƙwace birnin el-Fasher, Majalisar Dinkin Duniya da masu fafutika da ƙungiyoyin agaji na fargaba game da makomar mutum 250,000 da ke maƙale a birnin, mafi yawansu waɗanda ba Larabawa ba.
Rashin kyawun sadarwa ya kawo tarnaƙi wajen tabbatar da ainihin abin da ke faruwa a birnin.
Sashen tantance labarai na BBC ya yi nazarin wasu bidiyoyi da aka wallafa a shafukan sada zumunta da ke nuna mayaƙan RSF na kashe wasu mutane masu yawa da ba sa ɗauke da makamai cikin ƴan kwanakin nan.

Asalin hoton, AFP/Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yayin da yake da wahalar samun rahotonnin abubuwan da ke faruwa a ƙasa, ƙungiyoyin agaji sun ce a yanzu ne za a fara sanin irin ɓarna da aka yi a el-Fasher kewayenta.
Wasu mutane na ƙoƙorin ɗaukar hatsarin tafiya zuwa garin Tawila, mai nisan kilomita 60 yamma da el-Fasher, tare da bayyana irin mummunar uƙubar da suka shiga.
"A ranar Asabar ne hare-haren suka yi matuƙar muni, inda muka rasa zaɓi illa mu fice daga el-Fashir," kamar yadda wani mutum ya shaida wa BBC.
"A kan hanya, mayaƙan RSF suka kama su suka doke mu tare da cin mutuncinmu, sanna suka ƙwace mana duka kayayyakinmu, suka kuma yi garkuwa da wasunmu tare da karɓar kuɗin fansa domin sakinsu''.
"Wasu da suka yi garkuwar da su kashe su suka yi daga baya. A lokacin wannan tafiya an kama mutane da dama, kuma mun sha wahalar yunwa da ƙishirwa.''
Jan Egeland, Tsohon babban jami'in jin kai na MDD ya shaida wa BBC cewa ana cikin yanayin bala'i a birnin.
"Mun fuskanci kisan kiyashi a cikin waɗannan watanni, ga yunwa da rashin magunguna,'' in ji shi.
Dr Tedros ya ce gabanin kai harin Asibitin Saudi, WHO ta tabbatar da hare-hare 185 kan cibiyoyin lafiya tun bayan fara yaƙin, lamarin da ya haifar da kisan mutum 1,204.
"Dole ne a gaggauta dakatar da duka hare-hare kan cibiyoyin lafiya ba tare da sharaɗi ba. Dole ne a bai wa marasa lafiya da jami'an lafiya da cibiyoyin lafiya kariya, kamar yadda dokokin duniya kan yaƙi suka tanadar." in ji shi
Ƙwace birnin el-Fasher ya raba ƙasar Sudan zuwa gida biyu, inda a yanzu RSF ke iko da mafi yawan yankin Darfur da Kordofan mai maƙwabtaka, yayin da sojojin ƙasar ke iko da babban birnin kasar Khartoum da yankunan tsakiya da gabashin ƙasar da ke kusa da tekun Maliya.
Ɓangarorin biyu masu faɗa da juna a baya sun kasance kawayen juna - inda suka ƙwace mulkin ƙasar tare a wani juyin mulki a 2021.
Sai dai a yanzu yaƙinsu ya hana su cika alkawarin da suka ɗauka na mayar da ƙasar kan tafarkin mulkin dimokraɗiyya.











