Maganin da ke iya sa mata jin 'ƙarfin sha'awa' ba tare da sun sani ba

Magani.

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 5

Mutanen da ke fama da matsalar tafiya, ciki har da ciwon ƙafa, sun ce likitoci sun kasa yi musu gargaɗi game da mummunar illar shan magunguna ba tare da amincewar likitoci ba - wanda ya janyo su shiga ɗabi'un jima'i masu haɗari.

Mata 20 sun shaida wa BBC cewa magungunan da aka ba su na ciwon ƙafa sun lalata rayuwarsu.

Wani rahoto da kamfanin harhaɗa magunguna na GSK ya fitar a 2003, wanda BBC ta gani, ya nuna cewa akwai alaƙa tsakanin wani magani da aka fi sani da agonist da kuma ɗabi'ar jima'i maras kyawu.

An kuma ba da misalin wani mutum da ya yi lalata da wani yaro yayin da yake shan maganin cutar matslar ƙwaƙwalwa.

Ko da yake babu wani takamaiman bayani game da wannan illar a cikin bayanin da aka bayar, amma hukumar kula da magunguna ta Birtaniya ta faɗa mana cewa, akwai gargaɗi game da ƙaruwar sha'awar jima'i da halaye masu cutarwa.

Kamfanin GSK ya ce takardun bayanai sun kuma nuna irin barazanar da ke tattare da sauyawar son yin jima'i.

Wasu mata waɗanda suka ce an jefa su cikin barazanar jima'i mai haɗari, sun faɗa mana cewa ba su san abin da ya janyo shi ba.

Wasu sun cean tilasta musu yin caca duk da cewa ba su taɓa yi ba a baya. Akwai wanda ya jefa kansa cikin bashin da ya kai fam 150,000.

Barin gida don jima'i

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kamar mata da yawa, Claire ta fara gamuwa da ciwon ƙafa ne lokacin da take da juna biyu. Ta fuskanci matsalar rashin barci da kuma ƙaiƙayin fata haɗe da matsuwar tafiya.

Lokacin da matsalar ta ki ci ta-ki cinyewa bayan haihuwarta, an ce ta sayi maganin dopamine wanda zai taimaka mata.

Ta ce likitoci ba su yi mata gargaɗi kan illar da maganin ke da shi ba.

Ta ce da farko maganin ya yi mata aiki sosai, sai dai bayan shekara ɗaya ko fiye da haka ta fara jin jarabar jima'i wanda ba ta saba ji ba.

Claire ta ce sun fara barin gidajensu tun da sanyin safiya don yin jima'i.

Ta ce ta saka riga da ke nuna jikinta a waje, yayin da take sanye da rigar sanyi, za ta ja rigar saka zuwa kirjinta duk lokacin da ta ga namiji.

Ta ƙara da cewa duk da tana da abokin zama, tana fita zuwa yin jima'i a wurare masu haɗari.

"Zuciyarka tana faɗa maka cewa abin da kake yin nan fa ba shi da kyau amma abin ya riga da ya yi tasiri a wajenka har ka manta kana yin sa," in ji Wu.

Claire ta ce an shafe tsawon lokaci kafin a alaƙanta maganin da jarabar jima'i, inda ta ce bayan ta daina shansa, jarabar ta tafi.

Suna jin ƙunya da baƙin ciki kan irin haɗarin da suka jefa kansu a ciki.

Claire

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Claire ta ce ta fara barin gidanta a kowace sanyin safiya don zuwa yin jima'i

Matsalar tafiya da cin zarafin jima'i

A cewar hukumar lafiya ta NICE, yin abu ba tare da tunani ba, ciki har da caca da ƙaruwar jarabar jima'i, an daɗe da saka su da cewa suna cikin abubuwan da ke janyo shan magani ba tare da amincewar likita ba - kuma ana tsammanin ya shafi tsakanin kashi shida zuwa 17 na masu matsalar tafiya.

A cewar hukumar lafiya ta NHS, illolin shan magani barkatai na shafar kashi ɗaya cikin mutane kaɗai.

Waɗannan kwayoyi suna aiki ta hanyar sanya kwakwalwa ta yi aiki yadda ya kamata.

'Ban san cewa laifina ba ne'

Ba a san yawan adadin mutanen da maganin ya sanya suka shiga jarabar jima'i ba, a cewar farfesa Valerie Vaughan na Jami'ar Cambridge, sannan ba a bayar da rahoto kan waɗanda abin ya shafa ba.

"Akwai tsangawama da yawa ga mutanen da suka tsinci kansu kan matsalar, kuma mutane ba su gane cewa magani ne ya haddasa shi ba," in ji ta.

Farfesa Vaughan ta yi imanin cewa ya kamata a gargaɗi cibiyoyin kiwon lafiya musamman game da sanya mutane cikin jarabar jima'i kuma ya kamata a bincike su saboda lahanin su yana da girma.

Ana tsammanin cewa cutar ƙafa ta RLS ta shafi mutum ɗaya cikin 20 kuma mata sun fi barazanar kamuwa da cutar sau biyu ga maza.

Masu fama da lalurar 20 da muka tattauna da su sun bayyana cewa, ba wai likitocin sun gaza sanar da su illar illar da magungunan ke yi ba, sun ma ƙasa tantance illar da magungunan ke yi a jikinsu.

Sarah tana da shekaru 50 lokacin da aka rubuta mata wani maganin na dopamine wanda wani kamfani ya samar da shi.

"A baya, idan Brad Pitt ya zo cikin ɗakin tsirara, ba zan damu ba," in ji ta. "Amma wannan magani ya mayar da ni zuwa macen da ke jarabar son jima'i."

Sarah ta fara sayar da fantin mata da aka yi amfani da shi da kuma bidiyon jima'i, sannan tana jima'i ta waya da wasu mutane daban. Ta kuma shiga caca abin da ya kai ta ga shiga bashin fam 30,000.

Daga baya an kwantar da ita don kula da ita a asibiti, aka kuma karɓe mata lasisin tuki har ma ta rasa aikinta.

"Na koma ga abubuwa da ba su da alfanu ga lafiya, na san wannan ba ɗabi'ata ba ce amma na ƙasa shawo kaina," ta faɗa wa BBC.

Wata mata ita ma mai suna Sue, ta ce an rubuta mata sayen magunguna kala biyu kuma ba a yi mata gargaɗi kan illolin da za su haifar ba.

Ta ce lokacin da aka rubuta mata magani na biyu da za ta saya, ta yi magana kan ɗabi'unta na caca, wanda ya sa ta rasa fam 80,000. 'Lamarin ya yi mummunar tasiri kan iyalina. Na rasa kuɗin da ya kamata ya sauya min rayuwa.'

"Amma a lokacin ban san cewa laifina bane," in ji ta.

Lucy
Bayanan hoto, Wata mata mai suna Lucy, ta ce ta ɓata shekara goma na rayuwarta wajen caca da kuma shiga jarabar jima'i bayan shan maganin dopamine.

Rugujewar alaƙa

BBC ta gano cewa wasu mutum huɗu masu fama da lalurar ƙafa, sun ɗauki matakin shari'a kan kamfanin GSK a 2011.

Sun ce maganin ya janyo musu cin bashi na caca da kuma rugujewar alaƙa. Sun kuma yi ƙorafin cewa kamfanin GSK ya ƙasa saka gargaɗi kan magungunansa har sai zuwa watan Maris ɗin 2007, duk da cewa bincike ya nuna cewa akwai alaƙa ta jarabar jima'i da maganin a farkon shekarun 2000.

Sai dai, GSK ya musanta alhaki a lamarin.

An kuma samu mummunar tasiri da maganin ya yi a wasu ƙasashe.

Mata da yawa waɗanda BBC ta tattauna da su, su ma sun yi ƙorafin cewa amfani da maganinna tsawon lokaci ya janyo ciwonsu ya yi ƙamari.

A cikin wata sanarwa, GSK ya faɗa wa BBC cewa maganin ya bi gwaje-gwaje da dama kafin fitar da shi.

A cewar kamfanin, maganin yana da inganci, sai dai kamar dukkan magunguna, shi ma yana da tasiri na daban - kuma an bayyana haka cikin bayanin maganin.