Yadda wani mutum ya ƙona agololinsa biyar bayan faɗa da uwarsu

Asalin hoton, NPF
Rundunar ‘yan sanda a jihar Ondo a kudu maso yammacin Najeriya ta kama wani mutum mai shekara 54 da haihuwa bisa zargin ƙona agololinsa biyar a unguwar Fagun da ke garin Akure.
Rahotanni sun ce wanda ake zargin ya yi hakan ne saboda matarsa wadda ita ce mahaifiyar waɗannan yara, ta ɓata masa rai saboda ta ƙi ba shi haɗin kai.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Funmilayo Odunlami, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin ta ce yaro ɗaya ya rasu amma sauran huɗun suna karbar magani a cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Owo.
Ta ce tuni aka kama mutumin mai shekara 54 da haihuwa bisa zargin ƙona ‘ya’yan matar tasa biyar.
Tace “Wani mutum ne ya zo ya bayar da rahoton abin da ya faru cewa wanda ake zargi Joseph, ya samu rashin fahimta tsakaninsa da matarsa, to saboda ya nuna rashin jin daɗin abin da ya faru - sai ya shiga ɗakin da yaran suke barci shi ne ya banka musu wuta.
Ta ƙara da cewa wannan wani lamari ne da ake zargin mutumin da yunƙurin kisan kai, kuma suna bukatar su yi bincike mai zurfi kan wanda ake zargin don sanin musabbabin faruwar abin da aka zargin cewa ya aikata.
Rundunar ‘yan sandan ta ce a halin da ake ciki, an tura wannan lamari zuwa ga sashen binciken manyan laifuka na (CID) don gudanar da binciken kwakwaf.
Kamar yadda ganau suka ce, tun farko rashin fahimtar ta yi tsanani bayan da uwar yaran ta ɓata wa mai gidanta rai saboda rashin fahimta da ta taso a tsakaninsu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sai dai wani ganau da bai so a bayyana sunansa ba, ya ce wanda ake zargin ya yi yunƙurin kusantar matarsa to amma ta ƙi amincewa da bukatarsa- wani abu da ake zaton ya ɓata masa rai kuma ya nemi huce fushinsa kan yaran da ke barci, da ba su san hawa ba su san sauka ba.
Ana zargin Joseph da zazzage man fetur a cikin dakin da yaran ke barci, inda kuma nan take ya bankawa dakin wuta kuma ta gobara ta tashi.
Rundunar ‘yan sanda ta ce yaron wanda uban riƙon nasa ya yi ajalinsa ya ƙone ta yadda ba za a iya gane shi ba.
Ita ma dai mahaifiyar yaran ta tsallake rijiya da baya daga gobarar da raunuka tare da tagwayenta ‘yan wata 18 wadanda ‘ya’yan mutumin ne.
A lokuta da dama rikici kan kaure a tsakanin ma’aurata wanda a yanayi irin wannan kan tilasta musu danganawa ga kotu domin a raba auren ko kuma a samar da mafita don gyara aure tsakankanin ma’auratan.
A nan gaba ne za a gurfanar da mutumin da ake zargi da danyen hukunci a gaban kotu, bayan ‘yan sanda sun kammala bincike a kan musabbabin yunkurin ƙona yaran da sanadin mutuwar daya daga cikinsu.











