Ana zargin wani uba da cire wa ƴarsa 'nono' ta amfani da dutsin guga a Lagos

Yan sandan Najeriya

Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta cafke wani mutum da ake zarginsa da cire wa ƴarsa ƴar shekara takwas nono ta hanyar amfani da dutsen guga mai zafi.

Bayanai sun ce mahaifin ya aikata wa ƴarsa ɗanyen aikin ne sakamakon takaicin yadda kirjinta ya fara nuna alamun 'kirgen dangi', alamun farko na balaga.

A yanzu yarinyar na kwance a asibiti inda ake kula da lafiyarta, yayin da rahotanni ke cewa tana cikin mawuyacin hali, sakamakon ta'asar da mahaifinta da ake kira Mista Banjo ya aikata mata saboda a tunaninsa ta yi saurin balaga a shekarunta.

Wata kungiyar kare haƙƙin yara da marasa galihu ce ta kai ƙarar mahaifin ga ƴan sanda, kuma kakakin ƴan sandan jihar Legas DSP Asijebotu bai musanta labarin ba inda ya ce za su gudanar da bincike.

Wasu rahotanni a Najeriya sun ce yanzu haka iyayen yarinyar na tsare a hannun ƴan sandan jihar Legas.

Kwamred Ebenezer Omejalile, shugaban kungiyar kare hakkin yara da marasa galihu da ta kai ƙarar mahafin ya shaida wa BBC cewa Mista Banjo da ake kira Panel, "ya gurje da ƙone nonon ƴarsa."

"Mahaifin yarinyar ya yi amfani da dutse mai zafi da ya lulluɓe da tsumma har sai da ya tabbatar cewa ya illata nonon ƴar tasa," in ji shi.

Ya kuma ce uban ya nuna rashin amincewarsa yadda ƴarsa da ake kira Aisha ta yi saurin fara nuna alamun fitowar kirgen dangi a kirjinta, kuma don yana son su daina girma.

Mahaifiyar yarinyar ta ce a kullum Mista Banjo kan bi 'yarsa da duka. Sai dai kwamred Ebenezer ya ce "a gaban mahaifiyar mijinta ya aikata ta'asar"

Kuma kwamred Ebenezer ya ce mahafin yarinyar ya amsa masa cewa shi ya aikata laifin.

Abin da ya fi baƙanta wa mahafin rai a cewar kwamred Ebenerzer, shi ne yadda uban yarinyar ya ce shi ne yake yi wa yarinyar 'yar shekaru 8 wanka a kowa ce rana.