Amurka da Majalisar Ɗinkin Duniya sun damu kan halin da Bazoum ke ciki

Asalin hoton, AFP
Amurka da Majalisar Ɗinkin Duniya sun bayyana damuwa game da tsaron lafiya da rayuwar hamɓararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum, tun bayan kifar da gwamnatinsa ranar 26 ga watan Yuli.
Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce yana cike da damuwa kan abin da ya kira "mummunan halin rayuwa" da Mohamed Bazoum da iyalansa waɗanda masu juyin mulki ke ci gaba da tsarewa, suke ciki.
Wani mai magana yawun Babban Sakataren, ya ruwaito Antonio Guterres na bayyana tsananin damuwa a kan tsaron lafiya da rayuwar Bazoum da iyalinsa, yayin da kuma ya yi kira a gaggauta sakin hamɓararren shugaban ba tare da wani sharaɗi ba kuma a mayar da shi kan mulki.
Matakin ya zo ne bayan wani rahoto da gidan talbijin na Amurka wato CNN da ke ruwaito cewa sojojin da suka yi juyin mulki sun ajiye shi cikin kaɗaici kuma suna tursasa masa cin shinkafa garau-garau.
Bazoum ya kuma aika wani taƙaitaccen saƙon waya ga wani abokinsa, inda yake bayyana masa cewa an "hana shi tuntuɓar kowa tun ranar Juma'a", sannan ya kasa samun ƙarin kayan abinci da magunguna, kamar yadda CNN ta yi ƙarin bayani.
Shi ma wani mai magana da yawun ma'aikatar wajen Amurka ya ce "Mun damu matuƙa a kan batun lafiya da tsaron rayuwarsa da kuma na iyalinsa".
Tun farko, jam'iyyar Shugaba Bazoum ta ce ana tsare da shi da iyalinsa a cikin wani yanayi na "rashin tausayi" da kuma "rashin mutuntawa" kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
Mambobin gwamnatin mulkin sojan ba su ce komai ba game da halin da hambararren shugaban Nijar ke ciki ba.
A ranar Talata sakataren harkokin wajan Amurka Anthony Blinken ya kira Shugaba Bazoum ta waya yana mai ba shi tabbacin samun goyon bayan Amurka, in ji ma'aikatar kula da harkokin wajen Amurka.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Mathew Miller ya kara da cewa: "Yayin da lokaci ke tafiya, ana tsare da shi a wani wuri da aka keɓe, kuma al'amari ne da muka nuna damuwa a kai ."
Jam'iyyar Shugaba Bazoum wato PNDS-Tarayya, a cikin wata sanarwa ta kuma yi iƙirarin cewa an hana shugaba Bazoum da iyalansa damar samun ruwan sha da wutar lantarki.
Sanarwar ta zo daidai da wani furucin firaministan hamɓarriyar gwamnatin Nijar Ouhoumoudou Mahamadou, a baya, inda ya ce ana tsare da shugaba Bazoum da matarsa da ɗansa, ba tare da wutar lantarki ko ruwa ba.

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ƙungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta debarwar jagororin juyin mulkin Nijar wa'adin kwanaki bakwai da su sauka tare da mayar da shugaba Bazoum kan karagar mulki.
Shugaban masu gadin fadar shugaban kasa, Janar Abdourahmane Tchiani, ya yi ikirarin cewa shi ne ke rike da ragamar mulki Nijar a yanzu; yayin da gwamnatin mulkin sojan kasar ta nada tsohon ministan kudi Ali Mahaman Lamine Zeine, a matsayin sabon firaminista bayan juyin mulki .
A ranar Alhamis ne dai jam'ian kungiyar ta ECOWAS za su gana domin shawarar abin da za su yi na gaba.
Sabuwar gwamnatin mulkin soja ta kuma rufe sararin samaniyar Nijar har sai abin da hali ya yi, saboda barazanar amfani da karfi Soji da ECOWAS ta yi.
A ranar Laraba , Faransa ta musanta zargin da gwamnatin mulkin sojoji ta yi a kan cewa tana kokarin tada zaune tsaye a kasar.
Shugabannin juyin mulkin sun yi ikirarin cewa jiragen saman Faransa sun keta sararin samaniyar kasar sannan sojojin Faransar sun saki wasu mayaka masu ikirarin jihadi da ake tsare da su domin a kai wa sojojin kasar hari.
" Faransa ta fito fili karara ta musanta zarge-zargen da masu juyin mulki a Nijar suka yi," a cewar sanarwar da ma'aikatar tsaron Faransa da na harkokin wajan kasar suka fitar kamar yada kamfanin dilancin labarai na AFP ya ruwaito.

Asalin hoton, Getty Images
Amurka da Faransa sun kafa sansanonin soji a Nijar karkashin shirin dakile ayuikan kungiyoyin masu ikirarin jihadi da ke wasu sasan kasar.
Nijar ta koma sansanin dakarun Faransa bayan da aka koresu daga Mali bayan juyin mulki sojoji.
A wani bangare na yunkurin diflomasiya, wakilai biyu da shugaba Bola Ahmed Tinubu na Nijeriya ya aika kasar sun gana da gwamnatin mulkin soja a Yamai babban birnin kasar.










