Wane ne Sowore, kuma me ya sa ake ƙorafi kan shafinsa na X?

....

Asalin hoton, @YeleSowore

Lokacin karatu: Minti 3

A ranar 6 ga watan Satumbar 2025 ne Hukumar DSS ta wallafa sanarwa a shafinta na X, inda ta bayyana cewa tana neman a gaggauta rufe ko dakatar da shafin ɗan gwagwarmaya Omoyele Sowore a dandalin X.

Hukumar ta DSS ta ce ta yi hakan ne bisa zargin ɗan gwagwarmayar da yaɗa bayanan ƙarya da cin mutunci da kuma kalaman da hukumar ta ce suna iya jawo rikici da barazana ga tsaron ƙasa.

Mene ne ya faru?

DSS ta ce ta gano kalaman da Sowore ya wallafa a ranar 25 ga watan Agusta, 2025, da ƙarfe 11:38 na dare a shafinsa na X, inda ya yi suka ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu tare da wulaƙanta shi.

Kalaman da Sowore ya yi kan Tinubu su ne "Wannan mai aikata laifin @officialABAT ya tafi Brazil yana cewa babu cin hanci da rashawa a gwamnatinsa a Najeriya. Wane irin ƙarfin guiwa ne ya sa shi yin wannan ƙarya ba tare da jin kunya ba?"

Kalaman Sowore barazana ce ga tsaron ƙasa - DSS

Hukumar ta bayyana cewa kalaman da Sowore ya rubuta kai tsaye ya yi nuni da shugaba Tinubu kuma barazana ce ga tsaron ƙasar.

Tun bayan da ya wallafa waɗannan kalamai, ya jawo ce-ce-ku-ce daga magoya bayan shugaban ƙasan, da ƴan Najeriya da sauran mutane wanda hakan ke ƙara haifar da hayaniya da barazanar tashin hankali.

DSS ta ce kalaman Sowore sun ƙunshi;

  • Bayanai da za su iya kawo tashin hankali da ɓata sunan shugaban ƙasa.
  • Kalaman ɓatanci da cin mutunci da za su iya ɓata hoton Najeriya a idon ƙasashen duniya.
  • Ƙarya da yaɗa bayanan da za su iya tada ƙiyayya da hargitsi tsakanin jama'a.

Sanarwar ta ƙara da cewa kalaman Sowore ya saɓawa dokokin ƙasa, ciki har da Sashe na 51 na dokokin hukunta masu laifi, da kuma Sashe na 19, 22 da 24 nadokoin laifukan intanet ta 2025, waɗanda suka haramta yaɗa labaran ƙarya da wulaƙanci da cin mutunci da zagi da kuma kalaman da ke iya tada rikici.

Haka zalika, DSS ta ce kalaman ya saɓawa Dokar Hana Ta'addanci ta 2022, wadda ke ɗaukar irin waɗannan kalamai a matsayin barazana ga tsaron ƙasa.

Dalilin neman rufe shafinsa na X

Hukumar DSS na ganin cewa ci gaba da barin Sowore yana amfani da X don yaɗa irin waɗannan kalamai zai ci gaba da haifar da rikici da ɓatanci ga shugaban ƙasa, da kuma ɓata sunan Najeriya.

Hukumar ta ce rufe ko dakatar da shafin nasa zai hana ci gaba da yaɗa bayanan da za su iya haifar da hatsari ga zaman lafiya da tsaron ƙasa.

Sai dai a gefe guda, masana harkokin dimokuradiyya da masu fafutuka na iya ganin wannan mataki a matsayin yunƙurin murƙushe 'yancin faɗar albarkacin baki da dandalin dimokuradiyya, musamman ganin Sowore ya shahara wajen amfani da kafafen sada zumunta don bayyana ra'ayoyinsa da sukar gwamnati.

Ana ganin buƙatar ta hukumar DSS ka iya kai wa ga rufe shafin X ɗin na Sowore.

Shin wane ne Omoyele Sowore?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Omoyele Sowore sananne ne a Najeriya da waje a matsayin ɗan jarida da ɗan gwagwarmaya da mai fafutukar kare haƙƙin bil'adama da kuma ɗan siyasa.

An haifi Yele Sowore a ranar 16 Fabrairu a 1971 a yankin Neja Delta man fetur da ke kudu maso kudancin Najeriya. Amma asalinsa shi ne garin Ese-Odo da ke jihar Ondo a Kudu maso yammaci.

Shi ne wanda ya kafa gidan jaridar Sahara Reporters, wani dandali na kafar yada labarai ta intanet da ya shahara wajen fitar da rahotanni kan cin hanci da rashawa.

Sowore ya yi takarar shugabancin ƙasa a shekarar 2019 da 2023, kuma ya fi amfani da kafafen sada zumunta wajen yaɗa manufofinsa da sukar gwamnati.

A tarihinsa, ya sha fuskantar kama da tsarewa daga hukumomi.

A ranar 2 ga watan Agusta 2019, gwamnati ta kama shi bisa zargin laifin cin amanar ƙasa.

Bayan share fiye da watanni uku a tsare, aka sake shi a ranar 5 ga watan Disambar 2019, amma aka sake kama shi a cikin kotu bayan sa'o'i ƙadan da sake ki.

Daga baya, ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya karɓi shari'ar daga hannun DSS, kuma daga bisani aka sake shi ranar 24 ga Disambar 2019 bayan tsananin matsin lamba daga cikin gida da ƙasashen waje.