Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda aka yi wa ƴar shekara tara maras lafiya fyaɗe a Kano
Gargaɗi: Akwai abubuwan da za su iya tayar da hankalin mai karatu
A jihar Kano, ma’aikatar kula da harkokin mata da yara da kuma masu buƙata ta musamman ta ce za ta tabbatar an yi wa iyayen yarinyar nan da aka yi wa fyaɗe ta rasu adalci.
Ana zargin wani mai kyamis da yi wa wata yarinya ƴar shekara 9 fyade a lokacin da take zazzaɓi aka kaita a duba ta, al’amarin da ya yi sanadin mutuwarta.
Yanzu haka dai gwamnatin jihar Kano ta ce za ta ɗauki mataki kan al'amarin.
Cikin wata sanarwa da kwamishinaniyar harkokin mata da ƙananan yara, Hajiya Aisha Lawan Saji ta fitar, ta ce "dole ne su wuce gaba a yi adalci ga wannan ƴar ƙaramar yarinyar da ta rasa ranta saboda ɗabi’ar dabbobi da wannan mutum ya nuna".
Mahaifin yarinyar Sadiq Badamasi ya shaida wa BBC cewa lamarin ya afku ne lokacin da ya kai ƴaƴansa mata biyu da namiji ɗaya, kyamis a duba su saboda suna zazzaɓi, a unguwar Jaba a birnin Kano.
Malam Sadiq ya ce mai kyamis ɗin ya ce mazan biyu za a yi masu allura yayin da ita kuma yarinyar za a ƙara mata ruwa.
"Bayan na koma sai na tarar an ƙara mata ruwan abun da yake faɗa ke nan, da rigar a hannu ya ajiye ta a gefen benci, sai ta ce mani 'Abba ciwo ƙuguna da cinyata ko ina yana ciwo'," in ji mahaifin yarinyar.
"Mun kawo ta gida, bayan wani lokaci kuma sai ta sake galabaicewa, ta riƙa zubar da jini sosai, bayan mun sanar da mai kyamis sai ya ce a je ayi mata hoto," cewar malam Sadiq
Sadiq Badamasi ya ce sun tafi zuwa wurin yi mata hoton, sai yaji bai gamsu ba, don haka ya tafi asibitin gwamnati.
"Sun duba ta asibitin Murtala suka kuma tabbatar cewa fyaɗe aka yi mata gaba da baya, abu mummuna wanda ya ƙazanta sosai, saboda idan aka ɗaga yarinyar kana hango kayan cikin ta duɓurarta da kuma gabanta, bayan wani lokaci sai Allah ya yi mata rasuwa."
Kuma ko da aka bibiyi lamarin, sai aka fahimci cewa mai kyamis ɗin da ya duba ta ake zargi da afka mata, inda aka kama shi. Kuma tuni aka gurfanar da shi a gaban kotu.
Barrista Badamasi Sulaiman Gandu shi ne lauyan iyayen marigayiyar, ya kuma shaida wa BBC cewa an tuhumi mai kyamis ɗin da laifin fyaɗe da kuma kisan kai, "Ya musanta duka zarge-zargen, kuma kotu ta tura shi gidan gyaran hali zuwa ranar 30 ga watan Satumba domin ci gaba da sauraren shari'ar."
Matsalar fyaɗe ta jima tana ci wa al’umma tuwo a ƙwarya a Najeriya kuma fyaden bai tsaya a kan manya ko ƴan mata ba, galibi a wannan zamanin an fi cin zarafin ƙananan yara da jarirai.
Kuma mutane da dama ba su fitowa su sanar da hukumomi saboda tsoron tsangwama.
Wasu dai na ganin rashin hukunta waɗanda aka samu da laifin fyaɗe ne yake sanya al'amarin ƙara ta'azzara, a gefe guda kuma akwai masu kiraye-kirayen da a tsaurara dokokin hukunta waɗanda aka samu da laifin.
A shekarar 2014, Majalisar dokokin jihar Kano ta yi wa sashen na 283 na dokar Penal ta jihat gyara domin ƙara tsananta hukuncin da ake yi wa masu fyaɗe.
Inda dokar ta tanadi hukuncin ɗaurin aƙalla shekara 14 a gidan yari har zuwa ɗaurin rai da rai.
To amma kamar yadda abin yake a sauran ƙasashe masu tasowa na duniya, kama waɗanda ake zargi da laifin yin fayɗe ya yi ƙaranci.
Fyaɗe a kan ƙananan yara wani lamari ne da ke iya yin matuƙar illa ga rayuwarsu. Baya ga illar da za a gani na nan take, lamarin na yin illa ga wasu har zuwa ƙarshen rayuwa.
Bayanai sun nuna cewa yara da ake yi wa irin wannan fyaɗe kan faɗa cikin hatsarin kamuwa da cutar HIV, haka nan mata daga cikin su kan iya ɗaukar ciki ba tare da shiri ba wanda wani lokaci kan sanya a zubar da cikin, kuma hakan babbar illa ce.
Haka nan fyaɗe kan yi tasiri ga tunanin yara, inda wasu yakan jefa su a cikin tsanananin damuwa ko ma tunanin kashe kai.