Me ya sa ba a ga Kwankwaso da Abba a 'taron NNPP na ƙasa' ba?

Asalin hoton, Kwankwaso/X
Bisa dukkan alamu rikicin cikin gida na jam'iyyar adawa ta NNPP na ci gaba da kamari, inda a yanzu haka bangarori biyu ke ikirarin iko da jam'iyyar.
Bangaren Kwankwaso wanda ya kafa gwamnati a jihar Kano da kuma zababbun 'yan majalisar dokoki sai kuma bangaren da ke karkashin Agbo Major.
A ranar Laraba 5 ga watan Fabrairun 2025, ne daya bangaren na jam'iyyar NNPP a Najeriya ya gudanar da babban taron inda aka zabi sabbin shugabannin da za su já ragamar jam'iyyar.
A yayin taron an zabi Dr Agbo Major a matsayin sabon shugaban jam'iyyar.
To sai dai kuma a yayin taron ba a ga bangaren Kwankwasiyya ba, hasali ma bangaren Kwankwasiyyar da ke mulkin jihar Kano ya nesanta kansa da babban taron.
Me ya hana Kwankwasiyya halartar taron?
Injiniya Buba Galadima, shi ne sakataren kwamitin amintattu na jam'iyyar, ya shaida wa BBC dalilin da ya sa ba a ga bangaren Kwankwasiyya ba.
"An ce wasu mutane sun taru a Legas sun yi taro har ma sun zabi shugabanni, to wannan abu bai zo mana da mamaki ba, saboda ba jam'iyya ce ta kira taron ba domin ina da hujja, saboda duk wani babban taron jam'iyya da za a yi babu jami'in Hukumar Zabe mai Zaman Kanta wato INEC, ai haramtaccen taro ne."
"Abu na biyu kuma da wacce alama jam'iyyar ta yi amfani? Mu alamar da muka sani ta jam'iyyarmu ta NNPP ita ce littafi da hular digiri a sama da ja jan aiki da kuma fari wato farin ciki da zaman lumana,"in ji Galadima.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Buba Galadima, ya kara da cewa "Su kuwa a nasu taron sun yi amfani da alamar jam'iyya mai kayan marmari, to INEC bata san da zamanta ba."
Sakataren kwamitin amintattu na jam'iyyar, ya yi zargin cewa akwai wasu da ke bayar da kudi domin tunzura bore a jam'iyyar ta NNPP.
To sai dai kuma bangaren da ya shirya taron ya ce babu wata jayayya game da halarcin taron.
Injiniya Muhammad Babayo Abdullahi, shi ne mataimakin shugaban jam'iyyar NNPP na kasa mai kula da shiyyar arewa, ya shaida wa BBC cewa, bangaren su Buba Galadima kame-kame kawai suke.
Ya ce,"Shi shure-shure baya hana mutuwa, mun dade muna fada jam'iyyar NNPP mai kayan marmari bata cikin wata damuwa da kowa sai dai wanda ya sanyawa kansa damuwa."
Injiniya Babayo Abdullahi, ya ce, "Kowa ya sani lokacin da aka yi rijistar wannan jam'iyya da alamar kayan marmari da tuta mai kore da shudi da fari aka yi ta, kuma a cikinta suka zo suka same mu, kuma takardar shaidar rijistar jam'iyya ma wato satifiket ma na hannun wanda ya yi rijistar ta wato Dr Boniface Aniebonam."
Ya ce,"Batun su ce mun yi taro babu jami'in hukumar INEC, duk shaci fadi ne, domin duk mun bi hanyoyin da ya kamata abi idan za a yi taro irin wannan."
Rarrabuwar kai a tsakanin 'ya'yan jam'iyyun siyasa a Najeriya ba bakon abu bane musamman a tsakanin jam'iyyun adawa.
Masu sharhi a Najeriya dai na ganin cewa irin wannan rarrabuwar kai da ake samu a jam'iyyun siyasar zai kara girman aikin da ke gaban jam'iyyun adawar idan suna da gaske suke suna son taka rawar gani a manyan zabukan da ke tafe.










