Matan da aka juyar musu da mahaifa saboda suna da cutar HIV

    • Marubuci, Dorcas Wangira
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa Health Correspondent

An bai wa wasu mata hudu da ke dauke da kwayar cuta mai karya garkuwar jiki da HIV diyyar dala 20,000, saboda juya musu mahaifa da aka yi ba tare da saninsu ba.

Matan sun bayyana wa BBC yadda lamarin ya faru.

Matan - wadanda suka shafe shekara tara suna neman hakkinsu a kotu - an sauya sunayensu domin kare su, wanda ko a lokacin da ake sauraron shari'ar ba a bayyana sunayensu na asali ba.

"Wanna abu ya lalata min rayuwa," kamar yadda Penda ta shaida wa BBC dangane da yadda aka gudanar mata da tiyatar da aka yi mata jim-kadan bayan ta haifi tagwaye a asibitin haihuwa na Pumwani wanda na gwamnati ne da ke birnin Nairobi.

Ana kiran tsarin da kaciyar mahaifa, inda ake yanke juya mahaifar mata ko a daure ta ko ma a yanketa ko ma a cireta, a mayar a dinke domin hana mace daukar ciki a gaba.

Mahaifin 'yan biyun nata ya barta tun kafin ta haifin tagwayen nata. Mijinta ya mutu shekaru da suka gabata sakamkon cutar da ke da alaka da HIV. Damuwa ta sanya ta kuduri aniyar ba za ta sake yin aure ba. ''Waye zai aureni bayan ya san cewa ba zan haihu ba?

Penda ta gano cewa tana dauke da cutar HIV ne a lokacin da samu juna-biyu , don haka ta nemi shawarar likitoci.

A lokacin an bai wa masu juna-biyu shawara da su rika haihuwa ta hanyar yi musu tiyata a ciro dan, sannan kada su shayar da 'ya'yan da suka haifa domin kare yaduwar cutar daga iyayen zuwa 'ya'yan.

Bayan haihuwar Penda, ta ce an gaya mata da ta rika amfani da madara wajen shayar da jariranta.

Ta ce an tabbatar mata da cewa za a ba ta abincin da za ta ci da na jariranta, amma bisa sharadin tabbatar da cewa za ta rugumin tsarin tazarar haihuwa.

"A matsayina na marar miji, wannan abu ya razanani. Dama ina fama da tsangwama. Ban ma san me zan yi ba,'' in ji ta.

Domin taimaka wa Penda ta ci wannan gajiya, likitar abincin asibitin ta tura ta zuwa wani jami'in asibiti wanda ya ce mata ta je wani karamin asibitin da ya kware wajen harkar haihuwa da ke gudanar da shirin tsarin tazarar haihuwa a kasar.

A nan ne aka bai wa Penda wani fom da ta cike, domin a yi mata aikin gimtse mata mahaifa. Ta ce ta saka hannu a kan fom din ba tare da sanin sharudan da ke kan fom din ba.

Aikin dindindin

Ita ma a nata bangare Neema ta bayyana makamancin wannan labari a asibitin Pumwani, wanda shi ne asibitin haihuwa mafi girma a Kenya.

Ta san cewa tana ɗauke da cutar HIV gabanin haihuwarta ta huɗu, inda ta shiga tashin hankali kasancewar tana tsoron shafa wa ɗan da za ta haifa cutar.

Ta ce ɗaya daga cikin jami'an lafiya a wurin sun shaida mata cewa ba za a ba ta man girki da garin masara ba, kuma ba za a biya mata kuɗin asibiti ba idan ba ta yarda an yi mata tiyatar toshe hanyar fitowar ƙwan haihuwa a cikin mahaifa ba.

Ta riga ta san cewa tana ɗauke da cutar HIV a lokacin da take jiran haihuwar ƴarta na huɗu. Ta damu cewa za ta iya yaɗa wa jaririn da ke cikinta cutar.

Ta ce wani kwararre a fannin abinci ya faɗa mata cewa idan ba ta yarda za a yi mata wani nau'in aikin toshe mahaifa bayan haihuwa ba, ba za ta cancanci a ba ta wani kaso na abinci ba, kuma ba za a biya ta kuɗin haihuwa a asibiti ba.

A ranar da za ta haihu kafin a kaita ɗakin tiyata, Neema ta ce ma’aikaciyar jinya da ke aiki ta yi mata nasiha akan buƙatar ta tsara iyali tunda ta haifi ‘ya’ya uku.

Ma’aikaciyar jinya ta faɗa mata ta je a yi mata aikin toshe mahaifa, kuma aka ba ta takarda ta sanya hannu kan amincewa da tiyatar haihuwa.

"Ban san me ake nufi ba, na ɗauka tsarin iyali ne na yau da kullun," in ji Neema kamar yadda ta faɗa wa BBC.

"Da sun bayyana mani tsarin yadda ya kamata, da ban sanya hannu a takardar ba."

Aikin juyar da mahaifar mace

An katse bututun hannun mahaifa

A wajen Furaha, ta tuna babu wata tattaunawa akan tsarin iyali kafin ta haifi ɗanta na uku a Asibitin karɓar haihuwa na Pumwani.

Ta tuna yadda ta yarda a yi mata tiyata don hana ta yaɗa cutar da HIV ga jaririnta - kuma ta tashi cikin tsananin zafi maras jurewa.

Wata ma’aikaciyar jinya ta bayyana cewa an kuma yi mata aikin hana haihuwa.

"Na ji tsoron in gaya wa mijina abin da ya faru, na bar wa kaina komai," kamar yadda ta shaida wa BBC.

"Lokacin da ya gano, sai ya zama mashayi. Ya mutu ne bayan da wata mota ta buge shi, waɗannan ƙungiyoyi sun lalata gidana."

Ita ma wata mata, mai suna Faraja, ta shaida wa BBC cewa ta shiga cikin matsin lamba na yin amfani wani nau'in aikin toshe mahaifa watanni biyu bayan ta haifi ɗanta na uku.

Da yake tana ɗauke da kwayar cutar HIV, an gargaɗe ta kan shayar da jaririn da ta haifa.

Sai dai ba tare da tabbacin cewa tana amfani da tsarin iyali ba - musamman aikin toshe mahaifa - ba ta sami damar samun madarar jarirai kyauta ba.

"Na matsu matuka. Mijina ya tafi. kuɗin gidan haya na ya kusa karewa, me zan iya yi?" Ta tambaya.

Faraja ta shaida wa babbar kotun Kenya cewa ta je wani asibiti inda aka yi mata aikin tiyatar.

An ba ta takarda ta sa hannu, amma ta ce saboda ba ta iya karatu ba, ba ta fahimci abin da ta sa hannu a kai ba.

Babu wanda ya bayyana mata cewa ta amince a yi mata aikin juya mahaifa, kuma ta ce ba a ba ta madadin tsarin iyali ba.

Domin masana kiwon lafiya ba su bayyana karara kan abin da waɗannan matan suka amince da shi ba ne ya sa suka ci nasara a shari’ar tasu.

Hakkoki

Babbar Kotun Kenya ta yanke hukunci a watan Satumba cewa wannan yin amfani da aikin toshe mahaifa ba tare da sanin matan ba, cin zarafinsu ne aka yi, ciki har da 'yancin kafa iyali.

Ƙungiyar agaji ta Marie Stopes International da Asibitin haihuwa na Pumwani da kuma ƙungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF), su za su biya matan diyya.

Babban darektan wata ƙungiya mai suna Kelin Kenya, wadda ke kare hakkin masu cutar HIV, ya ce hukuncin na da matukar muhimmanci ga mata masu ɗauke da cutar a Afirka da kuma suka fuskanci matsin lamba kan a yi musu aikin juya mahaifa.

"Tsawon lokaci, shari'o'in da aka shigar a Afirka ta Kudu, da Namibiya, suna da matsala wajen daidaita alaka tsakanin aikin nau'in hana haihuwa da kuma cutar HIV. Muhimmancin wannan shari'ar shi ne ya sake tabbatar da cewa ba daidai ba ne." ya shaida wa BBC.

Mai magana da yawun ƙungiyar Marie Stopes a Kenya ya shaida wa BBC cewa lamarin ya kasance doguwar wahala ga duk waɗanda abin ya shafa.

"Muna maraba da kudurin bayan kusan shekaru goma. Yarjejeniyar da aka sani koyaushe tana da mahimmanci ga duk abin da muke yi.

"A matsayinmu na mamba na ƙungiyar kare hakkin haihuwa ta duniya, mun fahimci irin tsangwamar da masu ɗauke da cutar HIV ke ci gaba da fuskanta, za mu ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai da kuma sanya ido don tabbatar da cewa an bi ka'idoji mafi girma, kuma ba za mu taɓa yin kasa a gwiwa ba kan kulawar da muke bayarwa."

Ƙungiyar likitoci ta MSF a Faransa ta ci gaba da cewa ba ta taɓa aikin juya mahaifa ba kuma a halin yanzu ba ta irin wannan aiki a Kenya.

Ya ce idan mace ta zaɓi yin aikin nau'in hana haihuwa, aikinsa shi ne bayar da shawara, sanarwa da kuma tura su zuwa wurare.

"Mun amince da wani ɓangare na alhakin abin da ya faru da matan da kuma mayar da su a matsayin mu na ƙungiyar kiwon lafiya," kamar yadda Dr Hajir Elyas, ko'dinetan ayyukan MSF a Kenya, ya shaida wa BBC.

Asibitin karɓar haihuwa na lardin Pumwani bai ce uffan ba lokacin da BBC ta buƙaci ji daga garesa.

Babu sahihin bayanai game da adadin mata masu ɗauke da cutar HIV a Kenya da aka yi wa aikin juya mahaifa ba tare da yardarsu ba.

Sai dai, wani bincike na shekara ta 2012 da ƙungiyar African Gender and Media Initiative - ta gudanar - ta ɗauki bayanan mata 40 da aka tilasta musu juya mahaifa.

Daga cikin waɗannan mata, biyar ne kawai suka yi nasarar shigar da ƙara.

Mista Maleche ya ce matan sun zaɓi shigar da kararrakin tsarin mulki ne, saboda irin wannan ƙara na da tasiri sosai.

"Aikata babban laifi zai kai ga ɗaurin zama gidan kurkuku, biyan tara, babu wani alfanu ta fannin kuɗi da matan za su samu," in ji shi.

Sai dai matan sun ce lamarin nasu ba wai don biyan diyya kawai ba ne. Sun ce hukuncin da babbar kotun ta yanke ya tabbatar da buƙatarsu ta yin adalci.

Lauyansu, Nyokabi Njogu, ya yarda cewa: “Ta yaya za ku biya diyya kan cin zarafin da ya ta'azzara?

"Sun so kawai a yarda cewa hakan ya faru. Ba sa son matan da suka sha wahala irinsu su ci gaba da wannan wahala."