'Ya yi min fyaɗe saboda ni zabaya ce, wai domin neman kariya'

Regina mary Nlodvu ta ce wani mutum wanda ta amince wa ne ya ci zarafinta a karon farko a lokacin da take wasa a cikin lambu.

"Ya bani alawa ne sai ya umarce ni da in zauna bisa ƙafarsa, a lokacin da na zauna sai ya cire mani kaya ya ci zarafina."

Regina ta ce wannan shi ne lokaci na farko da aka ci zarafinta a lokacin tana da shekara takwas a duniya. Sai dai ta ce ba shi ne karo na karshe da aka yi mata fyade ba, inda ta ce mutumin ya sake komawa gidansu da ke garin Ennerdale a Afirka ta Kudu, da sunan zai gaishe da iyayenta amman ya je ne domin ya yi lalata da ita, kuma ya kwashe shekaru yana cin zarafinta.

Ta shaida wa BBC cewa ba shi kadai ba ne mutumin da ya yi mata fyade, Regina ta ce ta kwashe shekaru tana fuskantar cin zarfi daga mutane da dama.

Matar ƴar shekara 34 ta ce an riƙa cin zarafin ta ne saboda an haife ta da lalurar zabaya, kuma ta ce sun yi hakan ne saboda sun yi amanna da camfin da ke cewa idan suka yi lalata da ita babu su babu kamuwa da rashin lafiya.

Camfi mai hadari da ta ce yana addabar zabaya.

Bayan kwashe shekaru tana fama da cutar damuwa, Regina ta zama jarumar fina-finai a Afirka ta Kudu, kuma tana kokarin wayar da kan mutane kan zabaya.

Duk da ta koyi yadda ake karatu ne da rubuta shekaru goma da suka gabata a lokacin da take yar shekara 24, amman tana rubutu kan zabaya musamman kan rayuwarta.

Regina wadda uwa ce tana fafutukar ganin wadanda suka kasance zabaya ba su fuskanci abin da ta fuskanta ba.

Wasu sun yi amannar cewa gashin zabaya na kawo arziƙi, wasu kuma sun yarda cewa saduwa da zabaya na maganin cututtuka da suka hada da HIV da korona.

Ana sacewa da kashe zabaya saboda camfe-camfen da ake yi cewa sassan jikinsu na da wani sirri.

"Zan iya tunawa cewa lokacin da nake yar shekara biyar yara kan yi dandazo kofar gidanmu kullum, ina tunanin sun zo mu yi wasa ne amman da na nufe su sai su tsere," in ji Regina.

A tunanin Regina, duk hakan wani ɓangare ne na wasan, har sai ranar da wata mata ta je gidansu da ɗiyarta "Yarinyar ta kalle ni sai ta fashe da kuka inda ta ce wai ta ɗauka ni dodo ce, abin ya yi mani ciwo."

Regina ta gano cewa abokan karatunta na tofa yawu cikin rigarsu idan sun gan ta.

Wanda daga baya ta gane cewa suna yin hakan ne saboda neman tsari daga haihuwar zabaya.

Regina ta kuma sha wahala saboda lalurar ido, inda ganinta ke raguwa- lalurar da yawancin zabaya ke fama da ita,ba ta iya ganin allon rubutu sai idan tana kusa da shi, kuma da ta yi ƙorafi sai aka ce mata babu wani tanadi da za a yi mata.

Regina ta bar makaranta ne saboda ba ta iya rubutu da karatu, hakan na nufi ta kasa samun aikin yi, amman a 2013 ta samo littafin Bible na murya wanda ya sauya rayuwarta.

"Idan na ga littafi ina shiga wani yanayi na damuwa, " amman sai na fara sauraren litattafai na murya, wadanda suka sauya rayuwata"

An sanya ta cikin masana'antar fim ƙarƙashin Young African Leaders Initiative, ta samu damar rubutawa da gabatar da littafinta na wasan kwaikwaiyo mai taken “Mary, My voice.”

"A lokacin da nake ƙarama babu zabaya a harkar fim, ina son in kawo sauyi kan hakan."

A cikin masu son wasan kwaikwayon ta ne wani ya biya mata kudin koyon karatu da rubutu, "har yanzu ina fama da karancin iya rubutu da karatu, sai dai ba kamar a baya ba."

Regina ta ce tana fatan a nan gaba za ta iya taimaka wa yarinyarta da aikin gida da ake ba su daga makaranta, koda yake ba ta dade da haihuwa ba.

"Kalle ta mai kyau da ita" ta bayyana haka ne a lokacin da take ƙoƙarin daukar yarinyarta mai suna Bohlale Sabelo Isabel.

Bohlale ba zabaya ba ce amman mamanta ta ce "Inda ta zo a zabaya zan yi farin ciki, saboda wani abu ne da na koyawa kaina son shi, ita ce dukkan rayuwata kuma ina fatan ba ta duk wani jin dadi da damarmakin rayuwa da ban taba samu."