Abin da muka sani kan kiki-kaka tsakanin Dangote da NUPENG

Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Litinin 8 ga watan Satumbar 2025, ne kungiyar ƙwadago ta ma'aikatan dakon man fetur da iskar gas a Najeriya, NUPENG, ta yi barazanar tsunduma yajin aiki domin adawa da matakin da matatar mai ta Ɗangote ta dauka na fara kai man fetur zuwa gidajen mai da ke fadin ƙasar.

Bayanai na nuna cewa a yanzu haka ministan ƙwadago na Najeriya na can na ganawa da ƴan ƙungiyar ta NUPENG da kuma ɓangaren matatar Ɗangote domin warware wannan kiki-kaka.

Har yanzu kamfanin matatar Ɗangote bai ce komai ba dangane da rikicin.

Ga wasu abubuwa da muka sani dangane da wannan rikici.

Ɗangote na son raba mu da aikinmu - NUPENG

Ƙungiyar ta NUPENG, ta zargi matatar Dangote da karya dokokin ƙwadago inda ta ce yana neman raba direbobin da ke dakon mai da aikinsu.

Kungiyar ta NUPENG, ta ce muddin matatar mai ta Dangote ta fara jigilar mai zuwa gidajen man da ke jihohi, to dubban ma'aikatan da ke aiki a depo-depo da kuma direbobin da ke tuka manyan motoci sama da dubu 30, za su rasa aikinsu.

Kwamared Lawan Garba, shi ne mataimakin shugaban kungiyar direbobin tankar mai ta PTD, daya daga cikin kungiyoyin kwadago da ke NUPENG, ya shaida wa BBC cewa, a doka babu wani mai kamfani kamar na Dangote, wanda ke depo da gidan mai sannan a sayi kaya ya kuma dauka ya kai, sam doka bata bayar da wannan dam aba.

Ya ce," Dalili shi n esu masu dakon mai idan hakan ta kasance za su zamanto basu da aikin yi ke nan, sannan mutanen da za su rasa aiki suna da dama tun da akalla yanzu muna da tankuna sama da dubu 30 da ke zirga-zirga, to idan aka ce a yau tankuna sun tsaya to ai masu tuka su ma aiki ya tsaya musu."

Muna goyon bayan NUPENG - NUGASA

Ita ma kungiyar masu gidajen mai da isakar gasa NOGASA, ta nuna goyon bayanta a kan matakin da NUPENG din ta ce zata dauka na shiga yajin aiki.

Abdullahi Idris, shi ne mataimakin shugaban kungiyar NOGASA a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa su ma basu yar da da wannan tsari na Dangote ba, saboda muna tare da NUPENG.

Ya ce," Idan har Dangote zai rika kai mai gidajen mai da motocinsa, to mu me zamu yi ke nan? Ta karfi an fitar da mu a cikin sana'ar da muka dade muna bauta a kanta."

Ra'ayin IPMAN

A bangare guda, kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya IPMAN, kira ta yi ga dukkan bangarorin biyu da su kai zuciya nesa.

Alhaji Abubakar Mai Gandi Shettima, shi ne shugaban IPMAN a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa su son kungiyar NUPENG da PTD da NARTO, da su kai zuciya nesa.

Ya ce," Ya kamata wadannan kungiyoyi su zauna da Dangote domin a sasanta domin mu ba ma son duk wani abu da zai jefa talaka cikin wahala, don haka yanzu su zo mu hada kai da Dangote a warware wannan matsala."

Tuni dai gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi kira ga kungiyar NUPENG da ta dakatar da shiga yajin aikin da ta ke shirin farawa.

Muna da isasshen man fetur - AROGMA

Ƙungiyar masu gidajen mai da iskar gas ta arewacin Najeriya wato AROGMA ta ce tana maraba da matakin da matatar Ɗangote ta ɗauka na yin dakon mai zuwa gidajen man a faɗin ƙasar.

Shugaban ƙungiyar, Bashir Ɗanmalam ya shaida wa BBC cewa "duk zalunci yana da ƙarshe domin komai nisan jifa ƙasa zai faɗo saboda NUPENG sun saba saka wa mutane kuɗi tsububu inda kuma dole ne mu fanshe su a kan mai sayen mai wato talaka kenan."

Bashir Ɗanmalam ya ƙara da cewa ba za su yi yajin aiki ba domin su abin da suka daɗe suna jira kenan.

"Mu masu gidan mai mun riga mun zauna a tsakaninmu kuma mun yanke cewa ba bu yajin aikin da za mu tafi saboda mu muna tare da al'umma."

Daga ƙarshe ya kuma bai wa ƴan Najeriya tabbacin wadata ƴan ƙasar da isasshen mai.

"A yanzu haka muna da man da ko ba a yi dakonsa ba daga defo to zai kai mu wata ɗaya ko fiye da haka duk kuwa da cewa an koma makaranta saboda zirga-zirgar ƴan makaranta."