Ko PSG za ta fitar da Barcelona a Champions League?

Barcelona za ta karbi bakuncin Paris St Germain a wasa na biyu a Champions League zagayen quarter final a Spaniya ranar Talata.

Kungiyar da Xavi ke jan ragama na cike da farinciki da wannan matakin da ta kai bayan shekara biyu, wadda ake fitar da ita a karawar cikin rukuni.

A kakar bana Barcelona na fuskantar kalubale, amma hakan bai hanata kai wa zagayen quarter final ba a gasar zakarun Turai, tana ta biyu a La Liga.

Mai Champions League biyar na fatan doke PSG, domin ta kai daf da karshe, idan da hali ta kai zagayen karshe a kakar nan.

A makon da ya gabata Barcelona ta je ta ci PSG 3-2 a Faransa, kuma wasa na 15 da za su fuskanci juna, bayan da kungiyar Spaniya ta ci shida da canjaras hudu.

Barcelona na bukatar sa kaimi a karawar da za a yi a Estadi Olímpic, domin kociyan PSG, Luis Enrique tsohon dan wasan Barca ne ya kuma horar da ita, kenan zai je da dabarun da zai yi nasara.

Wasan zai ja hankalin 'yan kallo tunda yanzu an soke dokar amfana da cin kwallo a waje, kenan guda daya ce a tsakaninsu, inda komai zai iya faruwa.

Kylian Mbappe zai so ya kai wasan karshe a Champions League idan da hali ya dauki kofin da ya rage ya daga a tarihin tamaularsa, wanda zai koma Real Madrid a karshen kakar bana.

Barcelona na fatan kai wa daf da karshe a Champions League karo na 13, amma na farko tun bayan 2018 - tana kuma sa ran fuskantar wadda za ta yi nasara tsakanin Atletico Madrid ko Borussia Dortmund, idan ta yi nasara a kan PSG.

Za a buga wasan karshe a Champions League a Wembley cikin watan Mayu.

Ranar Laraba Barcelona ta je ta doke PSG 3-2, kenan wasa biyu kungiyar Camp Nou ta yi rashin nasara daga tara baya da suka fafata.

Haka kuma Barcelona na fatan doke PSG gida da waje a gasar zakarun Turai karo na biyu, kamar yadda ta yi a 2014/15.

Paris St Germain ba ta taba lashe Champions League, wadda har yanzu ba ta shiga gurbin manyan kungiyoyin Turai ba.

'Yan wasan Barcelona:

Ter Stegen, ⁠João Cancelo, R. Araujo, I. Martinez, Ferran, Pedri, Lewandowski, Raphinha, Iñaki Peña, João Félix, Marcos A., Romeu, Vitor Roque, F. De Jong, Gündoğan, Kounde, Astralaga, Lamine Yamal, M. Casadó, Fermín, Cubarsí, Marc Guiu da kuma H. Fort