Waɗanne Larabawa ne suka ci lambar yabo ta Nobel a tarihi?

Lokacin karatu: Minti 7

Tsawon sama da karni daya tun lokacin da aka bullo da bayar da lambar yabo ta Nobel a 1901, Larabawa kadan ne suka ci lambar, to amma fa aduk lokacin da wani Balarabe ya samu lambar za a ga cewa ya yi fice sosai kuma ya cancanta matuka gaya.

Irin bajintar da suke da ita a fannin kimiyya da adabi da sakonnin siyasa, Larabawan da suka ci wannan lamba ta yabo suna nuna wa duniya irin kokari da bajinta da fasaha da Larabawa suke da.

Duk wanda ya ci wannan lamba ta yabo a tsakanin Larabawa, walau jagoran siyasa ne da ke neman tabbatar da zaman lafiya ko marubuci ne yake bayyana wani abu na rayuwar dan'Adam ko masanin kimiyya ne da ya gano wani ilimi, za ka ga abin da ya kai shi ga samun wannan lamba ya yi tasiri a duniya.

Wadanda suka ci lambar

Peter Meador (1960): Likitanci (Dan Birtaniya asalin Lebanon)

Peter Brian Meador na daya daga cikin masana kimiyya da suka kawo sauyi a yadda ake aikin likitanci a zamanin nan ta fannin dasa wani sashe na jikin mutum.

Meador wanda dan Lebanon ne amma kuma mahaifiyarsa 'yar Birtaniya ce ya mayar da hankali a rayuwarsa kan binciken yadda jikin mutum ke alaka da wata bakuwar tsoka da aka saka masa, abin da ya kai shi ga gano yadda za a iya dasa wa mutum wani sashe na jikinsa da ya mutu ko ya lalace.

Wannan ilimi da ya gano ya taimaka wajen ceto rayuwar miliyoyin mutane a duniya.

An bai wa Meador wannan lamba ne a 1960 tare da Sir Frank Macfarlane Burnet, a kan bincikensu a fannin garkuwar jikin mutum.

Anwar Sadat (1978): Zaman lafiya (Masar)

Anwar Sadat ya kafa tarihi a matsayin wani shugaba na kasar Larabawa da ya nemi zaman lafiya da Isra'ila bayan rikici na gomman shekaru.

Sakamakon yakin watan Oktoba na 1973, Sadat ya tashi takanas ya je Birnin Kudus inda ya gabatar da jawabi a majalisar dokokin Isra'ila a wani mataki da ba a taba ganin irinsa ba.

Wannan abu da ya yi ya haifar da rarrabuwar kai, amma shi ya kai ga sanya hannu a yarjejeniyar Camp David a 1978 a karkashin jagorancin shugaban Amurka na lokacin Jimmy Carter.

A bai wa Shugaba Sadat lambar ta zaman lafiya ta Nobel tare da Firaministan Isra'ila na lokacin Menachem Begin saboda karfin halinsa na neman tabbatar da zaman lafiya.

Duk da cewa kisansa da aka yi a 1981 ya kawo karshen siyasarsa, to amma tarihinsa ya kasance abin da ake ce-ce-ku-ce a kansa a wani bangaren kuma abin da ake yabawa, kasancewar ana daukansa a matsayin daya daga cikin shugabannin Larabawa mafiya tasiri a rikicin Isra'ila da Larabawa.

Naguib Mahfouz (1988): Adabi (Masar)

Naguib Mahfouz ya ci wannan lamba ne ta zaman lafiya ta Nobel a fannin adabi a 1988, inda ya zama marubuci na farko daga wata kasar Larabawa da ya ci wannan lamba.

Mahfouz ya yi fice a matsayin jigo ko uba a fannin rubutun zube na Larabawa na zamani, inda ya rika bayyana wa duniya yanayin rayuwar Masar ga duniya, ta hanyar iya sarrafa harshe da rubutu.

Littattafansa irin su "The Trilogy" da "Children of Gebelawi," ba labarai ba ne kawai, - domin sun kasance tamkar wasu hotuna ne da ke magana a kan rayuwa da adalci da kuma kaddara.

Nasarar samun wannan lamba da ya yi ta sa duniya nazari da sanin adabin Larabawa, har adabin ya samu gindin zama a duniya.

Elias James Corey (1990): Kemistiri (Ba'amurke asalin Lebanon)

Elias James Corey ya ci wannan lamba ne a 1990 a fannin kimiyya (Chemistry) ta yadda ya bayar da gudummawa wajen gano yadda masana kimiyya za su iya hada sinadarai masu sarkakiya cikin tsanaki, wanda ba a taba samun hakan ba a baya.

An haifi Corey a jihar Massachusetts ta Amurka - iyayensa sun kasance 'yan Lebanon.

Ana daukansa a matsayin daya daga cikin masana kimiyya da suka yi tasiri sosai a duniya, kuma har zuwa yau dalibansa na yada ilimin da ya gano.

Yasser Arafat (1994): Zaman lafiya (Falasdinu)

Yasser Arafat ya kasance wata alama ta gwagwarmayar Falasdinwa kuma daya daga cikin jigon siyasa mai wuyar sha'ani na karni na 20.

An ba shi lambar Nobel ta zaman lafiya a 1994 tare da Isra'ila Yitzhak Rabin da Shimon Peres bayan sanya hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya ta Oslo wadda ta tanadi sasanta rikicin Falasdinu da Isra'ila cikin kwanciyar hankali.

Duk da cewa yarjejeniyar ba ta kai ga cikar burin kafa kasar Falasdinu ba , to amma ba shi lambar, nuni ne ga irin rawar da ya taka wajen matsar da rikicin daga fagen-daga zuwa teburin tattaunawa.

Ahmed Zewail (1999): Kimiyya (Ba'amurke asalin Masar)

Ahmed Zewail ya kafa tarihi a fannin kimiyya inda ya kirkiro hanyar da masana kimiyya za su iya nazarin haduwar sinadarai cikin dan kankanin lokaci - kamar walkiya.

Wannan bajinta ta kawo sauyi kan yadda a baya ake daukar yadda sinadarai ke haduwa, wanda hakan ya sa aka ba shi lambar yabon a fannin kimiyya a 1999.

An haife shi a Damanhour, da ke Masar, kuma ya kasance wani tauraro na kasar Larabawa a kasashen Yamma.

Mohamed ElBaradei (2005): Zaman lafiya (Masar)

Mohamed ElBaradei na samu lambar ne a 2005 a kan irin kokarin da ya yi na hana bazuwar makaman nukiliya tare da ganin ana amfani da nukiliya a fannin zaman lafiya a lokacin da ya shugabanci hukumar kula da nukiliya ta duniya IAEA.

ElBaradei ya yi fice kan yadda yake amfani da diflomasiyya da kuma tsayawa kan gaskiya ko da kuwa ba ta yi wa manyan kasashe dadi ba.

ElBaradei ya kasance wata alama ta son zaman lafiya da adalci ta kasashen Larabawa kuma har yanzu muryarsa na tasiri a kan manyan al'amura na duniya.

Tawakkol Karman (2011): Zaman lafiya (Yemen)

Tawakkol Karman ta yi fice aka san ta a lokacin juyin-juya-hali na kasashen Larabawa a Yemen, a matsayin mace da ta jagoranci gwagwarmayar zaman lafiya wajen tabbatar da dumukuradiyya da adalci.

An ba ta lambar Nobel a 2011, tare da Ellen Johnson Sirleaf da Leymah Gbowee of na Liberia, inda ta kasance mace ta farko daga kasashen Larabawa da samu lambar.

Ana daukan Tawakkol a matsayin uwar juyin-juya-halin Yemen, kuma ta yi fice wajen yaki na mulkin danniya da fafutukar 'yancin mata da 'yancin 'yan jarida.

Kungiyoyi hudu da suka jagoranci tattaunawar zaman lafiya a Tunisia (2015): Zaman lafiya (Tunisia)

Wadanda aka bai wa lambar yabo ta Nobel - kungiyoyi hudu na masu raji da suka jagoranci tattaunawar sasanta dambarwar siyasar Tunisia: Shugaban kungiyar masu masana'antu na Tunisia, Widad Bouchamaoui (a tsakiya), Shugaban kungiyar alkalai ta Tunisia, Abdel Sattar Ben Moussa (a hagu), Shugaban kungiyar lauyoyi ta Tunisia, Fadhel Mahfoudh (a dama), da kuma Babban Sakataren kungiyar kwadago ta Tunisia, Houcine El Abassi (na uku daga dama).

An bai wa hadakar wadannan kungiyoyi hudu lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel a 2015 saboda rawar da suka taka daga kare kasar Tunisia fadawa rikici, bayan juyin-juya-halin da aka yi a 2011, inda suka shiga gaba wajen tattaunawar da ta kai ga mayar da kasar kan tsarin dumukuradiyya.

Abdulrazak Gurnah (2021): Adabi (Dan Tanzania asalin Yemen)

Marubuci Abdulrazak Gurnah ya samu lambar Nobel ne a fannnin adabi a 2021 a kan rubuce-rubucen da ya yi a kan tarihin mulkin mallaka da kuma kan rayuwar 'yan gudun hijira da 'yan ci-rani.

Littattafansa sun hada da : Paradise da Life After Death.

Gurnah wanda aka haifa a Zanzibar ta Tanzania, amma kuma iyayensa 'yan Yemen ne, ya koma Birtaniya lokacin yana matashi, inda ya zama daya daga cikin fitattun marubuta a duniya.

Mongi Baoudi (2023): Kimiyya (Bafaranshen Amurka asalin Tunisia)

Masanin kimiyya Mongi Baouendi ya ci lambar ne a 2023 a fannin kimiyya (Chemistry) a kan irin gudummawar da ya bayar wajen samar da ilimin da ya kawo sauyi a fanni biyu : fasahar nuna abu da haskakawa da wuta da kuma bangaren aikin likita.

Al-Bawundi ya kasance daya daga cikin fitattun masana kimiyya kuma farfesa ne a fitacciyar Jami'ar fasaha ta Amurka : Massachusetts Institute of Technology.

An haife shi ne a Paris kuma iyayensa 'yan Tunisia ne.

Omar Yaghi (2025): Kimiyya (Ba'amurke, dan Saudiyya asalin Falasdinu da Jordan)

Omar Yaghi shi ne wani Balarabe wanda ya samu wannan lamba ta yabo ta Nobel a baya-bayan nan.

Bincikensa ya kawo gagarumin sauyi a kan kayayyaki (materials) da kimiyyar makamashi.

Ya ci kyautuka da dama na duniya, kuma yana daya daga cikin masana kimiyya da a yau ake ambatawa a duniya.

An haifi Yaghi a Jordan, kuma ya yi karatunsa ne a Jami'ar Amurka (American University) da ke Beirut, kafin ya koma Amurka, inda ya jagoranci wani sabon bincike kan yadda ake amfani da wadannan abubuwa ko kayayyaki wajen adana ruwa da makamashi.