Yadda Juma Bah ya taso daga tallan burodi zuwa taka wa Man City leda

    • Marubuci, Mohammed Fajah Barrie
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Marubucin Wasanni, Sierra Leone
  • Lokacin karatu: Minti 2

Juma Bah ya saba taya taimaka wa mahaifinsa wajen gasawa da tallan burodi a Saliyo (Sierra Leone), amma yanzu nan gaba kaɗan zai fara taka wa mai horarwa Pep Guardiola leda a Manchester City.

Wata tara da suka wuce kacal, matashin ɗanwasan na taka leda ne a ƙasarsu da ke Afirka ta Yamma, bayan ya taso yana murza leda a kan turɓaya.

Bayan nuna kansa a wasannin La Liga a ƙungiyar Real Valladolid a kakar bana, ɗanwasan bayan ya ƙulla yarjejeniya da Man City a watan Janairu.

"Burina zai cika idan na taka leda da waɗannan ƙwararrun 'yanwasan na Manchester City," kamar yadda Bah ya faɗa wa BBC Sport Africa.

"Ina yawan buga wasa da su a wasan game na PlayStation. Taka leda tare da su a gaske zai yi min daɗi sosai.

"Ina da burin na koyi abubuwa a can kuma na samu koci mafi ƙwarewa a duniya. Babban burina shi ne na lashe kofuna."

Bah zai cika shekara 19 da haihuwa a watan Afrilu mai zuwa.

Sai dai City ta miƙa shi aro ga Lens bayan ta ɗauke shi, inda ya koma buga gasar Ligue 1 ta Faransa.

Sabon kocin Sierra Leone, Mohamed Kallon, ya yabi ɗanwasan a matsayin "tauraruwa mai tasowa".

"Na san wani babban al'amari na shirin faruwa, kuma yana jiran damarsa ne kawai," in ji Kallon.

"Zai iya yin nasara a Turai. Man City ta saye shi ne saboda ta ga wani abu a tare da shi. Muna sane cewa yana da hazaƙar da za ta bunƙasa nan gaba."

Tasowar Juma Bah

Bah ya girma a unguwar Congo Market da ke Freetown babban birnin Saliyo.

Har bayan ya fara zama ƙwararren ɗanwasa yakan kai wa mahaifinsa Abdul Karim itace a gidan burodi, kuma ya taya mahaifiyarsa Umu aiki kafin ya tafi atasaye.

"Nakan ɗauki itace da ƙarfe 4:00 na dare saboda mahaifina kan fara aiki da sassafe," in ji Bah.

"Zan iya cewa burodinsa ya fi na kowa daɗi a duniya. Na sha rarraba wa masu shaguna burodin. Mahaifiyata na sayar da mandaƙon kaza. Nakan je na taimaka mata da niƙa naman. Ina jin daɗin taimakawa iyayena."

Bah ya fara wasa kamar akasarin yaran Afirka ba tare da takalmi ba, inda daga baya ya koma kulob ɗin AIK Freetong mai buga gasa mai daraja ta uku daga ƙungiyar matasa ta Giant Academy a watan Afrilun 2021.

Tun kafin ya cika shekara 16 ne kuma ya fara taka leda a babbar gasar tamaula ta Sierra Leone Premier League.