Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Faransa za ta amince da kafuwar ƙasar Falasɗinu - Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce kasarsa a hukumance za ta dauki Falasdinu a matsayin kasa, wanda hakan kenan zai sa Faransa ta zama wata babbar kasa a Yammacin duniya kuma ta farko a kungiyar G7 da ta yi hakan.
A wani sako da ya sanya a shafinsa na X, Macron ya ce, Faransa za ta yi wannan sanarwa ne a hukumance a lokacin babban taron Majalisar Dinkin Duniya, a New York, a watan Satumba.
Wannan mataki na Shugaba Macron da ke zaman irinsa na farko daga wata babbar kasa a Yammacin duniya, ko ba komai ana ganin wani karfin hali ne da hobbasa da zai karfafa wa masu irin wannan ra'ayin gwiwa.
A sakon da ya sanya a shafin nasa na X, ya kara da cewa babban abin da ake bukata a yanzu shi ne kawo karshen yakin Gaza da kuma ceton al'umma - fararen hula.
Ya ce lalle za a iya cimma zaman lafiya. ''Muna bukatar dakatar da bude wuta nan take, da sakin dukkanin wadanda aka yi garkuwa da su, da kuma gagarumin aikin jin-kai ga al'ummar Gaza.''
Jami'an Falasadinawa sun yi maraba da matsayin na Shugaba Macron, yayin da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce matakin – saka wa ta'addanci ne – bayan harin da Hamas ta kai na ranar 7 ga watan Oktoba, 2023 a kan Isra'ila.
A sakon na X da ya sanya ranar Alhamis, Macron ya rubuta cewa : ''Kamar yadda aka san kudurinta a tarihi na tabbatar da adalci da zamana lafiya mai dorewa a Gabas ta Tsakiya, na yanke shawarar cewa Faransa za ta amince da kasar Falasdinu.
''Haka kuma dole mu tabbatar da kwance damarar Hamas ta soji, tare da ceto, da kuma sake gina Gaza.
''A karshe dole mu gina kasar Falasdinu, mu tabbatar da wanzuwarta, tare da tabbatar da raba ta da makamai da kuma yarda kada'na da kasar Isra'ila, tare da tabbatar da tsaron dukkanin yankin Gabas ta Tsakiya. Babu wani zabi bayan wannan.''
Bugu da kari Mista Macron ya aika da wasika ga shugan hukumar Falasdinawa Mahmoud Abbas, yana tabbatar masa da wannan mataki nasa.
Da yake magana a kan sanarwar ta Shugaba Macron, mataimakin shugaban hukumar Falasdinawan - Hussein al-Sheikh, ya ce wannan matsayi na nuni da kudurin Faransa na martaba dokokin duniya.
Tare da goyon bayanta ga al'ummar Falasdinu wajen samun 'yancin kai da kafa kasarsu da kansu,'' kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Faransar - AFP, ya ruwaito.
Shi kuwa a martaninsa a shafin X, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu cewa ya yi : ''Mun yi Allah-wadarai da matakin Shugaba Macron na amincewa da kasar Falasdinu a kusa da Tel Aviv – a yayin kisan kiyashin 7 ga watan Oktoba.
''Samar da kasar Falasdinu a wannan yanayi zai kasance tamkar dan-ba aka sa na share Isra'ila – ba ta zauna cikin kwanciyar hankali a kusa da ita ba.
A sani fa cewa: Falasdinawa ba wai suna son kasarsu ta kasance kusa da Isra'ila ba ne. Su fa kasarsu suke so maimakon Isra'ila,'' in ji Netanyahu.
Ita ma Amurka babbar kawa kuma mai taimaka wa Isra'ila ta soki sanarwar ta Shugaba Macron.
A wani sako da ya sanya a shafin sada zumunta Sakataren harkokin Waje na Amurka, Marco Rubio, ya bayyana matakin da ganganci wanda Hamas za ta ci moriya.
To amma kuma Saudiyya ta yaba wa shugaban na Faransa inda ta bayyana sanarwar ta sa da ta tarihi.
Ita ma hukumar Falasdinwa ta yi maraba da sanarwar.
A yanzu dai kasashe sama da 140 ne daga cikin 193 da ke Majalisar Dinkin Duniya suka amince da kasar Falasdinu.
Kadan daga cikin kasashen Turai da suka hada da Sifaniya ne suka amince da Falasdinu.
Amma babbar kawa kuma mai tallafa wa Isra'ila – Amurka da kawayenta ciki har da Birtaniya ba su yarda da wanzuwar kasar Falasdinu ba.
Tun bayan da Hamas ta kai wa Isra'ila harin ba-zata a kudanci ranar 7 ga watan Oktoba na 2023, inda ta kashe akalla mutum 1,200 ta kuma yi garkuwa da 251.
Isra'ila ta kaddamar da yaki a Gaza inda zuwa yanzu ta kashe akalla Falasdinawa 59,106, kamar yadda hukumar lafiya ta Gaza ta bayyana.
Yanzu dai kusan gaba dayan yankin Gaza Isra'ila ta mayar da shi buraguzai.
A ranar Alhamis hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce yaro daya a cikin biyar a Gaza na fama da cutar tamowa, kuma abin kullum kara kamari yake.
Wannan kuwa ya kasance ne saboda takaita shigar da kayan agaji zirin da Isra'ila ta yi.