Kiristocin Gaza na cikin fargaba sanadin rikicin Isra'ila

Gaza
Bayanan hoto, Wani harin Isra'ila da ya faɗa kan ginin Cocin Girka a Gaza ya kashe Falasɗinawa Kiristoci 18
    • Marubuci, Daga Yolande Knell
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Jerusalem

A tsawon watan da ya gabata da aka shafe ana kazamin faɗa, kowace rana Fafaroma Francis na yin kira ga limaman coci a Gaza da su riƙa duba mutane a cocin iyalai da ke cikin Gaza.

Ya yi ta yin addu'o'i da kuma nuna jimaminsa.

Ga George Anton, wanda ke zaman mafaka a harabar cocin tare da matarsa da ƴaƴansa uku, ya ce wurin yana da daɗin zama, sai dai babu wani tabbaci na smaun kariya.

"Mun yarda da Fafaroma Francis, sai dai ba mu yarda wasu su ji muryar zaman lafiya ba," in ji shi. "Ban san yadda zan kwatanta abin da muke ji ba. Abu ne mai matukar ban tsoro. Za ka ji kamar kana zaune kana jiran lokacin mutuwarka. Ba ka san yaushe ne ba kuma ba kan ta wace hanya ba ko kuma me ya sa."

George, wanda ke aiki da ƙungiyar ba da agaji na cocin Roman Catholic Caritas, ya faɗa min cewa yayi tattaunawa mai ban wahala da ƴaƴansa mata ƴan shekara takwas, goma, da kuma 12.

"Ina faɗa musu gaskiya. Na ce muna tare da Yesu, sai dai na kuma faɗa musu cewa suna cikin yaƙi," in ji George. "Wasu lokuta, ina barinsu domin fita na samu biredi, da magani, da tufafi, kuma duk lokacin da na zo fita ina sallama da su. Idan na dawo to, idan kuma ban dawo ba, shikenan."

Ya ce ba abu ne mai kyau ba ci gaba da ajiye ƴaƴansa mata daga mugun ganin mace-mace da kuma ruguza gine-gine.

"Wannan shi suke ji daga wajen mutum 600 da ke kusa da su a cocin, waɗanda ke kallon bidiyoyi a shafin intanet. Wannan shi suke ji daga lugudan bama-bamai a ko'ina. Ba sa yin barci da dare, suna cikin firgici. Ƙarar saukar makaman roka ya zama tamkar bala'i."

…

Asalin hoton, VATICAN NEWS

Bayanan hoto, Wata malamar coci da fasto a Gaza sun tattauna da Fafaroma daga Cocin Iyalai da ke birnin Gaza
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Lokacin da sojojin Isra'ila suka bai wa mazauna arewacin Zirin Gaza sama da miliyan ɗaya umarnin ficewa zuwa kudanci, dubun-dubata ba su bi umarnin ba.

Mutane da yawa daga al'ummomin Kirista tsiraru, waɗanda ba su fi 1,000 ba, maimakon su fice, sai suka ɗauki iyalansu zuwa cikin majami'u, da tunanin cewa za su tsira, kamar yadda yake a faɗa tsakanin Isra'ila da ƙungiyoyi masu gwagwarmaya da makamai na Falasɗinawa a baya.

Bayan wani kazamin hari ta sama da ya ruguza ginin wani Cocin Girka na gargajiya mai suna Greek Orthodox Church - wanda yake wurin wani tsoffin majami'u na duniya - an rasa dukkan tsaro.

Wata Cocin Girka da ke birnin Jerusalem ya kwatanta harin a matsayin "aikata laifukan yaƙi".

Sojojin Isra'ila sun ce sun hari wata cibiyar Hamas ne da makaman roka wanda ke kusa ba wai cocin ba.

A cikin al'amuran da ke nuna ɓacin rai, an jera gawawwakin waɗanda aka kashe su a cikin fararen kyalle a harabar cocin domin yi musu jana'iza a ranar 20 ga Oktoba. An kashe mata Kiristoci 18, maza da kuma yara.

A Yammacin Gaɓar Kogin Jordan da aka mamaye, majami'u sun gudanar da addu'o'i na musamman don nuna goyon baya ga duk waɗanda ke shan wahala a Gaza tare da tunawa da waɗanda suka mutu.

Yawancin Kiristocin Gaza suna da dangi a nan, ko da yake tsarin ba da izini na Isra'ila ya yi musu wahala a cikin 'yan shekarun nan.

A wata majami'a a Beit Sahour, Shireen Awwad ta kunna kyandir ga gwaggonta da aka kashe a St Porphyrius.

"Na yi baƙin ciki sosai. Ba za mu iya tunani ba, jikinmu yayi sanyi," in ji ta.

Kiristocin Gaza
Bayanan hoto, Majami'u a Gaɓar Yamma sun gudanar da addu'o'i na musamman wa mutane a Gaza

Har yanzu Shireen akwai ƴaƴan ƴan uwanta a birnin Gaza, ciki har da kanwar uwarta da aka jikkata a harin bam da aka kai cocin, wadda kuma aka yi wa tiyata ba tare da allurar kashe zafi ba don gyara mata kwankwaso a asibitin Shifa saboda ƙarancin magunguna.

Ta ce ƴan uwanta suna alfahari da kasancewarsu ƴan asalin Gaza, waɗanda suka zauna a wurin cikin yaƙe-yaƙe da aka yi tayi.

"Kowane lokaci muna tambayarsu cewa: 'kuna son barin Gaza?' Cewa suke, 'a'a, nan ne mahaifarmu. A nan ne aka haifemu', in ji Shireen. "Sai dai a wannan lokaci, a karon farko, ba su san cewa ko suna son su zauna ba, idan ma suka tsira kenan."

Al'ummar Kirista tsiraru da ke yankunan teku na Zirin Gaza na da daɗadɗen tarihi. St Porphyrius malamin coci ne a Gaza na ƙarni na biyar wanda kabarinsa ke ƙarƙashin cocin.

Kiristoci da yawa sun ƙaura, musamman tun shekara ta 2007, lokacin da Hamas ta karɓe ikon Gaza.

Isra'ila, kamar sauran ƙasashe, ta ayyana ƙungiyar ta Islama a matsayin ƙungiyar ta'addanci. Tare da Masar, ta yi wa Gaza killacewar gurgunta al'amura a yankin bayan da ta kwace iko.

Reverend Dr Munther Isaac, wani limamin addinin Lutheran a Bethlehem, ya ce abubuwan da suka faru a Gaza, sun sa shi "kaɗuwa".

Yana kuma fargabar makomar ɗaya daga cikin al'ummar Kirista ma fi daɗewa a duniya.

"A majalisar gudanar da harkar coci-coci ta farko, akwai wakilan cocin a Gaza, in ji shi. "Muna cikin damuwa kan duk wani ran ɗan adam, sai dai bayan yin komai, babbar damuwar mu ita ce, wannan zama na Kiristoci ta lokaci mai tsawo a Gaza za ta iya zuwa karshe."

Yayin da Fafaroma Francis ya yi kiran tsagaita wuta, Kiristoci Falasɗinawa sun nuna ɓacin ransu kan kalamai da wasu shugabannin coci suka yin ka yaƙin a bainar jama'a, musamman ma babban limamin cocin Ingila, Justin Welby, da Jagoran addini na Cocin Angilika mai yawan mabiya miliyan 85.

Mabiya ɗarikar Angilika a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan sun zarge shi da fifita majami'un Birtaniya

Mabiya ɗarikar Angilika a Gaɓar Yamma sun soke shi da fifita harkokin coci da na siyasar Birtaniya a kan martaba 'yancin Falasɗinawa

A birnin Gaza, inda hare-haren Isra'ila suka ruguza wani ginin Cocin Girka na Gargajiya a makon da ya gabata, George Anton na lura da abubuwa yayin da al'amura ke ƙara munana.

"Ba mu laifin komai ba. Ba mu da hannu a harkokin siyasa ko kuma na soji na kowace iri. Mu fararen hula ne. Me ya sa za a far mana? Saboda me?" ya tambaya.

"Mun rasa abokai da yawa. An kashe waɗanda aka kwashe zuwa birnin Khan Younis da ke kudancin birni Gaza. Harbin makaman roka ya faɗa musu kuma an ruguza dukkan gine-gine a yankin. Dukkansu sun mutu, sai dai ba mu da lokacin jimami.

"Kowace rana za ka ji an kashe wannan, an kashe iyali, an ruguza wannan gida, an shafe zuriya gaba-ɗaya. Ba za mu iya ganin wannan duka ba."

A karshe, ya sha alwashin ci gaba da zama a cocin tare da iyalansa.

"Mun ji kiraye-kiraye da dama na son a kwashe mu, sai dai ba za mu fice ba," ya faɗa min. "Nan ne wurin mu. Wannan ne gidan mu."